*JINI D'AYA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Wattpad@Ayshatmadu*
*16*
Washegari tunda tayi sallan asuba bata koma barci ba tayi wanka, dan ta san tafiyar wuri zasu yi, d'akin Hajja ta shiga ta sameta kan sallaya tana share hawaye. Zama tayi kusa da ita tana kallonta dai-dai lokacin da take saurin k'o'k'arin goge hawayen. D'an murmushi Humaira tayi ta gaidata, bayan ta amsa tace."Hajja kuka kike yi ne?" Da sauri Hajja ta girigiza kanta tace. "A'a wani abu ne ya fad'a min idanu." Binta Humaira tayi da kallo ba tare da tace mata komai ba, dan itama kanta ji take hawayen kamar zai zubo mata. Maganar Daddy taji ya shigo gidan. Ji tayi gabanta ya fad'i, ji tayi tafiyar da za tayi kamar za a rabata da wani abu ne.
Shigowa d'akin yayi ya duk'a dan gaida Hajja, bayan ya gama gaidata Humaira itama ta gaidashi, bayan ya amsa yace. "To kin dai gama shiryawa ko mu samu mu d'auki hanya da wuri?" D'aga mashi kai tayi ta mik'e ta koma d'akinta, hijabinta kawai ta maida a kanta tana share hawayen da taji ya zubo mata. Aryan ne ya shigo d'akin yace. "Har zaku tafi kenan?" D'aga mashi kai kawai tayi, dan ji take idan tayi magana kamar kuka zai kufce mata. Jakarta ta bud'e ta ciro dubu biyar ta mik'a mashi, ta maida dubu biyu koda zata buk'aci wani abu. Amsa yayi yana mata godiya. Yace. "Shiyasa idan baki nan nake jin ba dad'i, saboda baki ta'ba barina in rasa wani abu."
D'an murmushi tayi, ya d'auki jakarta ya fita dashi, itama ta fito, su Adama ne suka fito suma dan rakata. Waigawa tayi tace. "Ina Hajja kuma?" Tana k'o'k'arin fitowa daga d'aki tace. "Gani nan fitowa."
D'akin Mallam Babba ta shiga dan yi mashi sallama, "Au har tafiyar ta tashi ne? To Allah ya tsare hanya, ga wannan ki aje a wurinki ko zaki buk'aci wani abu ko." Kanta na duk'e dan bata son d'agowa tace. "A'a Mallam ka barshi ina da kud'i."
Yace "Ke amshi nan bana son sakarci, idan bamu baki ba wa zai baki? Kuma kafin in sake ganinki ai zan dad'e." Hannu biyu tasa ta amsa tayi mashi godiya. Sannan ta mik'e ta fita, duk nan ta taddasu gaban motar. Bud'ewa tayi ta shiga ta du'kar da kanta k'asa, hawaye take jin yana zubo mata. Suma duk sunyi cirko-cirko duk basu son tafiyarta. Nan Daddy ya d'aga masu hannu bayan driver ya tada motar ta fara tafiya. Saida suka tafi sannan suka koma gida cike da kewar Humaira.
Daddy ne ya waigo ya dubeta yace. "Ya akayi Humaira baki son tafiyar ne?" Girgiza kanta tayi dake duk'e. "To mai yasa naga tun jiya da nazo baki cikin walwala ko wani abu yana damunki ne?"
Tace "A'a Daddy ba abinda ke damuna."
Yace. "To ko kin gaji da zama damu ne kinfi son zama dasu Hajja? Dan naga itama duk fuskarta wani iri?"
Tace. "A'a Daddy ina son zama daku, sai dai ina son zama da Hajja." D'an dariya yayi yace.
"To ai dama ba wanda zai rabaki da Hajja, amma ai komin daran dad'ewa ai zaki yi aure ku rabu ko? Yanzu kinga karatu nake so kiyi kuma hakan ma ai an rage ma Hajja nauyin wani abu ko? Yanzu ki saki jikinki idan har kika fara karatu na maki al'kawarin da kun samu hutu zaki rin'ka tahowa wurin Hajja hakan ya maki?" Da sauri ta d'aga kanta cikin jin dad'i.
Sunyi nisa sosai da tafiyar suka tsaya suka yi sallan azahar, gasassar gasa ya siya masu da yoghourt sannan suka ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali.
Sosai tafiyar tayi masu sauri, suna isa Mommy dake zaune ta mik'e da sauri ta rungume Humaira tana murnar dawowarta. Daddy ne yayi tsaye yana kallonsu yana dariya yace. "Wato ta d'iyarki kike yi ko ni baki ta nawa ko?"
Tana dariya tace. "Kada ka damu ai kai naka tarbar special ce ba sai kayi k'orafi ba." Dariyar yaci gaba dayi, yayin da itama Humairan take dariya, dan rayuwar gidan yana birgeta, ta wata fuskar kuma baya birgeta. Talatu ce ta fito da sauri tana mata oyoyo. Bayan tayi ma Daddy sannu da zuwa ta d'auki jakar Humaira ta shigar mata dashi d'aki tana ta k'ara mata sannu da zuwa. Humaira ta dubeta da dariya tace. "Kai Talatu wannan irin murna haka baki ya'ki rufuwa."
Tace. "Ke Humaira ba zaki gane bane, baki san yanda na k'osa ki dawo bane, dan ina ji ko Mommy bata kaini k'osawa da ki dawo ba. Wai kinga yanda muka yi kewarki ne a gidan nan, kinga hatta Daddy ko ba yanzu yayi niyyar zuwa ba, amma nan naji yana ce ma Mommy shifa ya k'osa ki dawo, kawai sai ji muka yi yace jibi zaije da kanshi ya d'aukoki. Wallahi Humaira kina da shiga rai, duk wanda ya zauna dake sai ya soki, baki da fushi baki da k'yamar mutane, duk da dukan gidan nan duk haka suke suma basu da k'yamar mutane, shiyasa ni dai wallahi ina sonki ina son inta kasancewa dake."
Dariya Humaira tayi cikin jin dad'i da maganar da Talatu tace. "Nima Talatu ina sonki kamar yanda kike sona, yanzu kinga duk sanda nayi aure sai ki koma gidana." Waro idanu Talatu tayi tana ri'ke da bakinta tace. "To ni ba zanyi aure ba?"
Humaira tace. "Idan kina tare dani mai zaki yi da aure, kawai ba sai kiyi zamanki ba." Tace. "Barni inyi auran nan nima in d'and'ana."
Humaira tayi dariya tace. "Banda wanda kika d'and'ana wanne kuma zaki k'ara d'and'anwa?"
Tace. "Wani auran mana, ai har yanzu da yarintata." Dariya suka yi gaba d'aya. Toilet ta shiga ta kunna mata ruwan zafi tace. "Ga ruwa nan na kunna maki kiyi wanka, yanzu zanje in had'a maki abinda zaki ci in kawo maki. Tace. "Ba sai kin kawo min ba bana jin yunwa saboda mun d'anyi ciye-ciyenmu a hanya."
Toilet ta mik'e ta shiga tayi wanka tayo alwala ta fito dan yin sallan la'asar.
Mommy kuwa d'aki taja Daddy ta had'a mashi ruwan wanka yayi, duk wani abu da ta san zata mashi saida ta mashi, sannan ta fito tazo wurin Humaira, zama suka yi suka yi ta fira. Yaya Jawad ne ya dawo. Yana ganinta ya sakar mata murmushi, itama murmushin ta sakar mashi. "Yar borno an dawo kenan?" Ya idasa maganar gami da zama kusa da ita.
Mommy ta dubeshi tace. "Ka dawo kenan?" Yace. "Aikuwa Mom sai kuma ga mutuniyata ta dawo, kin san Humaira da ba kya nan gidan nan ba dad'i, amma na san yanzu gidan zai ci gaba da dad'i ko Mom?" Ya idasa maganar yana kallon Mommy. Tace. "Sosai kuwa."
Tunda Humaira ta dawo soyayya sabuwa suka k'ara 'kullawa, in dai suna waje Jawad baya kunyar nuna mata soyayya, sai dai a cikin gida ya kasa nuna yana son Humaira, ko miye dalilin haka? Shi ya bama kanshi sani. Sosai suke jin son junansu a ransu, wanda dai-dai da second Humaira bata son tajita bata tare dashi, wanda idan har baya gida suna nan mak'ale da waya a kunne, sosai ta saki jikinta dashi, wanda har ta manta ma da duk wani abu da ya faru a tsakaninsu kwanaki, sosai suke soyayyarsu.
Wanda yanzu gaba d'aya ko waya bata son yi da Ashir ko kiranta yayi bata son d'auka, sai ma idan sun had'u ta WhatsApp ne suke d'an gaisawa har suyi fira. Duk da yana son su had'u amma ta'ki bari su had'u.

YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fanfictioncikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...