19. sirrin 'boye

429 20 5
                                        

*JINI D'AYA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Wattpad@Ayshatmadu*

*19*

Haka ta k'ara fita daga rayuwarshi bata son abinda zai had'ata dashi dan tana tsoron ta ci gaba da biye mashi k'arshe kuma tazo tayi da na sani, dan a yanda yake nuna mata zai iya aikata komai shiyasa yanzu take tsoron had'uwarsu.

Sai dai ba nan gizo ke sak'ar ba, sabo da aikatawa yasa yanzu Humaira har ta san ta shiga tayo download d'in blue film, wanda duk ranar da ta kalla duk duniya sai taji hankalinta ya tashi tsoron had'uwarta da ubangijinta, gashi da zarar ta gama aikatawa zata fara kuka da neman yafiyar ubangiji. Wanda ta rasa dalilin da yasa take aikatawa.

Kamar kullum yau ma ta gama kallonta ta zauna zaman rera kuka. Tamabayarta kanta take mai yasa take aikata wannan abin? Ko dai aljanu ne suka shigeta ko kuma wani ne ya mata asiri? Wani zuciyar ya bata amsa da. Ba wani aljani ko asiri, zuciyarki ne ke baki damar aikatawa wanda da zarar kin aikata kuma sai kuma ruwa.

Abin ya zaman mata ta rasa yanda zata yi, duk yanda taso ta daina ya gagareta. Koda ta d'auki tsawon lokaci bata kalla ba, k'arshe dai sai ta koma ruwa. Sanadin haka ta goge operamini d'inta dan ta daina d'aukowa. Amma k'arshe da kanta ta k'ara maido dashi kan wayanta. Yaya Jawad ko bai fasa bibiyarta ba, haka wani zubin take ci gaba da biye mashi yana yanda yaga dama da ita.

Yanzu har ta kai Humaira na biye ma wasu mazan a waje wanda abinda ya zama ruwan dare kenan a zamanin nan da muke ciki. Saurayi yazo wurinka ba ya san ba auranka zai yi ba, kawai dan yayi k'ok'arin 'bata maka rayuwa ne kawai.

Dan yanzu zamanin nan ya canza sai a nuna maka ai dan ana sonka ne, to idan ya ta'ba maki jiki ya tafi ribar mai kika samu, 'yan matan yanzu muna ganin wak haka ba zina bace, itama kanta wannan abin da mafi yanwancinmu ke yi Zina ce, saboda ba mijinki bane. So be careful woo... Idan ba haka ba zai kaiki ya baro k'arshe ya gudu ya barki da cizon yatsa da dana sani. So duk yanda kika ga baki aure ba kiyi ha'kuri lokaci na nan zuwa in dai da rayuwa kada kiga rashin aure yasa ba zaki iya jurewa ba ko ki je wurin wasu mazan ko kuma ki biya ma kanki buk'ata duk wannan bai kamata ba, Idan har kika yi ha'kuri kina kyakykyawan zamanki Allah zai fiddo maki da mijinki nagartacce.

Yanzu ga Humaira nan saboda rashin ha'kuri d'an uwanta na jink yana so ya 'bata mata rayuwa tana ji tana gani.

Ga abin sosai yake bugun zuciyarta yanda take biye ma samarin waje koda ba zasu bata kud'i ba, in dai ta fidda abinda ke jikinta ya wadatar da ita. Duk da haka bata ta'ba bari wani abu ya shiga tsakaninta dasu. Zaune take shiru tana tunanin abinda take aikatawa fa ba mai kyau bane, meyasa ta biye ma k'awayenta da suke aikatawa har suka dulmiyar da ita wanda a yanzu su kansu basu san tana yi ba, ganin suna yi tana ganin suna rayuwarsu ba tare da sunji komai ba yasa taga itama zata iya, Anya kuwa tayi ma kanta adalci kuwa? Hawaye ne ya zubo mata a idanunta tasa hannu ta share.

Mommy ce ta shigo d'akin ta dubeta, ganin yanayin da take ciki yasa ta k'araso wurinta da sauri ta rik'eta tace. "Daughter meke damunki haka kike hawaye." Ta idasa maganar tana mai share mata hawayen daya k'ara biyo kuncinta.

Tace. "Mommy kaina ke ciwo." Ta idasa maganar tana mai kwantawa a jikin Mommy."

Tace. "Haba shine to abin kuka? Ba sai ki mik'e kije ga first aid box ki d'auki magani kisha ba, ai kukan k'ara maki da ciwon zai yi." Da kanta ta mik'e taje ta d'auko mata maganin da ruwa ta mik'a mata ta sha. Komawa tayi ta kwanta. Mommy ta bita da kallo cikin kulawa tace. "Idan fa wani abu na dumunki kada ki boye min ki sanar dani." Da sauri tace "A'a Mommy bakomai." Tayi maganar tana mai k'ok'arin maida hawayen da yake shirin zubo mata.

Mik'ewa tayi tana mai shafa kanta ta fice had'i da ja mata k'ofar d'akin. Dogon ajiyar zuciya ta sauke tana mai runtse idanunta da ya bama wasu guntun hawayenta zubowa.

***
Washegari kuwa tun da wuri ta gama shirin makaranta ba tare da tayi yunk'urin karyawa ba tayi ma Mommy sallama, kallonta tayi tace. "Ya naga zaki fita ba tare da kin yi break ba?" Kanta na k'asa tace. "A'a Mommy sauri nake yi shiyasa." Tana idasa maganar ta tafi. Binta da kallo Mommy tayi tana mai tunanin tabbas akwai abinda ke damun Humaira a ranta.

Koda Humaira ta isa School haka ta wuni a can sukuku da ita. Tunaninta idan ta mutu mai zata fad'a ma Allah tunda ta san abinda take yi ba mai kyau bane. Haka ta dawo gida wata iri da ita. Tunda ta shigo Yaya Jawad ya tsareta a palour da fira haka ta zauna ba dan ranta yaso ba sai dan bata so Mommy ta fahimci komai.

Tashin Mommy a wurin yasa ta d'an dubeshi tace. "Yaya Jawad ya kamata fa muyi ma kanmu fad'a mu san mai yuwuwa dan irin haka ba zai fishshemu ba." Tashi yayi daga kujerar da yake ya dawo kusa da ita ya zauna. D'an matsawa kad'an tayi, ya kalleta da murmushi yace.

"Guduna kuma kike? Humaira kina maganar mai yuwuwa zamu yi auran nan fa kada ki damu, ki saki jikinki dani nan bada jimawa ba zamu yi aure. Da kin shiga level 2."

Ajiyar zuciya ta sauke tace. "To Yaya mai zai hana mu fad'a ma Mommy sai ta fad'a ma Daddy?" Waro idanu waje yayi yace. "Kai kada ki kuskura yanzu ai sai kuyi fad'a da Daddy, gara ki bari karatunki yayi nisa." Duk'ar da kanta k'asa tayi ba tare da tace mashi komai ba, sai tunanin data sani take data dawo kaduna da zama.

Mik'ewa tayi ta fara tafiya, sunanta ya kira cikin wani yanayin murya. "Humaraaa.."

Tsayawa tayi cak ba tare data juyo ba. "Tafiya zaki yi ki barni ni kad'ai?" D'an lumshe idanunta tayi ba tare da hakan yasa ta juyo ba taci gaba da tafiya. D'akinta ta shige ta turo k'ofar har da sa key dan kada ma ya shigo. Samun wuri tayi ta zauna ta sauke dogon ajiyar zuciya. Tabbas idan har haka zamu ci gaba da zama da Yaya Jawad akwai ranar da za a samu matsala tabbas. Maida kanta tayi jikin gado had'i da jinginar da kanta tana girgiza k'afafunta.

*** ***
Yau gidan ta tashi shiru tunda Mommy ta fita bikin d'iyar k'awarta take d'aki kwance, dan Mommy ma sai da tace ta shirya suje tace ba zata ba. Waya ta d'auka ta kira Hajja suka yi ta faman fira, shigowan Yaya Jawad d'akin ne yasa ta d'ago ta kalleshi. Yace. "Ke da wa kike ta waya haka kina dariya?"

Tana ci gaba da dariyar tace. "Ai ka san ba wanda zanyi waya dashi in samu farin ciki haka in ba Hajja ba." Yana murmushi ya k'araso ya fige wayar ya kara akan kunnanshi had'i da cewa. "Tsohuwa mai ran k'arfe ranki shi dad'e." Tace "Ai kai Jawad ina nan ina jiranka yaushe rabon da in saka a idanuna."

Amsa ya bata da cewa. "Kada ki damu ina nan zuwa, aiyuka ne suka min yawa. Sun d'an ta'ba fira ya mik'a ma Humaira suka yi sallama itama ganin ya tsaya yana kallonta. Yace. "Humaira coffee nake so please." Tace.

"Kai Yaya Jawad har da rana ba zaka ha'kura ba?" Yace baki ga yanayin da muke ciki ba sanyi fa ake ai kinga sai da abu mai d'umi." Tace. "To ai Talatu na nan ba sai ta had'a maka ba." Ma'ke kafad'a yayi yace. "Nak'i naki nake so, ina d'aki ina jiranki." Yana gama fad'a yasa kai ya fice. Tana k'unk'une ta mik'e ta fita tayi kitchen, tana gama had'awa ta d'aura a kan d'an k'aramin tray ta fita, d'akinshi ta shiga da sallama. Ya amsa ta aje a gabanshi, d'auka yayi ya fara sha ta mik'e zata tafi. Kallonta yayi had'i da cewa. "Ina kuma zaki?"

Ba tare da ta kalleshi ba tace. "D'aki mana akwai abinda zanyi."

"Zauna ina son muyi wata muhimmiyar magana." Samun wuri tayi ta zauna fuskarta a d'aure dan ta d'auki aniyar ba zata k'ara yarda ta biye mashi ba. "Kallonta yayi ya d'an saki murmushi kana yace mata.

"Wai Humaira mai yasa kike guduna haka? Nine fa naki Yaya Jawad." Ya idasa maganar yana mai d'ago da ha'barta. K'ara d'aure fuskarta tayi yanda ka san bata ta'ba dariya ba.

"Jibeta d'aurewar ma ko kyau bai mata ba." Har yanzu fuskarta a d'aure take tace. "Ina so zan shiga ciki akwai abinda zanyi." Kallonta yake da mamaki dan bai ta'ba tunanin Humaira zata iya had'e mashi girar sama data k'asa ba.

_____________

Sai kuna yi kuna ha'kuri dani sbd kin typing da nake Allah ya bani ikon ci gaba da maku.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 01, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JINI D'AYAWhere stories live. Discover now