9 Taron biki

308 17 0
                                    

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

           *9*
Yau gagarumar dinner ce ake had'awa inda zai tara mutane da yawa, harda iyaye, Humaira tsayawa kawai tayi tana kallon ikon Allah, kallon Maryam take wadda take zaune ana tsara mata kwalliya. Tace "Yaya Maryam dan Allah bari muyi gulma."

Dariya wurin suka yi, Maryam na dariya tace. "Ke kuwa gulmar me zamu yi?"

D'an sunkuyo da bakinta tayi dai-dai kunnanta tace. "Wai Yaya Maryam ni naga dinner d'in nan da za ayi harda iyaye meyasa zasu je? Ba gara mu yara su barmu muje ba ko k'ara'in da basu yi da bikinsu bane suke son yi? Ni naga fa Daddy d'an gidan malamai ne kamar hakan fa zaiyi tsauri da yawa ko?"

Saida suka yi dariya sannan Maryam tace. "Haba sister kada ki bani kunya mana duk wayewarki da k'awayenki da abokanki wayayyu amma kike ganin haka wani iri? Ai ba wani abu bane kuma kinga Daddy d'an boko ne yayi gogayya da mutane kala-kala, ya zaga k'asashe da yawa."

Humaira ta ta'be baki tace. "Hakane kuma amma zanga mai zai faru wurin dinner d'in nan, sai dai fa so nayi in cashe sosai gashi idan su Daddy na wurin ba zan samu confidence d'in cashewa ba."

"Zaki samu mana, wai ke yanda Daddy ke janki a jiki kin kasa sabawa, baki ga yanda muke dashi bane a cikin gidan? Ya kamata ki saba dashi danni dai kinga na kusa tafiya in barki dasu."

Haka akaita shirin tafiya dinner Humaira bata zauna an mata kwalliya ba saida ta tabbatar data yi sallan isha'i sannan ta zauna zaman shiryawa, gaba d'ayansu shigar material blue suka yi. Duk kowa ya fito yayi kyau, an fara jigilar d'aukasu ana kaisu wurin. Shi kanshi Hall d'in ya k'ayatu sosai da decoration.

Wuri ya cika sosai da manyan mutane 'bangaren amarya da ango, su kansu iyayen gaba d'aya suna hightable, inda aka k'awata masu side d'insu, haka 'bangaren couple's d'in.
Sai hidima ake, can lokaci ya fara tafiya, Mc ya bada umurnin yana son ganin iyayen amarya a wurin inda zasu yi rawa, wanda yafi iya rawa tsakaninsu shi yayi winning za aci tarar wanda aka ci naira na gugan naira har dubu hamsin, nan wuri ya d'auki tafi, raf-raf, da shewa da dariya. Nan suka fito aka sakar masu kid'a, Mommy dagewa tayi ta zage tayi ta rawa, yayin da Daddy ya d'an rin'ka takawa a hankali, wuri ne ya kacame kowa ya fito sai lik'i ake masu.

Humaira na masu lik'i itama tana takawa. Can aka tsaya da kid'a ana mai k'ara tafa masu, wanda abin ya birgesu suna nuna jin dad'i. Mc na yabawa yace. "Kai wannan abu ya k'awatar dani sosai ya sani nishad'i, ba zamu fad'i result ba har sai suma iyayen ango mun basu tasu damar sannan mu had'a mu fad'i result."

Nan wuri ya k'ara d'aukan shewa da tafi. Haka suma suka fito aka sakar masu nasu kid'an suka fara cashewa. Saida suka gama sannan Mc yaci gaba. "Yanzu zamu fad'i wad'anda suka fi iya rawa a ciki, wanda basu manta da rayuwarsu ta matasa ba. Dangin amarya wanda ya lashe ba kowa bane illa..... Wai naji zuciyar mutane da yawa a wurin yana bugawa.." dariya suka hau yi ci gaba yayi "Bakowa bace illah Hajiya Fatima, dan haka Alh Mustapha masoyiyarka ita taci naira dubu hamsin."

Nan wuri ya k'ara d'aukar sowa, nan Daddy ya ciro bandir d'in d'ari biyar ya mik'a ma Mc shi kuma ya damk'a ma Mommy. "Sai abu na gama nan ma ba kowa bace illah Hajiya Nana. Wai ya kuma bari matan nan suka cinyeku ne?" Nan wuri ya hautsine da surutu ana dariya, gaba d'ayansu suka amshe kud'insu suma suna dariya.

Bayan an huta, ciye-ciye aka fara inda kowa yake serving kanshi. Sai sha biyu sannan aka tashi, motar da suka shiga ne ya li'ke mata sai faman tambayarta yake sai ta bashi number d'inta, 'karshe dai Mariya da suke tare ta bashi, Humaira sai faman harararta take, yana saukesu yace mata "To sai na kira ko?" Ko kallon inda yake bata yi ba ta wuce.

Tunda suka dawo gida ake maida yanda aka yi, Humaira tace. "Lallai yau naga bikin 'yan boko, abin ya k'awatar dani sosai, ji nake ina ma a maimaita."

Mariya tace. "Dama ke da son bidi'a ai ba'ki k'i ba a jera sati ana yi. Koda yake ai gashi kin samo mana d'an kaduna mun kusa k'ara shan biki."

Humaira ta zum'buro baki tace. Tunda ance maki shi zan aura kawai daga had'uwa da mutum yau sai kice wani aure, ai ba zanyi aure ba duk sai na gama kaiku d'akinku, ai ni har yanzu yarinya ce banyi hankali ba."

Dariya suka yi suna tsokanarta. Nan fa suka dosa fira, saida suka yi ma'ishi sannan suka kwanta, ai Humaira bata kwanta ba saida ta gama updating status hotuna da videos d'in ranar sannan ta kwanta tana mai jin dad'in hidimar da ake yi haka.

Washegari tun k'arfe sha d'aya aka fara hidimar bud'an kai da baifi awa biyu ba, inda amarya tasha lifaya mai kyau, haka dangin amarya da amarya, bayan an gama bud'an kai kuma wani shigar lifaya tayi na shirin walima. Wanda suka gayyato babbar malama data ma amarya nasiha mai ratsa jiki. Kuma an samu abinda ake so dan kam nasihar ta shigeta.

Washegari kuma aka d'aura auranta da angonta yamma nayi aka d'auki amarya aka kaita gidanta dake unguwar rimi, sosai suka ri'ke junansu suna kukan rabuwa. Koda suka kaita zasu tafi gida haka suka rungume juna suna kuka, haka suka rabu suka taho gida suna jin kewarta. Koda suka dawo gida ji take gidan ya mata girma.

Waje ta fita ta samu Aryan suka zauna sukai ta fira, dan tun da asuba suka shirya zasu tafi, shiyasa ta zauna suna ta fira. Saida ya fara jin barci sannan ya mata sallama ya shige ciki, itama d'aki ta koma ta kwanta, wayarta ta jawo tana kwance taci gaba da chat d'inta, saida ta fara jin barci sannan ta aje wayar tayi addu'a ta kwanta.

'Yan biki kam suna idar da sallan asuba suka fara shirin tafiya, har waje suka rakasu Humaira na jin kamar ta bisu. Haka suka gama shiga suna d'aga masu hannu har suka fita daga layin, komawa ciki suka yi Humaira na jin duk ba dad'i, ji tayi duk gidan ya fita ranta, dan dama zaman Maryam yasa take jin dad'in zaman gidan.

Shima Yaya Najib ya fara shirye-shiryen tafiyarshi, kiran Humaira yayi tazo ta samu wuri ta zauna ya dubeta yace.

"Hamsin dama ina so inyi maki magana, yawan shige ma Jawad da kike yi ki daina, kada dan kinga d'an uwanki ne komai zai iya faruwa a tsakaninku, saboda shaid'an da kike ganinshi ba abinda ba zai iya tunkud'a mutum yayi ba, dan haka ki kiyaye, rayuwar nan sai a hankali. Bade a fita yawo ko?"

Kanta na duk'e tace. "A'a ba inda nake zuwa." Sun dad'e nan yana mata nasiha na yanda zata kula da kanta. Sannan ya sallameta ta koma d'aki. Wayanta taci gaba da dannawa, shi kad'an zai d'an d'ebe mata kewa dan dama ita ba gwanar zama tayi kallo bane, gani take 'bata lokaci ne.

Wayarta ce taji tana k'ara ta duba taga bata san number d'in ba, har ta katse bata d'auka ba, sai da aka k'ara kira sannan ta d'auka cikin sallama. Amsa mata yayi kana yace. "Na san baki gane mai magana ba? To driver d'inki ne daya d'aukoku da biki."

"Oh dama kaine? To ya kake?"
Can 'bangaran ya amsa mata da lafiya lau, yaushe za a bani dama inzo mu gana?"

Amsa ta bashi da. "Gaskiya nan ba za a barni in fita ba, sai dai mu rin'ka waya har inga yanda za ayi."

Nan dai suka d'anyi waya kad'an suka yi sallama da zumar zuwa anjima zai k'ara kiranta.

Tun daga ranar ko kullum sai ya kirata sun gaisa. Har ta d'an fara sabawa dashi duk da har yanzu bata bashi damar yazo inda take ba.

Saboda Yaya Jawad bai barinta tayi sa'kat in dai yana gidan, ko Mommy sai su dad'e basu zauna sunyi fira ba, sai idan duk suna gidan sun had'e a palour.

Bayan sunyi waya da dare ya nace kan dole yana son su had'u a ko ina ne, ba yanda zata yi dole tasa tace ya bari gobe idan taje gidan Yaya Maryam sai yazo nan su had'u.

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now