chapter 20

39 6 1
                                    

       💖💖💖💖💖💖💖💖💖

              ***tarkon so ***

Yanxu kowa yasan cewa Emily din muktar bata mutu ba tana  nan da ranta domin kara tabbatar wa mukhtar yaje office yanemi leave na sati daya domin xuwa ganinta a spain sukaki bashi wai hutun daya dauka wannan shekarar tayi yawa dakyar dai yasamu suka bashi kwana uku.yayi masu godiya yakoma gida domin shiryawa.dama already yafada ma yan gida.afrah kodata dawo gidane takejin labarin tafiyarshi gobe.hankalinta idan yayi dubu to ya tashi,tarasa inda xata sa kanta taji dadi kawai kai tsaye ta wuce dakinshi takwan kwasa tare da sallama yana xaune yana hada kayanshi acikin akwati ya amsa mata sallaman tashiga kafun yayi magana tace yaya karkaje spain dinnan fuska adaure ya juyo ya kalleta"futar mun daga daki indai abun daya kawo ki dakina kenan im busy.."ta girgixa kai"nima ai yaya  kawarkace kaga ai ina da..."can you hear yourself afee?this is my girlfriend we are talking about fa kina wani fada mun wai kar inje inganta, kina tunani kuwa?."
wani abu taji ya tokare mata kirji,nandanan ko idon ta ya ciko da kwalla.murya na rawa tace shikenan to yaya Allah ya kiyaye hanya ka gaida mun da emily.ta juya ta futa xuciyarta na kuna tana mai daukan alwashin cire sonshi axuciyarta kata wani haline.
ta shiga daki fuskarta a cunkushe da an ganta xa asan kadan take jira tafashe da kuka.aneesah ta kalleta tace hakurifa xakiyi da yaya afee.ta kalla aneesa tace anee tun farko dama nice ke son shi dan haka yanxu ma nice xan daina sonshi,na hakura da yaya na bar ma emily shi.ta girgixa kai"hmm afee kidaina fadin haka,inada yakinin cewa big b na son ki sosai dan kawai yana murnan dawowar emily ne shiyasa kika ga yana xumudin xuwa ganin ta tace koma menene na hakura dashi.  tana gama fadin haka sai ga hawaye shar!.
        daxe tafi ma ko sallama bata mashiba tana kwance a daki tana kokarin ganin batayi kukaba amma abun ya faskara,ta tashi kawai ta shige bayi ta sharba kukan ta har tagode ma Allah.data gaji daxaman dakin tafuto falo taxauna tayi shiru lost in thought sai ga alqasim yashigo,ya dawo daga rakiyar mukhtar.ganin hankalinta kwatakwata baya jikinta yasa hannunshi ya rufe mata ido ta baya.firgigit tayi xata fasa ihu yasa hannayenshi biyu ya rufe mata baki yana dariya yace"to matsoraciya nine bakowa ba,ina hankalinki yajene da bakiji shigowataba?"
  tayi murmushi"ba ko ina doctor"yayi murmushi tare da xagayowa ya xauna kusa da ita sannan ya kalleta itama ta juya gareshi yace"so tell me when was it?"cikin rashin fahimta tace menene?yace yaushe kika fara son yaya?
ta xaro ido  tanan kallonshi xuciyarta na bugawa da sauri.ya daga mata gira"yes!angaya maki bansani bane?"
ta kauda kai"taya akayi ka sani?"yayi yar dariya yace afee kenan nifa yayan kine kar kiga danna dade a  kasar waje ki dauka bansan halin da kowannen ku yake ciki ba hardashi yayan.anyway rannan dakika barmin wayarki na duba na ga hotunanshine duk a ciki sannan kuma na shiga draft dinki naga abun dakika rubuta game dashi"ya matso kusa da ita sosai cikin rada yace harda kiss din dakukayi sharing.
ya koma yadda ya ke xaune kafun ya matso.ita kuma ta kauda kai idonta na xubarda hawaye"to ai yayan baya sona emily yakeso"
"waya ce maki baya sonki?"ta kalleshi da sauri "dagaske yana sona?taya akayi kasani?" yagirgixa kai yace "saboda nasan halin yaya ciki da bai haka kuma nasan yana sonki girmankai da miskilanci irin nashine yahanashi fahimtar haka amma karki damu i will help you get him"
ta kura mashi ido tana tunanin yadda hakan xe kasance.ta sauke numfashi"ta yaya xaka taimakamun?"yayi dariya"plan xamu hada nidake amma sai kin yarda"da sauri ta gyada kai"na yarda wlh doctor xanyi!"
yace first miko mun wayarki tace yana daki barina je na dauko.ta mike ta yi hanyar daki can sai gata ta futo rike da wayarta ta xauna sannan ta mika mashi ya bude marfin wayar ya ciro sim card dinta ya kalleta yace yaya xe iya kiranki at anytime kuma baxe samekiba tace 'meyasa?' yace saboda kin canxa number anjima xamufuta musiyo sabon sim card taxaro ido tace to contacts dina fa yace kisamu waje ki kwafe su a ciki ta sauke numfashi to amma doctor da layin na bude account dina fa da sauran abubuwana musamman ma na sch ya gyada kai kinyi gaskiya kuma a wannan to basai mun siyo wani sabon sim card ba,kici gaba da amfani da wannan din sai kawai kiyi blocking numban shi koda yakira ki baxe same kiba tagyada kai to shikenan.
'yawwa abu na biyu kuma shine ki daina kula shi kamar da,kinsan shi baya son takura so kidaina sakin mashi jiki kamar yadda kikeyi abaya kar kuma kisake aikata abun da kukayi rannan,i mean it afee kar ki kara yunkurin kissing din shi ba girman ki bane kuma ba mutuncin ki bane kinajina?dan emily tayi mashi ta same shi bayana nufin kema sai kinyiba kina 'yar musulma."ta girgixa kai wlh nima yaya lokacin danayi nayi regretting din shi sosai kuma insha Allahu baxan kara ba"yace better!abu na uku kuma shine xamu dunga pretending as lovers duk lokacin dayake nan,ina nufin I'll call you a phone mudunga fira irin na saurayi da budurwa da dai sauransu kin amince? tayi dariya harda tafi na amince sosai ma doctor yaya...

Wat do you think?plan dinnan xe yiwu kuwa?kokodai tahakura dashi din kawai xefi?
Sorry for the late update 😍😍😍

LOVE WEB(tarkon so)Where stories live. Discover now