8 Humaira

401 17 0
                                    

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

           *8*

Hausawa suka ce wai kwanci tashi asarar mai rai, wannan haka yake, gashi har suna ss3 ita da Aryan suna gaf da fara ssce.
A hankali Humaira ta k'ara girma, an zama 'yan mata, wani k'ara wayewa tayi, ga kyau data k'ara, bak'inta ya kwanta sosai a jikinta ya k'ara mata kyau, dan tana son bak'inta, tana jin yana mata kyau. Bata da sha'awar sirka kalarta, musamman data ga mutane da dama suna yabon kyanta da kalarta.

Kyawunta ne ya fito sosai, ga duk inda Humaira ta zauna sonta ake, tana da farin jini ga kwarjini, gata da son mutane kowa nata ne.

Sun fara zana jarabawa wanda take yinshi cikin hankali kwance, duk da har yanzu bata riga ta yanke hukuncin abinda take so tayi ba, duk da a son samu tafi son tayi aure, dan ita burinta tayi aure, sai dai yanayin kuma samarin ne yasa har yanzu bata san makomarta ba. Amma tana addu'ar Allah ya za'ba mata abinda zai fi zama alkhairi.

Tunda suka gama Daddy ya diro garin dan d'aukarta, nan hankalin Hajja ya tashi, tana jin ba zata iya rabuwa da Humaira ba.

Daddy yace. "Hajja d'aukar Humaira ba yana nufin an rabaki da ita bane, zata rin'ka zuwa tana ganinki, yanzu ina so inga na inganta mata rayuwarta, sannan Humaira idan Allah ya fiddo mata da miji ai aure zata yi."

Sunkuyar da kai Hajja tayi hawaye ya zubo mata tace. "Yaran nan na riga dana saba dasu bana so inga sunyi nesa dani, gashi zaka d'auketa ka tafi da ita uwa duniya har kaduna. Kuma kaduna bariki ce bana so d'abi'unta su banbanta da namu."

"Hajja zan kula zansa ido sosai a kan Humaira, yanda zan kwa'ba ma su Maryam haka zan kwa'ba mata itama, Humaira ma ai 'yata ce."

Mallam Babba ne ya shigo ya taddasu kamar wad'anda aka aiko ma da mutuwa yace. "Lafiyarku kuwa?" Daddy ne yayi dariya yace. "Wai duk akan tafiya da Humaira ne."

Mallam yace. "Kada ki damu ai Humaira ko tana can tamkar tana tare damu ne, sai dai Humaira ina son ki kama kanki ki san irin k'awayen da zaki yi tarayya dasu. Duk wannan Tara k'awayen naki ki ajeshi wuri guda, koda karatu kika fara ki san wanda zaki zauna dasu."

Daddy yace. "In dan wannan ne matsalarku da Humaira zata rabu dasu, ai ta san gidana ba a yawo ba tara abokai. Gata ga Maryam nan, duk da aure itama zata yi."

Hajja dai har yanzu tana jin bata son tafiyar Humaira, dan har a ranta take jin kewar Humaira, ranar dai tare suka had'a kayanta, tace ma Humaira yau tare zasu kwana, ku san raba dare suka yi suna fira.

Washegari tunda safe suka d'auki hanyar kaduna, suna mai kewar juna, haka Aryan bai so rabuwa da 'yaruwarshi ba.

Sune basu isa ba sai yamma, suna isa da gudu Maryam tazo ta rungumeta tana murna, haka Mommy ma ta k'araso ta rungumeta tana mata sannu da zuwa. D'aki Maryam ta wuce da ita, toilet ta shiga ta tara mata ruwan wanka, ta fito tace. "Ga ruwa can kiyi wanka kizo kici abinci."

Mi'kewa tayi a gajiye ta fad'a toilet tayi wanka ta d'auro alwala, saida ta shirya tayi sallah, Maryam ta shigo d'auke da tray d'in abinci ta dire a gabanta. "Ga abinci nan kici kinsha hanya."

"Kai akwai tafiya baki ji ba gaba d'aya jikina yayi weak."

"Ai dole tafiya ce mik'ak'k'a." Nan suka zauna tana cin abinci suna fira, har ta gama suka kwashe kayan suka fito palour, zama tayi suka gaisa da mommy. Mommy tace. "Humaira yanzu kin zama 'yar kaduna, wai mai ya hanaki yin jamb da ba sai ki fara karatunki tun yanzu ba?"

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now