*JINI D'AYA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Wattpad@Ayshatmadu*
*14*
Tunda ta dawo yau satinta d'aya ko ina bata je ba, sai zaman sa Hajja surutu da take. Hajja ce ta dubeta tace. "Kai ni yau na bani da wannan yarinya, wai ba inda zaki ne tunda kika dawo kin'ki fita sai kace mugun abu?"Humaira kallonta tayi tana dariya ciki-ciki tace. "Au Hajja korata kike? To bari in tashi in k'ara gaba." Da sauri Hajja tace.
"Kije ina kuma?" Tace. "Inda nafi wayau mana tunda kin gaji dani ba sai in tafi ba." Hajja tace. "Ke ni bana son sakarci, naga ne tunda kika dawo ko gidan iyayenki baki je kin gaidasu ba, gashi har kinyi sati d'aya." Humaira na dariya tace.
"Uhm! Kaga su Hajja har an tsorata ba a son rabuwa dani, gashi kuma tafiyar zanyi." Hajja tace. "Ni dai ya kamata dai kije ki gaida 'yanuwanki ko?" Tace. "To Hajja Insha Allahu zanje, amma yau ina da ba'ki sai dai gobe na shirya naje."
Mi'kewa tayi ta fita ta zauna tare dasu Adama suna fira, jin sallama tayi, da gudu ta mik'e had'i da ihu ta d'aresu tana murna. Sumy ce ta kalleta tace. "Na bani Humaira har yanzu halinki na nan ba zaki girma ba." Hajja ce ta fito da sauri ganin abinda ke faruwa tayi tsaki had'i da cewa.
"Mutts! Kede ko Humaira gaba d'aya wallahi ta bani tsoro Allah ya shiryeki." Adama tace. "Ni kaina wallahi sai da na firgita wannan uban ihu data buga." Hajja tace. "Wato kunji labarin k'awarku tazo shiyasa kuka zo ko? Ashe zan k'ara ganinku?"
Humaira tace "Wato Hajja basa zuwa gaidaki kenan? Kun kyauta." Sumy tace. "Wallahi ba haka bane makaranta ne ya 'boyeni." Humaira tace. "To ke dai nayi maki uziri amma su Halima kam ba zan masu ba."
Halima da Rukayya suka ce. "A'a Hajja ayi ha'kuri zamu rin'ka zuwa." Hajja tace. "Ku dai kuka sani." Dariya suka yi.
Jansu tayi suka yi d'aki suka zauna, fita tayi ta kawo masu ruwa ta dawo ta zauna. "Iye ka gansu kowa ya k'ara girma masha Allah.!"
Ruky tace. "Ke kuma fa baki ga yanda kika koma ba? Ai na zaci a hoto ne kawai ashe har a fili, lallai ba k'aramin amsarki kaduna tayi ba." Dariya tayi tace. "Bari in lalubo maku wad'annan yaran." Sumy tace. "Suwa kenan?"
Tace. "Su Farouk mana." Halima tace "Za dai ki kirasu su damemu dai wallahi." Tace. "Ai dama sun fad'a min zasu zo sai gashi kun rigasu zuwa." Suna tsaka da fira suka ji sallamarsu. Gaida Hajja dake tsakar gida suka yi tace. "Ban amsawa sai yau kuma nake ganinku?" Sosa kai suka hau yi, Humaira ta fito tace. "Kai ku shigo kada Hajja ta tasaku da surutu."
Deen ne ya dubeta bayan sun shigo yace. "Kai mutuniyar ashe duk kallon da muke maki a haka kin wuce yanda muka gani? Wai kin ganki kuwa gaskiya kaduna ta amsheki 'yar yarinya." Harararshi tayi tace.
"Lallai Deen wuyanka ya isa yanka, ni zaka kalla kace ma yarinya, ai ku kuka canza bani ba." Mubarak yace. "Ke baki lura da canzawar da kika yi ba? Wai ya maganar soyayayyarmu ne dan har yanzu fa ina ciki?" Dariya suka yi tace.
"Amma yaron nan baka da kunya, ana harkar manya mai za ayi da kai, ko kunga laifina." Dariya suka k'ara yi, Sumy tace. "Oh kinci moriyar ganga zaki yada koranta ko? Ai naga a da a school baki da tamkar Mubarak wato d'an cock da snacks kin gama amsa ko?"
Dariya tace. "Hmm! Har kin d'an bani budurwar dariya dan abin ya girmi bazawarar dariya, baki ji da kika ce ba, ai yanzu muke harkar girma." Kallonta yayi yace. "Aiko baki isa ba dole muci gaba da soyayya, dama kanainayeni da kike a waya duk na yaudara ne? Wai waye kika samu ne da ya fini?" Dariya suka k'ara yi. Nan suka zauna suna ta tuna rayuwar makaranta suna dariya.
Sun dad'e sannan su Deen suka tafi, nan suka bar su Ruky suna fira. Sumy sarkin son jin labari ta dubi Humaira tace. "K'awa wai ya nake ta jin kina maganar wani ne? Ko kin samo mana d'an kaduna ne?" Juya idanunta tayi tace.
"Ba yanzu zaku ji ba sai nan gaba zan fad'a maku." Fati tace. "Haba tsakaninmu akwai jan rai ne, kin dai sani ko waya ne muna fad'a maki halin da muke ciki, sai ke zaki 'boye mana. Kina kaduna fa muka kiraki muka fad'a maki za a sa ma Ruky rana."
D'an dariya tayi tace. Wallahi lokacin da kuka fad'a min ba k'aramin dad'i naji ba, dan a yanzu nafi son inga gaba d'ayanmu munyi aure. Dan yanzu rayuwa ta lalace gani nake a yanzu a zamanin nan da muke ciki kamar ba mazan arzi'ki. Burin samarin yanzu su 'bata tarbiyar da iyaye suka dad'e suna ginawa. Shiyasa yanzu nafi son inyi aure da Allah ya kawo min na gari." Fatima ce ta k'ara magana.
"Wai hala kin had'u da irinsu a kaduna ne? Dan na san kaduna bariki ce, akwai halittu kala-kala." Duka Humaira ta kai mata tace. "Dama ai ke sarkin son jin gulma gareki, to ni ban had'u da irinsu ba, ina dai fad'a maku yanda yanzu rayuwar ta lalace ne." Sumy tace. "Gaskiya kam yanzu zamanin nan da muke ciki sai dai addu'a, sai kuma wanda Allah ya tsare."
Sun dad'e gaba d'ayansu suna tattaunawa akan wannan matsalar ta halin da matasanmu suke ciki, dan sai kaga mutun gashi ya san ba kyau ya san tabbas Allah zai kamashi akan laifin, amma son zuciya sai ya rufe mana idanu muna ganin hakan kamar dai-dai ne, kamar kuma ba zamu mutu ba, to akwai lokacin mutuwar yana nan zuwa ko ka shirya ko baka shirya ba, Allah ya shiryemu ya k'ara tsare mana imaninmu Amin.
Shirin tafiya suka fara yi, kaya ta d'auko dogayen riguna ta mik'a masu, cikin farin ciki suka amsa. Sumy tace. "Allah sarki k'awar arzi'ki, har yanzu kyautarki na nan mun gode." D'an murmushi tayi tace. "To idan ka samu ai ka bada, dama tsarabarku ce na yo maku dan ban samu na fito ba shiyasa ban kawo maku ba."
Har bakin titi ta rakasu sannan ta dawo gida. D'akin Mallam Babba ta shiga ta taddashi zaune yana lazimi. Samun wuri tayi ta zauna tace. "Allah sarki tsohon kirki kana nan kana ta bauta, to a sani a addu'a."
Yana dariya yace. "Dama ai kullum kuna cikin addu'ata, ina nan ina maku tare da sa maku albarka a kullum." Tace "Allah sarki Mallam shiyasa a kullum nake alfahari da gode ma Allah da kasancewata cikin ahalin gidanka."
Yace. "Nima ina alfahari da samunku da nayi, wai meyasa tunda kika zo baki zuwa ki amshi rubutu kisha, yanzu gashi ki sha." Ya idasa maganar yana mai tsiyaya mata a kofi. Zum'buro baki tayi tana kallonshi ya mik'a mata. Amsa tayi ta shanye ba dan ranta yaso ba ta mik'a mashi kofin. Murmushi kawai yayi dan dama ya riga da ya san halinta bata so ya bata. Mi'kewa tayi ta mashi sallama ta koma wurin Hajja ta zauna. Hajja ta dubeta tace.
"Ke kuma lafiya na ganki haka?" Tace "Ni da tsohon nan ne yayi ta d'inkirama mutane rubutu, inda yana tsiro da yanzu yayi ma mutane a jiki."
Hajja tace. "Yau naga ikon Allah da wannan yarinya, to ai taimakonki yake, gara idan ma zaki sha ki sha da zuciya d'aya ko zaki samu yayi maki aiki. Sai nan gaba zaki ji dad'in abin nan da yake maki, ba cutarki yake ba rubutu ne na tsarin jiki."
Humaira tace. "To ai yanda na sha shekara da shekaru yaci ai na daina sha, tunda ai kad'an ma ya isa ba ayi ta abu d'aya ba." Binta da kallo kawai Hajja tayi dan tama rasa mai zata ce mata, sai dai ta saki baki tana kallonta. Dariya Humaira tayi dan ta san sau tari idan Hajja ta rasa abin ce mata sai dai ta bita da ido, dan idan har ta biye mata sai dai tayi ta haya'kata.
"To yanzu kuma miye abin dariya da zaki ta sani da dariya kin dai san bana son dariyar nan taki ko."
Dafa Hajja tayi wanda har yanzu tana dariyar tace. "Kwantar hajiya jajjata ta kaina ina sonki zan barki."
Hajja tace."Ai ni gara ma kiyi ki tafi, wai yaushe zaki tafi ne?"
"Au Hajja har kin gaji da ganina? Shikenan bakomai zan tafi." Ta mik'e ta yi d'akinta Hajja ta bita da kallo tana 'yar dariya.
______________________________
Sai kun rin'ka ha'kuri dani typing na bani wahala shiyasa kuke ganin kad'an

YOU ARE READING
JINI D'AYA
Fiksi Penggemarcikin d'aga murya mai rikitarwa yayi magana wanda yasa tayi saurin d'ago da rinannun idanunta da suka rine daga kalar fari suka koma ja. "ina so ki fita a harkata, mace wadda ta san mutuncin kanta nake so na aura ba ba wadda ta watsar da nata a titi...