*JINI D'AYA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Wattpad@Ayshatmadu*
*17*
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah,
Wannan haka yake, Humaira ta samu ta rubuta jamb d'inta inda ta samu score mai kyau, wanda ta zauna jiran admission. Cikin hukuncin Allah kuma ta samu gurbin karatu a KASU (kaduna state University) ba k'aramin farin ciki tayi ba da jin haka.Tun a waya ta kira Yaya Jawad ta bashi labari, shi kanshi sosai ya tayata murna tun a waya. Dan duk wanda ke son Humaira dole ya tayata murna ganin ta samu abinda take buri karatu, sannan gashi ta samu course d'in da take so computer science. Wannan ai abin murna ne. D'aki ta shige tayi alwala tayi sallah tayi ma Allah godiya akan burinta da ya cika mata. Da rok'onshi ya bata abinda zata ke nema.
Tana idarwa ta kira Aryan ta fad'a mashi, sosai ya tayata murna tare da sanar da ita shima ya samu admission a nan unimaid. Cikin jin dad'i tace. "Kai amma na tayaka murna, shine ko ka kira ka fad'a min sai da na kiraka, wai mai yasa baka son kirana sai idan ni na kiraka?"
Yace. "I'm sorry sister! Ai na san dama sai kinyi complain in dai kika kirani."
Saida suka yi fira mai isarsu sannan suka yi sallama. Hajja ta kira ta fad'a mata ta tayata murna sannan ta d'aura da yi mata nasiha. "Humaira yanzu idan kika shiga makarantar nan zaki ga rayuwa mabanbanta, zaki had'u da mutane kala-kala, dan haka ina rok'onki da ki tsare mutuncin kanki. Ki san k'awayen da zaki yi mu'amala dasu. Ki san wad'anda suka dace da tarbiyarki. Kada ki biye ma k'awayen banza ki samu na kirki kiyi k'awance dasu. Ki rin'ka tuna ke marainiya ce baki da kowa, makaranta ce da zaki shiga ki had'u dana banza dana kirki. To ki ri'ke na kirkin masu k'o'k'ari wad'anda suka san abinda ya kaisu. Sannan zan d'inko maki hijabai in aiko maki dashi."
Dariya Humaira ta hau yi tace. "Hajja wane irin hijabi ki aiko min da gyalulluka masu kyau wad'anda zan rin'ka shiga na kece raini." Hajja ta buga salati a waya. Humaira tace. "Hajja lafiya wannan irin salati haka?"
Tace. "Ba dole inyi ba nasiha fa nake maki amma kin maidani inyi in gama ba. Kin san Allah idan kika je kika rin'ka malaman nan haka ko ina daga gefe ba ruwana." Dariya Humaira ta k'ara yi tace. Shikenan Hajja ya wuce zan kiyaye duk abinda kika fad'a min."
Sallama suka yi ta mik'e ta canza kaya ta shiga kitchen dan d'aura abinci. Dan yau gidan dambu suke son ci kuma Daddy yace ita za tayi dan tafi su iyawa. Tare suka shiga ita da Talatu suka fara aiki.
Talatu ta dubeta tace. "Wai Humaira dan Allah wa ya koya maki girke-girke hakane?" Murmushi ta d'anyi tace. "Hajja mana kin san bata sakeni ba in zauna wai sai anyi an bani, haka zata sa in fito cikin masu aikin ayi dani. Zata sani inyi wannan inyi wannan, ke tun bana so har nazo yabi jikina sai kuma yanzu nake jin dad'in haka nake alfahari yanda ta tsaya tsayin daka sai da taga na iya duk wani aikin da ya shafi cikin gida."
Talatu tace. "Gaskiya Hajja tayi k'o'k'ari sosai kuwa, tunda gashi duk abinda kika dafa idan har zamu ci sai munyi santinshi." Dariya suka yi.
Girki abu ne da yake k'ara ma mace k'ima bama a wurin miji kad'ai ba, hatta a ko ina, sai kaga ga mace har mace amma bata iya girki ba, bata san yanda zata gyara d'aki ba, ita gata 'yar gata sai dai asa mai aiki tayi mata komai, ba a nan matsalar take ba sai sanda aka aurar dake daga lakacin zaki gane kin rasa wani babban jigo a zaman auranki. Dan haka duk gatanka duk miye naka ka mik'e kama kanka ba komi ka sakar ma aiki ba kai hutu.
K'amshi ne ya fara ziyartar cikin gidan, tunda ta d'aura na biyu ta mashi had'i, ji kake har k'amshin gyad'ar na fitowa. Yana dahuwa ta juyeshi, yayi kyau sosai gashi yaji zogale. Had'a ma Daddy nashi tayi a babbar flask ta had'a masu komai ta kai palour d'inshi. Dawowa tayi ta had'a kunun ayar da ta riga ta markad'a. Talatu ta dubeta tace. "Ni dai Humaira gaskiya zan d'iba inci saboda tun d'azun miyauna sai tsinkewa yake yi."
Humaira tace. "Aiko sai ki bari sai an gama gyara komai sannan." Da sauri Talatu ta fara kaye-kayen wurin Humaira sai dariya take mata. Saida ta gama komai ta kai ma Daddy sannan ta zuba nata ta dawo palour dan taci. Muryar su Daddy taji sun shigo su da abokanshi.
Mommy ta mik'e ta shiga d'akin suka gaisa, bayan sun d'an ta'ba fira, mi'kewa tayi ta fara serving nasu na dambun. Tunda suka yi loma d'aya suka fara santi. Wani da ake kira Alh umar ne yace. "Kai wannan wane irin dambu ne haka ni ban ta'ba cinshi haka ba?" Dariya suka fara mashi Mommy tace. "Kai Alh umar wannan irin santi haka?" Yace. "Ai wannan ya wuce santi dan Allah ya akayi wannan dambun?"
Mommy na dariya tace. "Sai in kira maka wadda tayi ka tambayeta." Yace "Au bake kika yi ba? Dan Allah kirata in ganta." K'wala ma Humaira kira tayi, sai gata ta shigo ta duk'a har k'asa ta gaidasu. Cikin barkwanci yace. "Yanzu kece kika yi wannan girkin haka, 'yar k'arama dake wa ya koya maki girki?" Du'kar da kanta k'asa tayi tana murmushi. Alh Isah yace. "Dole a bada tukwicin girkin nan." Hannu yasa a aljihu ya ciro 'yan dubu guda biyar ya mik'a mata. K'in amsa tayi Mommy ta amsar mata. Godiya tayi ta fita. Haka suka zaune suka cinye duka dambun da kunun Aya. Dariya Mommy take ta masu yanda suka zauna sai faman maganar dambu suke. Koda zasu tafi Alh umar sai da yasa aka zuba mashi wani ya tafi dashi.
Da daddare Daddy da kanshi ya kira Humaira ta samu wuri ta zauna ya dubeta yace. "Humaira 'yar makaranta, yanzu dai ga admission kin samu ko? To ina so ki kula da kanki kiyi abinda ya kaiki, ba na son k'awaye, ki dage kiyi abinda ya kaiki, karatu ne ba irin na secondary ba sai ki dage kuma ki dage da addu'a. Banda shigar banza ko kiga wasu na shiga su birgeki kema kice sai kinyi, ke musulma ce 'yar gidan malamai. Koda so ki tsare mutuncin kanki. Sosai ya zauna yayi mata nasiha. Tayi godiya ta koma d'aki.
Duk wasu shirye-shiryen da za a mata da duk wasu abu daya kamata duk an mata. Sai jiran fara shiga school. Wanda ita har ta k'osa taga ta shiga. Sai d'auki take.

YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fanfictioncikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...