chapter 2

55 7 0
                                    


          
            TARKON SO

Da misalin karfe 11:30am, alhaji Aslam ya sauke hajiya Amatullah a kusa da gidan su Afrah. Ta shiga da sallama inna Larai ta amsamata ta samu wuri ta xauna a tabarma sai inna Larai tace baiwar Allah daga ina? Wa kike nema? Tace wata ce tayi mun kwatancen gidannan danace mata ina neman mai aiki shine kika ganni anan dan Allah ki taimaka mun da 'yarkaramar yarinya wacca xata dunga taimaka mun wajan aikace-aikace, tace aiko kinxo gidan da xaki samu 'yar aiki amma fa 'yar karama ce dan ko shekara mai xuwa awatan mayu xatacika bakwai, tace babu komai inna Larai tace dai kuma baki fada mun adadin albashin da xaki dunga biyanmu ba tace dubu biyune da dari biyar tace to shikenan mun gode.
Hajiya Amatu tace sai dai xanso ta dunga kwana a gidana tace lah ai babu komai ki tafi da ita sai tace to ina yarinyar take "yanxu xata shigo nadan aiketane... inji inna Larai.”
Haka ta xauna tana jiranta can sai gata ta shiga dauke da nika akai da kyar take tafiya saboda nauyin nikan, hajia Amatullah ne ta tayata saukewa aranta tana Allah wadai da mutane irin wannan matar. Inna Larai tace yi maxa kije ki kwaso kayanki xaki bi wannan baiwar Allah din ki dinga tayata aiki, tace toh.
Haka ta shiga ta kwaso kodaddun kayanta Wanda saboda tsufa sun soma yagewa ga uban datti. Tace naga baki tambaye ni inda nake da xamaba kar inxo inki kawo maki kudin ko 'yarki. Inna Larai tayi murmushi tace na yarda da Allah haka ma na yarda da ke nasan ba xa ki cuceniba tace duk da haka ya kamata kisan gidana tace ba komai hajiya kuje Allah na tare da mu.
Axuciyar ta tace uhm! Allah a baki amma cuta da mugunta a xuci tace to shikenan nagode ta kalla Afrah tace ke muje. Haka ta tasa Afrah agaba har suka shiga cikin mota tana ganin Alhaji Aslam tace lah dady?! ina kwana yayi dariya yace lfy lau Afrah ya gida? Tace lafiya lau.
Haka kawai hajiya Amatu taji Afrah ta kwanta mata arai gata tubarkallah haka suka isa gidan. Tsayawa kawai tayi tana kallon gidan, hajiya amatu tace karkidamu Afrah sai kin gaji da ganin gidannan tayi dariya ta jata suka shiga ciki ta hada mata wani kakkauran shayi da bread da fried egg ta xauna taci tayi nak tace nagode inna, tace ni ba sunanta inna ba kice min mummy tace to nagode momi.
Tace cire kayanki anan kixo muje tace to ta tube kayan ta gaba daya sannan tabita bayi suka shiga inda ta tsefe mata daburtaccen kitsonta guda biyu ta wanke mata kanta tsaf tayi mata brush sannan tayi mata wanka har sau biyu sbd tsananin dauda na rashin kulawa da wanka, da suka gama suka futo ta shafeta da cream mai kamshi ta busar mata da gashinta da hand dryer sannan ta gyara mata gashi.
Ta bude wardrobe mai cike da kaya saiti saiti, na English wears, jallabiyoyi (after dress) da dai sauransu, sai ta dakko riga da wando a bangaren English wears ta saka mata sannan ta fesa mata turare na Onde Vertige sai ga Afrah ta fito acan acan kamar balarabiya.
          Sai ta kaita parlour ta samata Tom and Jerry tace xauna kiyi kallo. Nan ta xauna tanata kallo har barci ya dauketa.
          Da misalin 3:30pm sai ga yaran gidan sun dawo daga makaranta suna ganin Afrah suka tsaya cak suna kallon ta itama din kallonsu takeyi bata cemasu komaiba suma basuce mata kala ba, daga bisani babban cikinsu yace kuxo muje mucire uniform dinmu mana suka wuce ciki suka barta a wajan.
          Bayan kowannen su ya canxa kaya sai suka futo suka nufi dinning table Inda suka tarar already hajiya Amatu ta fara serving dinsu, suka xaxxauna sai wani daga cikinsu yace mummy wacece wannan beautiful gale din a parlour mai kama da sis Aneesah? Tayi murmushi tace itama sister dinku ce kuma sunanta Afrah.
          Aneesa tace anan xata dunga kwana? tace eh mana tare xaku dunga kwana a dakinki tayi dariya tace nima yanxu ina da sister mai kyau. Alqasim yace nima haka ina da sisters guda biyu masu kyau. Aneesah ta kalla dayan wanda tunda suka fara magana bai samasu baki ba tace yaya kaifa? Kaima kana sonta? Yagyada kai batare da ya kalletaba tayi dariya tace shima yaya yaji dadi...
           Da karfe 4:00pm suka shirya suka tafi islamiya tare da Afrah, Mummy taba Mukhtar kudin registration din aka mata interview aka sata a aji daya (nursery one) shi kuma ya wuce nashi ajin, da aka tashi suka dungumo tare suka dawo.
          MUKHTAR shine da na fari ga alhaji Aslam da hajiya Amatullah, shekarar shi 15 yana kuma JSS3 ne. Mukhtar yaro me tamkar dubu, yana da tsananin ladabi da biyayya ga kyau ga kokari. Sai ALQASIM, shine na biyu a wurin iyayenshi, yanada shekara 11 yana kuma primary 5 ne. Sai na uku kuma ta qarshen su itace ANEESAH, 'yar shekara bakwai tana kuma primary 1 ne...
       
                           ***

Wai inna ina Afrah tajene tun dana shigo gidan nan nake ta kiranta amma shiru nakeji tace wlh wata baiwar Allah ce taxo ta dauketa wai xata dunga tayata yin aikace aikace, tabe baki tayi tace nawa xata dunga biyanta? "dubu biyu da Dari biyar ne" tace kash Inna! dani kikace tadauka wlh da kila dubu goma xata dunga biyana tayi tsaki "Allah ya kyauta indauka 'yata inbada tana ma wasu aiki alhalin koni bansan suba (kujifa!) sai wasu bare wanda bansan usulinsu ba. Ta turo baki tana kunkunai tace ni dama nasan bason ganin cigaba na kikeyi ba...

LOVE WEB(tarkon so)Where stories live. Discover now