chapter 11

44 6 0
                                    

            TARKON SO

       Da tafarka tajita garau babu wannan kasalan datakeji saidai kawai Dan daci2n da bakinta kemata.

      Tajuya taga mukhtar na kwance Yana barci. Takare ma dakin kallo sai ta fahimci cewa har yanxu a dakin mukhtar take sai takoma ta kwanta tacigaba da kallonshi tana murmushi.

     Sai da aka fara kiraye2n sallah ya farka itakuma tayi sauri ta rufe idanunta.ya juya ya kalleta yaga har yanxu barci take gashin kanta ya Dan rufe mata ido daya.

   Yasa hannu ya gyara mata sai taji wani yarr...

      Yasa bayan hannun shi ya taba mata goshi da nufin ji ko jikinta da xafi har yanxu sai yajita wayam babu xafi ko kadan alaman sauki ya samu kenan.sai yayi hamdala.

     Ya tashi ya nufa toilet ya dauro alwala ya wuce masallaci.yana futa ta tashi ta xauna na Dan mintoci kadan sannan ta Mike tafuta to koma dakinsu.

       Tana ko shiga aneesa tabita da ido giranta adage tace"afee kece kuwa?"

    Tadan harareta kadan "banganeba meyafaru?".

    "Ganinayi daxu dai dakyar kike tafiya Kuma da an kalleki ansan baki da cikakken lfy but yanxu Kuma na ganki garau Kamar bakiyi ciwo ba sai dai ramar da kikayi meye sirrin?"

    " Allah ne sirrin,shiya kawo mun sauki"

    "To Allah ya Kara kawo saukin"

    " AMIN..."sannan ta shige toilet dan dauro alwala.
   
    Shiko daya dawo yaga Bata nan ya sauke ajiyar xuciya yace" better".

   Direct ya wuce wajan side drawer dinshi ya jawo drawern farko ya lalubo simcard dinshi na Nigeria yasa a waya sannan yakikkira wanda yakeson Kira aciki harda Emily.
 
                             *****

     "Mummy wannan month dinne birthday nafa"cewar aneesah

  Hjy tace "itama  afee wannan month dinne,y not kuyi celebrating dinshi tare Kuma afrah I won't take no for an answer dan yakamata kema kiyi celebrating dinshi wannan karon"

   Tayi murmushi " duka abun dakika xe shi xa ayi sweet mum"

Tagyada Kai " but b4 DT mekike so in baki as a birthday gift?"
   
Tace " komamenene inaso!"
   
  Ta girgixa Kai " nafiso kifada mun"
   
  Sai tadan daga Kai tana tinani can tace"mum abu daya nakeso kiyimun.akan maganar nan dakikayimana ranarnan akan ko 300l baxa mu gama ba xa amana aure inaso kiyi hakuri kibarmu mugama karatun kafun ayi maganar aure"

   Hjy amatu tayi dariya irin na manyan matan nan tace
  
      "kunyi kadan yara nixakuyi wa wayau to karyar ku Tasha karya aure dai sai kunyi shi ko Kuna so ko ba kwaso sai dai ke afee xan iya daga maki kafa danki gama makaranta amma banda ke aneesah tunda dama kin girmeta"

Aneesah ta xumburo baki tana kunkuni

Hjy ta tabe baki tace

     "kuje wajan yayan ku ya kaiku inda ake buga IV in Kuma yaki kun huta dannidai Banda lokacin kaiku Kuma baxan bada motataba aje a bugamun shi abangoba"

Sukayi dariya aneesah tace   "mum  ai ita afee ta iya nine dai nasa tsoro nakasa iyawa sosai tace komadai menene nidai baxanbada motataba "

      afee tace"mum wanne venue yakamata muyi?"

   tace "kuyi a inda annesah tayi last two years mana"

tace "to aneesah tashi muje mu tambayo Yaya inxaikaimu"

  ta Mike ta Mika mata hannu suka tafi.

   As usual yana xaune yana magana da masoyiyarshi Emily.

  Suka yi sallama ya amsa sannan suka shiga ya dago Kai ya kallesu sai ya maida kanshi kan Emily dake kallonshi yace hold on Emy sannan ya Kara dagowa ya kallesu yace

  "Ya akayi ne?"

   aneesa ta kalla afrah wacce idonta yake cike da kwalla sbd kishi shima ya Kai dubanshi ga afrah ya yamutsa fuska

yace "meyasamu idon ki afee?"

ta  girgixa cikin rawar murya tace

   "Babu komai dama munaso mutambayo ko xaka kaimu inda ake buga IV card "

yace "baxan  iyaba go and find some one else"

aneesah tace
  
   " Yaya pls mum tace Bata da lokaci kuma baxata bamu motar ta ba wai karmu lalata mata"
  
     ya Kara yasina fuska yace

    "ku  wuce kubani wuri as u can see I'm also busy"

   Afrah tayi sauri tasa gwiwowinta akasa taja hannun aneesah itama tayi kneel down
  
   tace
    " Yaya pls kataimaka ka kaimu Dan Allah"

    emily  tace
        "babe  what's happening?"
   
    yace
         "dey r just asking me to take Dem somewhere and I can't coz I'm busy"
   
    Nan fa ta fara rokanshi nandanan ko ya amince
   
     yace
       " naji shikenan!"   

     kafun subashi amsa yace
       "but  baxan samu kaiku yauba saidai gobe in Allah ya kaimu"
   
     cikin murna suka Mike suna godiya yagyada tare da yarfa hannu alamun su wuce su bashi wuri suka just suka futa shikuma ya maida hankalinsuu ga Emily.
   
Aneesa ta kalla afrah wacca haryanxu idanunta da alamun kwalla

tace
  " afee meyafaru tace Babu komai mekika gani tace muna shiga dakin brother naga fuskarki ta canxa meyafaru tace kinsan Allah natsana Emily dinnan "
   
    tayi murmushi tace
       "  kishi kike yi afee bawai kin tsanetabane"
   
     ta kauda Kai tace nasani anee.na San kishi nakeyi Ni wlh bansan yadda akayi na xurfafa cikin sonshi ba dama ace yana mun rabin son danake mashi da abun yaxo da sauki amma ina he has no clue about my feelings towards him
    tace
      " don't worry lokacine xai fara sonki Danko naga alamun haka dagagareshi"

  ta dube ta tagirgixa kai
     " hmm barshi kawai ke dai Allah ya shige mana gaba"

  tace
    "Wai  mutane nawa xamu gayyatane?"

tace
  
     "as much as possible Dan kusan rabin classmates dina xan gayyato"

tace
       “ to shikenan nima haka xanyi"
 
   Da safe ya samesu a dinning suna cin abinci shima saiya Sami wuri kusa da afrah ya xauna ya amsa masu dakai.
 
   Da sannu a hankali ya fara cin abincin shi har ya cinye ya Mike yace ku shirya mutafi sannan ya wuce Suma suka kwashe kwanuka suka wuce daki domin shiryawa.

  Daga bisani sai gasu sun futo cikin shiga ta alfarma duk sunyi kyau.
 
Shima sai gashi ya futo sanye da English wears na t-shirt baki da wando na jeans shima baki sai ya sa black palm slippers

ya kallesu yace
    "muje ko "

yayi gaba suka bi bayan shi,ya shiga driver’s seat .

  aneesah tace
   " afee ki shiga gaba "

Babu  musu ta bude ta shiga ta kulle ita kuma aneesa ta shige baya.ya ko tada mota yarufe windows ya kunne AC sannan ya kunna music na Westlife.

   Babu Wanda yace komai har suka Kai wajan suka Gama abun da xasuyi aka fada masu ranar da xasu dawo su amsa mukhtar ya xaro kudi ya biya suka juya suka tafi.haka ma da xasu dawo Babu Wanda yayi magana har suka Isa gida...

LOVE WEB(tarkon so)Where stories live. Discover now