18 Kaduna state University

545 30 7
                                        

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

           *18*
Yau ce ranar farko da Humaira zata fara shiga school,fannin registration da komi ta riga da ta gama, Yaya Jawad ne zai kai ta suna tafiya ta waigo ta kalleshi tace.

"Ka san ko Yaya Jawad yau sai nake ta jin wani iri, wallahi ji nake gabana sai fad'uwa yake." Yace. "Kin jiki dan me gabanki zai fad'i, da kin shiga kin had'u da students tun a yau zaki ga kin saba dasu, kada ki damu kanki sai kace ba wayayyiya ba, kina shiga ma zaki ga rayuwar school d'in kowa hidimarshi yake. Keda kanki fa da kika zo yin screening ce min kika yi kowa hidimarshi yake."

D'an raunana fuska tayi had'i da cewa. "Amma duk da haka sai nake jina wata iri."

Har suka isa yana bata shawarar yanda zata kasance da yanda zata yi d'abi'unta yake. Saida ya tabbatar ta shiga sannan ya juya akalar motarshi ya fita. Tunda ta shiga ta fara sabawa da mutane ta had'u da wasu da suka jawota wurinsu. Hauwa'u, Khadija, sai Hafsat. Komi a ranar tare suka yi. Tun a ranar duk wani dake cikin class d'in nan sai da ya san Humaira. Domin ita akwai son mutane ga saurin sabo da mutane. Tunda suka tashi lectures Yaya Jawad yazo d'aukarta a mota take ta zuba mashi surutun yanda ta kasance a zuwanta na farko. Wani yayi dariya wani ya biye mata. Haka tunda ta isa gida ta tasa Mommy da surutu yau kaza ya faru yau anyi kaza.

Yau tunda ta kwanta rayuwar da tayi a cikin school take ta tunawa. Washegari kuwa tunda wuri ta shirya dan tafiya. Yaya Jawad ne ya shirya dan ya kaita. Tana isa ta had'e da k'awayenta. tunda suka fito lectures suka isa dan suci abinci. Tunda suka gama suka zauna fira wanda kamar sun manta abinda ya kawosu, haka itama Humaira ta biye masu suna ta fira. Wasu maza suka yi joining nasu suka ci gaba da fira.

Haka rayuwar Humaira taci gama cikin school, yau ma kamar kullum tunda suka fita basu k'ara dawowa class ba, yau ma haka suka had'e da fans d'insu maza, TK da KB sai Ibrahim. Yanda taga suna ta tafiyar da mu'amalarsu da mazan yasa abin yayi ta bata mamaki, kallonsu kawai take wanda abin yana ta d'aure mata kai ko kunya basu ji na yanda mutane ke wucewa suna kallonsu, sai faman kashewa suke da rungume rungume, to dama haka ke faruwa a cikin makarantar? Tambayar kanta ta rin'ka yi. Mi'kewa tayi tana mai jin kunyar kallonsu tace. Hi guys! Ni zan koma ciki naga kamar mun manta da lectures ko?" Ta juya ta tafi, dai-dai lokacin da mallam Sani mai d'aukarsu Introduction to computer ya fito, da sauri ta shige tana jin bata kyauta ma kanta ba, farawa da iyawa har zata fara wasa da karatunta. Samun wuri tayi ta zauna duban wadda ta zauna kusa da ita tayi wadda ta d'an mallaki hankalinta tace.

"Dan Allah baiwar Allah idan ba damuwa ina son in san abinda kuka yi."

Nafisa ta kalleta tace. "Ba damuwa ai. Amma ina kuka je gashi har test ya mana" Zama tayi ta koya mata wanda Humaira ta amshi littafinta tayi jotting. Taji dad'i sosai, sai dai abu d'aya ne bata ji dad'i ba na test d'in da ya masu bata ciki. Anya ko wasan abokan karatu ne kuwa? Tambayar kanta take. Ya zama dole tayi ma kanta fad'a ta zauna ta nemi serious students da zasu zauna suna k'aruwa da juna. Idan har karatu ya kawota to wad'annan ba abokan da zata zauna dasu bane idan har ba tana son carry over ya rin'ka bibiyarta ba wanda idan ta samu sune na farko da zasu rin'ka mata dariya da gulmarta.

Har suka tashi abin yana damunta. Yaya Jawad yazo d'aukarta. Tun a mota ta fara bashi labari wanda har ya riga da ya saba da labarin, kowace rana da labarin da za a samu, dan da kanshi yake tambayarta yau kuma mai ya faru wane jaridar muka samu?
Har suka isa gida tana bashi labari, suna isa ta gaida Mommy ta wuce d'aki saida tayi wanka sannan ta fito ta zuba abinci ta zauna wurin Mommy. Tana fara cin abinci ta fara bata labari.

"Mommy ni rayuwar nan tana bani tsoro, wai kiga mutanen bahaushe tashin addinin musulunci, amma basu kunyar su rin'ka ta'ba junansu, gashi mazan ma ba wasu manya ba. Hmm! Mommy baki ga abinda ke faruwa ba ni har kunya ma nake ji idan naga suna wani abin. Shiyasa ma canza k'awaye zanyi."

JINI D'AYAStories to obsess over. Discover now