chapter 8

39 5 0
                                    

          💖💖💖💖💖💖💖💖💖

              ***tarkon so***

          Alokacin daya rage kwana shida su Mukhtar suka tafi hutu, da daddare ya samu Alhaji Aslam a xaune tare da matar shi suna fira ita kuma Aafii ta futo daga daki xataje kitchen taji yana cewa dad dan Allah inaso kayi mun ixinin tafiya Spain, cak ta tsaya abakin kofar kitchen tana sauraron ansar da Alhaji Aslam xai bashi sai tasamu kanta me addu'a aranta akan kar Allah yasa ya amince mashi zuwa Spain din, alh.yace spain kuma? mexakayi a can? Yadan sosa keya yace I just want to go and visit my...uhm friend there kafin mudawo hutu yace shi friend dinnaka a can yake xaune ko karatu yakeyi? Ya dukar da kanshi yace macece dad kuma acan take xaune kuma sunanta Emily Jayden, ya maimaita sunan Emily?!! Ya danyi shiru sai kuma yacigaba "baxan hanaka xuwa ba, ko ban fada ba nasan kai ba yarobane kuma kasan abunda ya kamata koba haka ba? Yace hakane dad, yace to shikenan idan kashirya kayi mun magana yace dad next week xan tafi yace to shikenan xamu hadu gobe cikin murna yace nagode dad, Allah ya saka da alkhairi yace amin sannan ya tashi ya tafi, Hajiya Amatu ta kalla Alhaji tace bansan meyasa yakeson xuwa wajan Emily dinnan ba duka duka yaushe yadawo dayakeson komawa? Yayi murmushi yace kika Sani ko xamu samu karin musulincine! tace to Allah yasa ni halin yaron na birgeni wallahi tace ai duk halinku iri daya yace ni!! Ina xan iya da miskilancinshi, tayi dariya...
          Da kyar ta iya daga kafanta ta koma daki tana xuwa ta fada kan gado tayi shiru tana tunani, Aneesah tace ya haka Aafii ina abunda kikaje kaowa? Tayi shiru bata tanka mataba sai ta tabota, firgigit tayi tace na'am tace tunanin me kikeyi haka ? Tace Aneesa yaya xai koma Spain tace dagaske? Yaushe xai tafi? Tace by next week, tace Allah sarki yanaso yaje yaga Emily kenan, Afrah tace ni wallahi banaso ya tafi tace to meye aciki? Kwata kwata fa 2 weeks xaiyi acan ta xaro ido tace har sati biyu fa kikace, ai yayi yawa dama ya fasa xuwa tayi murmushi tace yarinya babu mai hanashi xuwa Spain indai har daddy ya amince ta kifa kanta akan pillow tace ni yanxu ya xanyi? Banganshi na kwana daya ba nashiga wani hali balle har na sati biyu! Aneesah tace me kikace? Tace badake nake ba...
           Ana sauran kwana biyu ya tafi alokacin sunyi hutu ta kwankwasa kofar dakinshi tare da sallama ya amsa yayi mata ixinin shiga, kwance yake yana karanta wani littafi tace yaya wurinka naxo yace ina sauraronki ta durkusa tasa gwiwowinta a kasa, ta bude baki xatayi magana kenan wayar shi yasoma ruri yadauka yace hello Sam (samad yake kira da Sam) (shiru) OK to ganinan xuwa, ya katse wayar ya tashi sai ya ganta yace oh I'm sorry Aafii na manta mekike cewa? Cikin karamin murya tace dan Allah kar katafi Spain dinnan? Ya tsura mata ido as if she's grown two heads yace yanxu ba lokacin wasa bane I'm busy tace Allah dagaske nake banaso katafi ya sauke numfashi yace fada min meyasa bakyaso inje? Idanunta cike da kwalla tace haka kawai naji banaso katafi yayi tsaki yace shirme kenan inkinga banje wajan Emmy ba to dad ko mum ne suka hanani ya mike ya dauka makullin motarshi yace ki kullo mun kofan inxa ki fita.
Har ya kai kofa ta ruko mashi wando ta kasa, fuska a daure what d hell is wrong with u? Sakeni mana tace yaya kanason Emily ne? Ya yamutsa fuska yace and who are you to ask me such a question? Hawaye suka soma xarya a fuskanta "yaya please kana sontane? Ya fusge kafanshi yace eh inasontane sai me? ya futa ya barta anan tanata rusa kuka (abeg wetin be dat?).
Shiko tunda ya fita yake ta tunanin abundaya sami Afrah take behaving haka ,tanaso tahanashi xuwa ganin abun kaunarshi abunda yake impossible but meye dalilinta?..…
How am I suppose to know that? Sai dai kila Ku kunsani readers.

LOVE WEB(tarkon so)Where stories live. Discover now