chapter 1

103 8 0
                                    

TARKON SO

Tuki yakeyi a hankali yana sauraron karatun shahararran malamin nan mai suna sudais a cikin suratul bakarah. Kamar ance ya juya sai ya hango wata karamar yarinya a tsugunne wacce baxata wuce shekara shida xuwa bakwai ba, kuka take kamar ranta xai futa gata busubusu kamar wacce ta futo daga bola abun gwanin ban tausayi.

Yayi parking Mota a gefen titi ya kashe karatun sannan ya futo ya kulle motar ya karasa wurinta ya tsugunna ya tabota a hankali, cikin tsoro ta dago kai shi kuma yana ganinta gabanshi ya fadi saboda tsananin kyanta.

Axuciyarshi yace shikenan naja makaina, na hadu da aljana kuma nasan babu mai rabani da ita yau sai Allah.

Idonta jawur tadago tana kallon shi, yayi sauri ya sai ta kanshi yana mai addua axuciyarshi yayi murmushi yace baby meyasa kike kuka? cikin muryar shagwaba tace ba inna larai bace tayi min duka ba!

Yace meyasa ta dakeki? Kinyi mata laifi ne ko? Da sauri tace banyi mata komai ba tacene inje insiyar mata da kayan miya shine wasu mutane guda biyu suka siya danace su bani kudin sai dayan cikin su ya dakeni yace in wuce gida baxa a badaba.

          Shine da naje gida na fada ma inna Larai, shine ta dauka muciya tayi ta duka na dashi.

           Tace infuta inje in nemo mata kudinta inbahaka ba wai kar indawo mata gida in kuma na dawo sai ta kashe ni na tafi lahira kamar yadda innata da abbana suka tafi.

Yace "subhanallah! dama ba ita ta haifekiba? "tace nima ban Sani ba inna larai tace mun wai innata ta mutu, kuma ni ban San hanyar xuwa lahira ba dana gudu wajan innata da abbana tunda dai kullum inna sai ta dakeni”.

Ya girgixa kai yace yanxu nawane kudin? maimakon tafada mashi sai tafara kirgawa da 'yan yatsunta tace guda haka ne kayan miyar tana nuna mashi duka ya tsunta yace to nawa nawa ne? Tace goma goma ne! mamaki da takaici suka kamashi, saboda Allah yanxu dan naira dari matar nan tayi maki irin wannan dukan? Da sauri tace dan Allah ka barni in bika in samo mata kudin yace meyasa xaki bini?

"To ai inna larai tace inbi namiji insamo mata kudinta kaga kuma ai kai namiji ne"a fadarta. Yayi dariya axuciyarshi shi ya ce yaro yarone.

Ya ruko mata hannu ba tareda jin kyamarta ba yace kina xuwa islamiya? Ta girgixa kai “da ina xuwa har da boko amma yanxu bana xuwa saboda inna larai ta hanani wai babu wanda xai dunga kai mata tallah" ya gyada kai.

Yace to bara kiji babu kyau mace tabi namiji kinga Kuma ke macece ko? Ta gyada kai yace ko kinaso kishiga wuta mai xafi sosai? Cikin tsoro tace a'a banaso yace good! toh duk macen databi namiji wuta take shiga tunda bakyaso ki shiga wuta ai baxakibi namiji bako? Tace eh baxan bishiba.

Yace yawwa haka nakeso amma kuma baki fada min sunankiba tace sunana Afrah amma inna Larai tana cemun aljana yace subhanallah! idan takara kiran ki da aljana karki kara amsawa kinji? Babu kyau.

Tace idan ban amsa ba xata dakeni kuma taki bani abinci yace INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN! Daman akwai irin wadanan mutanen a duniya? gaskiya innarki bata kyautawa, ita bata da 'ya'ya ne? Tace tana dasu guda haka tanuna mashi yatsunta guda hudu, da yaya Zulai, da yaya Ramatu, da yaya Hannatu, da wata 'yar kankanuwa bata iya magana sosai ba sunanta Mashida.

Yace su basa xuwa tallanne? Ta girgixa kai "basa xuwa sai dai suje gidan kawayensu" yace kefa ina naki kawayen? Ni banda kawaye ya girgixa kai yaciro makullin motarshi daga aljihu yace jirani anan ina xuwa tace toh! ya nufa motarshi ya bude ya xaro kudi daga aljihun kujerar ya futo ya kulle ya koma wurinta ya mika mata dari biyar yace ga kudin, tagirgixa kai "a'a baxan amsa ba inna Larai xata cemun kudin bai kaiba kuma ba irin wannan bane yace uhm! to kudin wani irine? Tace nima bansan kalarba alokacin ne ya gane abunda take nufi wato 'yan gomagoma dayawa.

Yace to xomuje musamo canji suka nufa wani shago yace dan Allah mallam xandan samu canjin dari biyar? Yace eh bari na duba ya ciro 'yan dari biyu guda biyu da naira dari guda daya ya mika mashi ya amsa dari biyar din sai yace kinga wannan shine naira dari wannan kuma Dari biyu cikin sauri tace wnnan ma dari biyu ko? Yayi murmushi yace eh ya mika mata ta amsa tace nagode Abba yace daddy xakice tace to nagode dady.

Yace to yi maxa ki tafi gida kar inna Larai tayi maki duka ta juya ta fara tafiya tana juyo wa tana mashi byebye sai da tasha kwana sannan ya fara binta abaya har ta shiga gida sannan ya koma.

Ko da isarta inna Larai tace kinko samo min kudin? Cikin murna tace eh gashi ta mika mata ta fusge tace shegiya aljana xaki jamun asara dako yau kin kwana awaje. Maxa wuce ki amso mun nika a gidan su kande mai nika, na ruga na biya kudin. Ta juya ta tafi...

             ***tarkon so***

Alhaji aslam yana kwance da daddare tare da matarshi hajia Amatullah. Tace wai ni yau alhaji me ya farune? Tunda kadawo naga kwata kwata baka walwala. Ya sauke ajiyar xuciya yace hmm! yau wani abun al'ajabi na gani ga tausayi shine nakasa cirewa araina tace menene wannan abun kuwa?!

          Nan ya labarta mata komai tace ikon Allah, yanxu ita yarinyar bata da dangin uwane kona uba? Yace Allah kadai yasan wannan, shiru sukayi kowannen su da abun dayake tunani. Can sai tace niko alhaji da sai ince mu dauko yarinyar nan ta dunga xama da mu a matsayin daughter din mu.

Yayi murmushi yace kamar kin shiga xuciyata kin gani amma kuma abun da kamar wuya, matarnan xata yarda kuwa? Tace aibaxa muje hakanan ba cewa xamuyi ta bamu ita a matsayin 'yar aiki albashin kuma xa a dunga aiko mata dashi kaga tunda tanason yarinyar ta wahala xata yarda ko ya kagani?

Yace hakane wannan dabara taki tayi yanxu mu bari gobe idan yarannan sun tafi makaranta sai muje mu daukota ko? Tace duk yadda kace haka xa a yi...

LOVE WEB(tarkon so)Where stories live. Discover now