chapter 5

45 6 0
                                    

TARKON SO
          Dawowar Mukhtar daga Spain bayan shekara biyar da rabi yasa kowa na gidan murna musamman su Aneesah don Alqasim already ya tafi Cambridge University dake London yana karantar medicine.
           Kwana biyu da dawowarshi ya koma kamar yadda yake na miskilanci. Salman ma yaxo gidan don gaisheshi, yadade agidan suna firan yaushe gamo, nan yake tambayar shi lafiyar Emily dayake ya santa ta waya da kuma Skype yace lafiya lau tare da yin murmushi yana tuno yadda suka rabu.
(Kuka take sosai ita adole bataso ya tafi yace Emily kinsan banason ganin hawayenki ko? Tace I can't help it, xaka tafi ka barni ba dole inyi kuka ba! yace don't worry xan dunga xuwa ganinki sai tayi murmushi tace promise? Yace i promised, tace to yaushe xaka fara masters degree dinka? Yace gaskiya sai next year saboda inason hutu wannan shekaran ta rugumeshi tace I'll miss you yasa hannayenshi ya xagaye kugunta dasu yace I'll miss u too sugar pie. Sai aka fara kiransu akan lokacin tafiyarsu yayi sannan ya saketa ya sumbace ta kadan a lebe sannan yace goodbye Emmy, ya juya yatafi itakuma tacigaba da kukanta .
      
                           ***

          Awannan shekaranne su Aneesah da Afrah suka gama secondary school da sakamako mai kyau alokacin, shekaran Aneesah 18 while Afrah is 17, sun kara girma da cika barinma Afrah, dirinta yakara futowa, fatarta takara haske ga sheki, kirjinta duk sun ciko ga kugunta ya kara fadi sai ka 'yar shekaru ashirin abun gwanin ban sha 'awa.
          Wataranar lahadi dukkansu suna xaune a falo har da Mukhtar sai Hajiya Amatu tace Aafii kina jina? Tace eh inajinki tace mexai hana kije kiyi ma Inna Larai hutu koda na saiti biyu ne da sauri ta dago ta kalleta tace Mummy kiyi mun rai banaso inje hutu wurin Inna Larai sai aneesah tace Mummy dan Allah kibarta tunda tace baxa tajeba ta sauko daga kan kujera ta nufeta sannan tafara lallashinta akan tadaina kuka daga bisani Hajiya Amatu tace dukkanku baku gane nufinaba kungadai haryau wannan matar bata taba tambayar lafiyar Aafii ba itadai nata kudine every month sai na aikamata da kudi sai kace tanayin wani aiki shiyasa nakeson Aafii taje let's pretend mundawo da itane kunga in two weeks time sai muje mu daukota batare da saninta ba Annesa ta gyada kai tace sai yanxu nagamsu Aafii nima na yarda kije aiba dade wa xakiyi acanba inma kina bukatar wani abune ga phone dinki sai ki kira Mummy ko ni ko yaya ko ya kikace? Tayi murmushi tace na amince xanje Mummy, tayi murmushi tace kokefa yanxu sai ki shirya jibi sai mu rakaki tace toh!
                            *  *  *

         Yau wanake gani agidannan Afrah! Kece haka? aiko sannunku da xuwa ga wuri nan ku xauna tanuna musu tabarma dake shimfide ajikin bango suka xauna ta kawo masu ruwa sukayi mata godiya amma basushaba, daga bisani bayan sun gama gaisawa sai Hajiya Amatu tace to yau Allah yasa na dawo maki 'yar dakika bani amanarta nagode Allah yasaka da alkhairi dan ko gaskiya na ji dadin riketa kusan shekara shadaya kenan ko! tace hakane kam gashi ta kara girma kamar ba itaba, kinsan ko sai da kuka tafi sannan nayi nadamar rashin kin tambayar inda gidan ku yake tace aidakin tambaya dansakon dake kawo maki kudi, tace kinsan kuma ikon Allah duk lokacin dayake xuwa bama haduwa saidai yabar ma yaran gidan amma ai yan xu komai ya wuce tunda na ganta cikin koshin lafiya axuciyar ta tace uhm! mutum angirma amma ba a san adaina karyaba amma Afili tace ayya ikon Allah kenan.
Haka sukagama surutansu suka tashi tafiya tadunga masu godiya sannan takira Afrah tace rakasu mana saikidawo, batare da tace komai ba tabisu har wajan dasukayi parking mota, Hajiya tace Aafii if u need anything just call any of us ok? Tagyada kai taci gaba "ki kare mutumcinki Afrah kar kisake kifuta talla" to Mummy nagode, kune xakuxo daukana ko indawo dakaina? "Ta girgixa kai tace karkije ko ina I will personally come and pick you up sannan kuma kudin danabaki in bai isaba ki kirani sai in aiko maki dashi tace xamasu isa wlh me xanyi dashi bayan bana bukatar komai, tace kidai rike in case of necessity tace to thank you sannan suka shiga Mukhtar ya tada motar suka tafi.
          Ita kuma ta koma gida tana shiga Inna Larai tace nawa suka baki kibani? Tace bata basu bani kosisi inbakiba tace toh wuce daga ciki ki ajiye kayanki ta dauka akwatinta tashiga dashi wani daki dake bangaren damanta, tsayawa tayi tana kare ma dakin kallo a xuciyarta tana tunanin yadda komai na dakin yake a yadda tasanshi. Daga waje Inna Larai tace kefa nake jira kixo kimun wanke-wanken nan tunda yanxu ke xaki dunga karuwa dani ai dolene kiyi aiki.
          Ta futo tace gani ina wanke wanken suke? Ta balla mata harara tace au tambayata kike? ki tsaya anan kar ki je kidibosu da kanki.
        Da yamma wajan karfe biyar da rabi tana tankade sai gawata yarinya 'yar kimanin shekara goma ta shigo kawai sai ta tsaya tana kallon Afrah, sai Afrah tace ya sunanki? Tace Mashida tace lah Mashida kece kika girma haka? Tayi dariya tace baki sanni bako? Ta gyada kai tace ni yayarkice kuma sunana Afrah kafin ta bata amsa Inna Larai tace kingama min tankaden ko kin xauna kina surutun banxa awajan? Ke kuma xaki wuce kibani wuri ko saina tashi? Ta xumburo baki ta shige daki. Data gama aikace-aikacen da aka sata sai ta shige daki ta sama Mashida tace ina su yaya Zulai da Ramatu da yaya Hannatu? Ta rage murya tace inna fada maki wani abu baxaki fada ma Inna ba? Tace eh baxan fada ba menene? Tace yaya Zulai tayi ciki tabi wani mutumi sungudu ta xaro ido tace sai ta tuna ranar da Inna Larai tace mata tabi namiji ta samo mata kudinta, da Allah ya taimaketane ta hadu da Alhaji Aslam dayake Allah ba azzalumin kowa bane sai ya saukar mata da aya akan 'yarta gashi tabi namijin da ita Inna Larai takeson ita Afrah tabi, ta girgixa kai tace Allah ya kyauta to ina sauran? Ta tabe bako tace nima bansaniba kullum sai sunfuta yawo.
          Da daddare bayan isha'i sai ga Ramatu da Hannatu sun shigo atare ta gaidasu suka ce kekuma daga ina? Tayi murmushi tace nice Afrah yaya Hannatu, duk da sunyi mamakin ganinta sai Ramatu tace to ni ina ruwana kin xo kina mana fi'ili kenan kin xauna agidan masu kudi, to aikin banxa tunda munsan amatsayin 'yar aiki kike tace kuyi hakuri na dauka baku ganeni bane, Hannatu tace kincire fuskar kine kinsa na akuya da baxa muganeki bane kome? Tayi shiru ta kyalesu, Ramatu tace kila dan taga tayi bilicinne shiyasa take ganin haka to bilicindin batayi maki kyau ba (see black belle abeg).
Ta tashi taje tabude akwatinta ta ciro phone dinta taga 4 missed calls biyu daga Mummy biyu daga Aneesah, batare da bata lokaci ba ta kirasu one bye one suka gaisa mummy harda kara jaddada mata cewa kartaje talla idan taje xata saba mata. Tashiga phone book dinta ta latsa wani number da akayi saving as big bros, tunda tasamu numban awurin Aneesah kodawasa bata taba kwatanta kiraba sai yau.
Shiko yana xaune akan gado yana magana da Emily ta skype yaji wayar shi na ruri kodaya duba yaga unknown number ne sai ya ajiye ya share yacigaba da abun dayakeyi tace don't u wanna pick the call yace its an unknown number, tace come on babe pick it up it might be someone important yayi tsaki ya dakko wayar xai danna kenan ya katse ya mayar da wayar ya ajiye can sai aka kara bugowa batare da bata lokaci ba ya daga fuska a daure yace hello daga other end din akace hello gud evening bros! jin muryar mai magana yasa yasaki fuska yace gud evening Aafii yakike? tace lafiya lau yace hope babu wani problem a wajan? "Everything is fine, dama na kirane in gaisheka yayi murmushi yace nagode Aafii sai anjima ko? Tace tom sai anjima yace take care sannan ya kasha. Hannatu tace uhm su iyayi manya na tabbata baki iya turancin nan ba kwamacala kikeyi (abeg see talk!na only u waka com?)
Tace yaya Ramatu a ina xan kwanta? Tace lallaima yarinyar nan ni xa ki tambaya? to kije ki kwana abayi tunda nabakina kikeson kiji, Hannatu tace da ba a kasa kike kwanaba! tace naga banga tabarma bane shiyasa natambaya, Mashida tace yanacan xaure nan ta tashi ta dakko duk ya kwankwance ya hargitse haka ta shimfida ta ciro wani xani daga akwatinta ta shimfida akai ta kara cirowani xanin ta kwanta ta lullubadashi.
          Da asussuba ta farka ta wanke bakinta ta dauro alwala tayi sallah sannan taxo tayi kokarin tashin sauran amma fafur sukaki tashi harda cewa inta damesu xasuyi mata duka haka ta kyalesu taje ta daura ruwa yayi xafi ta sauke ta kashe wutan sannan ta shiga bayi tayi wanka alokacin gari yadan soma wayewa sai ta latsa wayarta ta kira mummy suka gaisa ta kira Aneesah sannan takira big bros tajishi akashe...
         

LOVE WEB(tarkon so)Where stories live. Discover now