'''💞HEARTBEAT💞'''
*JIDDAH*
Nimcyluv'''
'''Wattpad@nimcyluv'''
CHAPTER 10The begining of beging
IMRAN MAI TANGARAN shine asalin sunan mahaifin IRFAN Allah babban lawyer ne a nan garin kano ubangiji Allah yay masa tarin arziki mai abarka wanda yake taimakon marasa galihu,kasan cewar baiyi aure da huri ba sai yana da shekara 30 yay aure lokacin yake Sudan akan wani bincike sabida zaman ƙarar da suke,a nan ya haɗu da HADIZA kyakkyawar yarinyace ajin farko shekararta 25,cikin sa'a ya samu soyayyarta yana komawa gida ya faɗa iyayensa a satin su kaje Sudan neman aurenta inda suka tsaida magana wata biyu masu zuwa.A cikin watan IMRAN ya samu nasara azaman court na ƙarshe da akai,kwanci tashi lokacin biki yay akasha biki ranar lahadi aka kai amarya ɗakinta a nan jahar Kano.
A watan da aka kaita a watan ta samu ciki sunyi murna sosai,wata tara ta haifi kyakkyawar ƴarta mai kama da ita sak,ranar suna tazu aka raɗa mata suna AMRAH.
Sosai suke son yarinyar akwaita da hakuri kamar mahaifiyarta,tana da shekara 2 HADIZA ta ƙara samun ciki tasha wahala sosai a laulayin cikin haka Amrah zata sata gaba da cewa "Mommy ciwo bafiii anuu"shikam IMRAN wanda yanzu Amrah take kira da Daddy cewa yay kawai a zubar da cikin idan babu dama,murmushi kawai take wani lokacin kuma tace"Allah yay mana baiwa shine kakeson mu nuna butulci mutane nawa keso Allah bai basu ba"idan ta faɗi hakan sai yaji daɗi yasa hannu ya rungomuta ya shiga yi mata addu'a a kunne.Wata 10 cif cikin yay jikinta kafinta haife tasha wahala sosai kwananta uku tana labour kafin ta samu nasarar haifar ɗa namiji kyakkyawa amma baƙine shi irin sosai ɗinnan😂.
Satina zagayowa ya amsa sunansa na IRFAN,lokacin Amrah na schl nusery section.
Lokacin da Amrah take shekara 5 shi kuma lokacin shekararsa 3 tsiransu shekara 2,sosai suka maida hankali kan karatu yayinda Irfan ya ɗauko duk wani hali na mahaifinsa taurinkai miskilanci ga zuciya,amma kuma yana da kyauta da kuma tausayi hakan yasa Daddy ya fifitashi da Amrah sosai yake banbanta soyayyarsu a fili.tun a makarantar primary Irfan ya haɗu da Aryan sosai suke son junansu idn ka gansu zaka ɗauka iyaye ɗayane suka kawosu duniya,dukkan Abinda Aryan ya samu sai yace shi Anty Amrah zai bawa haka zata karɓa tana dariya ko kuma tai hug ɗinsa,iyayensu kuwa zumunci suke kasancewar suma a anguwar suke.
Irfan ya tasu da gayu sam baison hayaniya jikinsa tsaf bayasa kaya idan ba manya bane,lokacin daya gama secondry yace shi baya son karatu a gida kuma shi Ball ya keso,haka aka gama komai na tafiyarsa ana gamawa ya huce PAKISTAN tofa tunda yaje rabi makaranta rabi wajan ball daga ƙarshema gaba ɗaya makarantar ball ɗin ya koma.
Abu kamar wasa tun yana ball da ƙanan mutane yana samun nasara sosai sai aka aka huce masa gaba ya shiga CLUB MADRID inda yake ɗauƙan IRFAN 5,sosai yake buga wasa harya zama abin kwatance,Club da yawa sun kawo masa hari yace baiso idan ba MADRID.
Wata rana mommy da Daddy suna zaune suna kallo cikin sa'a abu ya sauya canel yace ball ya keson kalla,ba'afi 5min da farawa ba ya hango tillan ɗansa dariya sosai yay har yana riƙe ciki,kallon mommy yay yace"madam come and see"wajan tazu ta zauna bisa cinyarsa da hannu ya nuna mata Irfan murmushi tayi tace.
"i"m soo proud of u my son Allah yay maka jagora"
Daddy ne yay murnushi tare da faɗin"ya ɗauka za'a hanashi abinda yake ambition nasa ne,ninaji daɗi hakan".
Ihu Daddy yay tare da taka rawa sabida ko 10min ba'a rufa da farawa ba Irfan yay nasarar cilla ball cin raga har sau 2.
Tun yana da shekara 19 yabar ƙasa yanzu shekarunsa wajan 25 aka ƙalla shekarunsa 6 a can,yayinda da Amrah take da shekara 21 akayi mata aure lokacin shekarunsa 2 data fiya,haka akai aurenta tana ta kuka babu Irfan babu Aryan domin shima yaje waje karatu.
YOU ARE READING
JIDDA
Romanceif you are looking for story that touch your heart and soul this is it