chapter 7

44 5 0
                                    

        💖💖💖💖💖💖💖💖💖

                  TARKON SO

This chapter belongs to u my three besties farda mustapha,Fatima Halliru & Habiba Bature.

         Komai ya daidaita yanxu Mukhtar ya fara xuwa makaranta domin yin masters dinshi sukuma su Aneesah sun shiga jami'a, tana karantar micro biology ita kuma afrah tana karantar mass communication, Hajiya Amatu kuma tace ita tagaji da xaman gida tunda kullum sai sun futa subarta ita kadai shine Alhaji Aslam ya bude mata wani katafaren boutique dan hakane ma kullum bata gida sai dai idan Alhaji Aslam yana gida.
              Wata rana Mukhtar yadawo makaranta a gajiye yana shigowa parlour sai ya fada kan 3 seater yanako kwantawa barci ya daukeshi sai ga Afrah ta shigo taganshi akwance tace yaya ina wuni shiru dataji yayi ne yasa ta gane cewa yayi barci sai tayi murmushi ta shiga dakinsu tayi wanka ta canxa kaya sai ta futo ta kara kai duban ta ga Mukhtar nan ta lura da bai cire takalman shiba, sai ta nufeshi ta durkusa ta cire mashi takalman ta samu wuri a gefe ta ajiye sannan taje wajan TV ta kunna takuma kunna dish tasa MBC Bollywood tana cikin kallonne taga ya gyara kwanciya, ya fuskanceta tsayawa tayi tana kallonshi tana yaba kyan halittarshi.
        Gashin idonshi yalayala ga gashi giranshi saura kiris su hade saboda cika, yanada siririn hancinshi mai tsawo, ga saje wanda ya bari abunka da farin mutum sai ya kara mashi kyau sai ya xamar mata kamar TV, ji tayi kamar ta matsa kusa da shi tashafa bakin gashinshi saboda shekin dayakeyi, ga plump pink lips that are so tempting. Caraf ta tashi ta shige dakinsu da dan gudu gudu can sai gata ta futo rike da waya, ahankali cikin sanda-sanda taje ta fara daukar shi photo sai data dauka kusan takwas sannan ta barshi ta koma ta xauna tacigaba da kallonshi yana barci.
          Daidai fara kiran sallar la'asar daidai farkawanshi kuma daidai lokaci tana kallonshi sai ta wayance tayi murmushi tace yanxu nake tunanin tashinka saboda lokacin sallah yayi, ahankali kamar baison magana yace dako kin raina kanki, yunwa nakeji menene a gidan? tace banyi girkiba amma mekakeso indafa maka? Yace dafamun indomie kawai kafun indawo masallaci tace to ya tashi ya kwashe tarkacen shi ya wuce daki.
          Yayi wanka ya dauro alwala sannan ya wuce masallaci yana dawowa ya tarar tana shirya mashi abincin akan dinning bai wuce ko ina ba sai dinning ta xuba mashi a plate sai taxuba mashi maltina a glass cup yace nagode kinkoyi sallah kuwa? Tace a'a yanxu xanje inyi yace to aje ayi idan kin idar kixo ki gyara mun daki kwana biyu ban fada makiba shiyasa baki san ki gyara bako? Tace ina mantawane yi hakuri yayi banxa da ita ta wuce taje tayi sallah sannan tawuce dakinshi ta gyara dakin data gama ta fara wanke toilet tana cikin wankewa ya shigo ya hau kan gado ya janyo system dinshi yakunna yayi connecting da skype yana yi sai ga kira daga Emily yayi murmushi just at the right moment yayi receiving yace holla ma che'rie,¿co'mo est'as? Tayi murmushi tace lafiya just missing you yace i missed u too, amma ya xanyi tunda yanxu ina karatune but don't worry idan mun samu hutu xanxo tace dagaske! Yaushe kenan? yace uhm...1 & half think tayi ihu tace really? Yayi dariya yace u'r such a baby tayi dariya I love u I can't wait for this day yace I love u too Emmy haka sukayi tafira wani sa'in suyi da Spanish wani sa'in suyi turanci, duk Afrah tana jinsu axuciyarta tace kuji wanda yace bayason surutu (na weti concern u for there?), tagama wanke bayin tayi komai har ta tafi bai gama magana da Emily ba.
          Tun daga ranar ta tsura xama a parlour din gidan ta dawo makaranta ta ganshi yana barci idan kuma bata Ganshi a daki ba sai tabishi daki da sunanta ta xo gyara mashi daki aiko rannan afalo yana kwance yana daddanna waya sai ya ajiye a saman kirjinshi ya kulle ido adaidai lokaci kuma ta futo daga daki sai ta ganshi tayi murmushi tayi sadaf sadaf taje ta tsaya a bayan kujeran tana kallon shi, shi kuma he felt uneasy kamar ana kallon shi kawai sai ya bude ido karaf idonshi ya fada cikin nata ta xaro ido tajuya xata gudu yace stop right there, cak ta tsaya gabanta na faduwa yace xonan jiki na kyarma ta taho a hankali ta iso gabanshi ya kalleta up & down"ina xaki?" Tace uhm dama xanje dakine yace shine xaki tafi da gudu ko? Bana cemaki banason rawar kai ba? Tace I'm sorry I thought you were going to penalize me yace meyasa xanyi penalising dinki, 0h! Saboda na kamaki kina yin abun da kika kware akai ko? Ta dukar dakai yace fada mun dalilin dayasa kike kallona shin ko wani abune a fuskata? Ta girgixa kai yace to shikenan tunda baki da dalilin da xaisa ki dunga kallo na to kar insake ganin kina kallona kinjiko? Tace eh yace be careful with me banason kallo kinjiniko? Ta kara gyada kai yace bace mun! Sumisumi take tafiya kamar munafuka har tashige dakinsu axuciyar ta tace wasa wasa yaya masifaffene fa (sai kyau kikasani?)

                        ***

          Abun mamaki shine  kwata kwata yanxu idan bataga Mukhtar a yini guda ba sai ta kasa walwala har sai ta sa shi a ido, yauma kamar kowace ranar lahadi dukkansu suna xaune a parlo including Alhaji Aslam da Mukhtar sai Hajiya Amatu tace 'yan matannan nawa kunkara girma fa sosai na kusa samun sirikai kenan? Aneesah tayi dariya tace Mummy sirikai ba yanxuba sai mungama karatu ko Aafii? Afrah tayi dariya tace gaskiya kika fadi, Hajiya Amatu tace to baku isa ba, badai anan gidan ba ni daso samune in hada ku da 'yan samarin dangi,to bara kuji ko 300 level baxa ku karasaba xan aurar daku inkunga dama tun yanxu kusamo tsayayye dan ba wacce xatace mun bata da saurayi musamman ke Aneesah dakike xaune a hostel inkuka ki ga babankunan, dashi xamu samo muku maxaje kuma dole ku xauna dasu ko kuna so ko bakwaso, Aneesah tace daddy kaji Mummy ko yace ai gaskiya ta fada, Afrah tace Mummy nibana kula kowafa saboda banaso inyi wasa da karatuna tace shikenan mahadaki dawani acikin dangi ta xumburo baki ta kwanta akasa tana kallon Mukhtar da hankalinshi ma baya kansu yanata chatting da I have no idea.
          One Sunday morning,  da misalin karfe goma Afrah ta kwankwasa kofar Mukhtar taji ba a amsaba saita dauka bayananne kawai saita bude kofan ta shiga batare da lura da mutum akan gadoba ta wuce toilet datagama wankewa sai ta futo nan idonta ya fada kan Mukhtar dake sharan barci axuciyar ta tace ashe yananan bai futaba sai ta fara gyara dakin tayi shara sai ya rage mopping da gyaran gado gashi kuma oga bai tashiba saita samu kujera na mirror ta xauna ta xuba mashi ido itafa gayen nan ba karamin birgeta yake yiba musamman gashin idonshi dana kai sai ta fara imaginating yadda xataji idan ta running hands dinta through his hair. Shiko ashe tun farko yaji shigowanta amma yaki bude ido.
          Ji yayi kamar ana kallonshi sai ya fara bude idanunshi ahankali sai yaga Afrah tana kallonshi tana murmushi sai ya bude gabadaya yace wa kike kallo? Cikin fargaba ta mike ta fara gudu har tayi taku uku shi kuma cikin xafin nama ya tashi ya cafkota nan danan jikinta ya fara kyarma sai tace dan Allah yaya kayi hakuri baxan kara ba yace shut up taja baki tayi gum! Yace xauna akan gado jikinta na bari yace if u tell me the truth, I will let you go understand? Ta gyada kai yace me yasa kike son kallona? Ta dago kai ta kalleshi suna hada ido ta yi sauri ta maida kanta kasa sannan tace babu komai yaya, I have no idea why I like watching u, its just...I don't know! Ya nodding kanshi yace tunda baxaki fadamun ba shikenan, ya nufeta fuskarshi a daure sai tayi sauri ta tashi xata gudu ya fincikota ya jefa ta kan gado idonta ya ciko da kwalla yasa hannayenshi biyu ya danne mata hannayenta biyu ta side by side takalle shi tace please alokacin har ta soma futar da hawaye, a hankali ya fara getting closer to her face tafara mustsu-mutsun fusge hannunta amma ta kasa sai da labbanshi suka kusa gogan nata sannan ya karkata ya kai kunnenta yace idan na kara kamaki kina kallona sai kinyi dana sani because abun da xanmaki  xaisa ko sha'awan kallona baxakiyiba kina jina? (u don spoil) ta gyada kai sai ya saketa yace get out of here da sauri ta tashi xata gudu yarikota yace kar kisake kiyi gudu, a hankali take tafiya har ta futa tana xuwa daki ta fada kan gado tare da kuka, ita kanta ta rasa dalilin dakesata kuka, haka taci kukanta harta gode ma Allah koda Aneesah ta shigo taga idanunta akumbure sai tace me yasameki kike kuka tace ba kuka nakeyi ba, mistakenly na tsokale idona, sai tace duka idon kika tsokale alokaci daya? In xaki fada min ki fadamun bansan wani kwane kwane, sai tayi shiru na 'yan dakiku sannan tace ba yaya bane yasani kuka ba tace meya maki? nan ta fada mata duk abundaya faru aranar sai tayi murmushi tace to ke meyasa kike son kallonshi bayan ya fada maki bayaso tagirgixa kai tace nima Allah bansani ba kawai dai ina samun kainane cikin nishadi idan ina kallonshi tace lallai kam!
          Da safe ma a makaranta zainab dikkoh kawarta tace yaya kawalli yau yana ganki looking so dull meya faru? Hmm! wlh nima bansan meke damuna ba kwanannan tace kamar yaya? Tace there is this feeling I get when ever I see my big brother kuma inna kalleshi bana iya kauda kaina, yasha mun fada akan indiana kallonshi amma na kasa ban San yadda xanyi ba wallahi, zainab dikkoh tayi dariya tace I can't believe bakisan abunda ke damunki ba wanda ko dan 10yrs ne yasan abunda ke damunki takalleta tace dan Allah fadamun tace kin fada TARKON SON yayankine tayi dariya tace u can't b serious! Ya xa ayi infada sonshi alhalin ko maganar kirki bata hadamu kuma fa brother nane how is that possible tace ai shi SO ba dole sai ana magana da juna ba, sai kiga mutum a hanya wanda baki taba ganinshi ba amma sai kiji sonshi kuma ma aike da brother dinki are not related by blood so kinga wannan ma fact ne ta girgixa kai tace I don't believe you tace to shikenan with time xaki game gaskiya tace "whatever" (how rude).

LOVE WEB(tarkon so)Where stories live. Discover now