Abokai

472 21 2
                                    

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

           *5*

Wayanta dake k'ara ta d'auka, saki k'ayatattar murmushi tayi kana ta d'auka had'i da fad'in.

"Yan hutu! Kuna nan kuna shan hutu ko? Gashi next week za ayi resuming."

"Kai zaki cika min kunne, tunda kika fara magana ba full-stop ba coma. Kina ina ne haka?"

Gyara kwanciyarta tayi tace.

"Ka Bari kawai nayi nisan kiwo."

"In dai kina gari ya kamata mu kawo maki ziyara, ke in za a had'u sai dai a had'u gidan sauran mate."

"To ai ka san yanayin gidanmu Mallam Babba bai zo shirme."

"To yanzu dai kina ina ne ya kamata a k'ara had'uwa a gaisa."

"Ina gidan Aunty Fanna bari inyi maka kwatancan gidan, yaushe zaku zo?"

"Zuwa anjima zaki ganmu."

"To sai kunzo ina nan ina jiranshi." Sallama suka yi ta aje wayan, mi'kewa tayi ta shiga toilet tayi wanka, ganin lokacin sallan la'asar na gabatowa yasa bayan ta gama wanka ta d'auro alwala sannan ta fito, zama tayi ta tsara kwalliya, wata doguwar riga riga na material ta d'auko tasa, ita kanta da ta kalli kanta ta san tayi kyau, d'an k'aramin gyale ta d'auko tayi Rolling d'inshi a kanta, k'ara kallon kanta tayi ta juya idanunta had'i da sakin murmushi.

Fatima ce ke kallonta dake zaune tana karatu, ta girgiza kai tace.

"Kai duniya duka dududu shekarunki nawa Humaira? Amma jibi yanda kike tafiyar da lamuranki sai kace budurwa."

Murmushi ta k'ara yi sannan tace.

"Ni d'an ara min wayarki inyi hoto dan bai kamata kwalliyata ta tafi a banza ba."

Mik'a mata tayi tana mai ci gaba da kallonta. Amsa tayi ta fara kashe ma kanta hoto, wanda yi kawai take.

"Wai ke wannan uban hotunan da kike ta cika min waya dashi miye ne? Duk ki gama gogesu zanyi."

Saida tayi mai isarta sannan ta zauna zaman gani.

Bayan an kira sallah ta gabatar da sallanta, ta zauna zaman jiran friends d'inta, tana nan zaune Deen ya kirata, ta d'aga ya sanar mata da suna waje. Mi'kewa tayi a hankali ta sulale ta fice wurinsu, shigo dasu harabar gidan tayi, suka tsaya suna ta fira, Farouk ne ya dubeta yace.

"Kai mutuniyar wannan irin wanka haka?" Deen yace.

"Ai ka san babbar yarinya ce."

Dariya tayi ta kalli Mubarak tace. "Mubarak kana jinsu fa."

D'an gyara zamanshi yayi kana yace "Ai gaskiya suka fad'a, ke ta da ban ce. Wai yasu Sumy kuna had'uwa kuwa?"

"Haba mai zai hana abokiyar fad'a ta, ai in fad'a maka ko a waya ne sai na kirata na hayak'ata. Koda akayi hutu sai mun ta'ba fad'an nan. Ai yanzu mun girma kaga da mun koma mun zama seniors dole akama kai, amma dai za a d'an ta'ba kad'an-kad'an."

Deen yace.

"Haba Humaira ba wani kad'an-kad'an, ke d'in ce zaki daina? Ai ina bana tunani." Ya idasa maganar yana mai sakin malalaciyar dariya.

Dariya suka hau yi, nan suka hau tuna rayuwar da suke a school suna ta dariya.

Jin hayaniyar dariyarsu da fira yasa Ummu taji ta lek'o ta window ta hangesu suna ta 'ba'b'baka dariya. Girgiza kai tayi ta d'auki wayarta ta kira Humaira, tana d'agawa tace.

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now