chapter 3

48 8 0
                                    

    💖💖💖💖💖💖💖💖💖

                TARKON SO

          Sister Afrah xomuje ki rakani dakin yaya Mukhtar ya koya mun assignment dina tace nidai babu ruwana baxan jeba saboda baya sona, tace waya cemaki bayasonki? Shima din fa yaji dadi dakika xo tace to meyasa baya min magana kamar yaya Alqasim? Tace toh ai shi yaya Mukhtar baya magana shiru-shirune shi, tace aw! Ashe shi kurma ne bansaniba tace ke bakurma bane yana magana amma ba sosai ba. Tayi dariya tace to muje ta rike mata hannu sukayi gaba.
          Kwankwasa kofar sukayi hade da yin sallama daga ciki aka amsa sai Aneesa tayi yunkurin bude kofa sai afrah tace ke, bai amsa ba xaki bude kofan? Tace ai ya amsa tace to nidai banjiba tace kedai mu shiga suka bude suka shiga.
          Xaune yake akan gado yana daddannan system dinshi da alama dai game yake bugawa Aneesah tace yaya, dan Allah ka koyamun wannan assignment din da aka bamu ban iya ba. Cikin karamar murya yace kawo mugani. Ita dai Afrah tana ta kallonshi, nan ya shiga koya mata sai daya tabbatar ta gane sannan ya dago kai ya kalla Afrah yaga shi take kallo yace ke kallamu ina naki assignment din? Ta xaro ido tace yaya sunana Afrah ba kallamu ba yace to Aafii ina littafinki? Ta kara cewa Afrah ne yaya A..FRAH yace to ni AAFII xan dunga cemaki tayi murmushi tace to yaya bani da littafi sai ya kalla Aneesah go and get her a new book, tace to ta tashi xata futa sai Afrah ma tayi yinkurin gashi sai tace Afrah ki jirani yanxu xan je in dawo ta gyada kai ta koma ta xauna. Can sai gata ta dawo dauke da wani sabon notebook ta mika ma Mukhtar ya amsa yace Aafii xonan! ta matsa kusa dashi ya fara koya mata karatun daidai da level dinta cikin lokaci kankani harta soma iyawa dayake dama ta ita ABCD, 1,2,3,4 da kuma 2,3 and 4 letter words sai data iya sosai sannan ya bata assignment wanda xatayi submitting washe gari (NB: ta iya rubutu). Suka tashi suka koma dakinsu.
          Lokacin da suka shirya kwanciya sai Aneesah tace Afrah bana fada maki cewa yaya nason ki ba! kikace a'a to bagashi ya koya maki karatuba! tayi murmushi, Aneesah tace amma fa yaya baya son mutum mara kokari, ranar danayi na biyar yace kar inkara mashi magana inba haka sai yayi min duka shine tun daga ranar na fara daukar 2nd ko 3rd position. Tace hu'um! yaya Alqasim fah? "shi babu ruwan shi kona karshe kika dauka baxai yimaki komai ba sai dai yace ki dada kokari...
          Tace nina na fison yaya Alqasim tace niko nafison big brother saboda yana da kyau kaman ke, tace ni nasan banda kyau saboda Inna Larai tace ni mummuna ce, Aneesa tace Allah Aafii kina da kyau, ta kwalo ido tace Aneesah sunana fa Afrah har kin manta ne? Tayi dariya tace a'ah ban manta ba sunanne yayi mun dadi kuma nima daga yanxu sunan xan dunga kiranki dashi, yaya Alqasim ma xanfada mashi ya dunga kiranki dashi tace to shikenan…

             ***tarkon so***

          Xango na farko akasa Afrah a makarantat boko inda akasata a primary 1, ita kuma Aneesah ta shiga primary 2, Alqasim jss1, sai Mukhtar ss1.
          Da aka tashi kowannensu ya halarci wurin mota harda Salman best friend din Mukhtar. Dayaga Afrah yace a'a wannan wacece? Alqasim yace kanwar muce sai ya kalla Mukhtar yace shine baka fada mun cewa kayi sabuwar kanwa ba, yayi banxa dashi ya shige mota suma sauran suka bi bayanshi.
          Haka driver ya fara jan mota ana ta fira tsakanin driver da yaran but banda Mukhtar shi tunda ya kama owners corner ya xauna bai kara cewa komai ba sai dai yayi ta kallon hanya.
          Shiko driver din a axuciyarshi tunanin hali irin na Mukhtar yake, shi tunda ya fara masu aiki bai taba ganin yayi magana ba illa kawai gaisuwa, anya ko ba aljanu gareshiba? aka sauke Salman akofar gidansu su kuma suka wuce.
          A karshen xango kowannensu ya futo da sakamako mai kyau musamman Afrah domin kuwa na takwas ta dauka out of 48, su sauran dama as usual Mukhtar na 1st yayi sai kuma Aneesah da Alqasim suka dauka na biyu. Alhaji Aslam yayi murna haka ya kwashe dukkansu suka tafi South Africa yin hutu.
                 A can South Africa
          Alhaji Aslam ya siyo double espresso coffee sai yace a hada a aika ma Mukhtar yasha yaji inyayi mashi sai a siyo da yawa inkuma baiyi ba sai a canxo.
          Da aka hada sai aka mika ma Afrah akace taje ta kaimashi ya amsa ta juya da dan gudu gudunta ko sallama batayi ba ta fada dakin batare da ta lura da akwatishi dake hanya ba, ai gata akasa gaba daya coffee din hannunta yayi spilling akan kan kayanshi da yake shiryawa.
          Haushi ya kama shi yace ke wace irin wawuyace mara hankali? Kin ruqo abu mai xafi kuma kina gudu, shin bakinki na maki ciwo ne da baxa ki iyayin sallama ba? Gaki doluwa bakisan komai ba kinje kin dauko na takwas sauran arba'in din dakika bari abaya me suka maki da baki daukesu ba? kokuma wanda ya dauka na daya kaibiyu gareshi ko uku?  
Sai rawar kai da surutun tsiya to listen and listen good daga yau karkikara mun magana balle kallo if not sai ranki ya baci because I hate talking to dull and foolish people like you, tashi ki bace mun daga gani!
          Da kukan ta tatashi ta tafi Mummy tace kedawaye? (cikin kuka) tace ba yaya Mukhtar bane yace kar inkara mashi magana saboda na fadi na xubar da coffee din kuma wai banda kokari, tace rabudashi yi hakuri wayace mashi baki da kokari? Kina da kokari sosaima! kyaleshi kinji, haka akayita lallashinta aka kara hada wani coffee din aka ba Aneesah ta kaimashi.
Suka karasa hutunsu suka koma.

                     *  *  *

             (Nigeria)

          Ko da suka dawo gida Nigeria, babu abundake hadasu ko dan lesson dinnan dayake mata ya daina, magana ma bata hadasu. Ita kuma Afrah ta koma shiru shiru Aneesah tace Aafii dan yaya yayimaki fada shiyasa kika damu haka? Bakyason magana kin koma so quiet! tace bahaka bane, kawai banaso munayin fada da big brother ne ta gyada kai tace Aaifa kin dunga samun matsala da shikenan har sai kin gyara result dinky, kifi da kokari.Da haka suka rufe shafin.
          Koda suka koma school bata bari wasa yayi gaba da hankalinta kamar na first term ba kawayenta ma duk sun lura da yanayin ta na kin shiga cikinsu sai suyi tamata fada saidai tayi murmushi ta share su, haka harsuka gama term din taxo na biyar (5th). Maimakon tayi murna sai tasamu kanta da maijin tsoro da haushi saiga Afrah tana kuka harsuka kai gida, kowa yana ta tayata murna ana cewa tayi kokari amma banda gogan naka danshi ko kallo bata isheshiba balle magana...           

LOVE WEB(tarkon so)Where stories live. Discover now