RAPPING 15

735 71 13
                                    

'''💞HEARTBEAT💞'''
         *JIDDAH*

'''MALLAKIN😘
ANTY NI'EEMERH
    Nimcyluv'''

CHAPTER 15
''''''RAPPING'''

'''Wattpad@nimcyluv'''

      *🥰2GIFT👇🏻*
'''Accept  ur self  the way you are  be  kind  ur self not be a selfish 😘'''

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

    
               15

Dukkan jikinsa rawa yake hankalinsa ba ƙaramin tashi yay ba domin bai taɓa tunanin zata aikata hakan ba,ashe daman da take cewa zata amsa sunanta na karuwa da gaske take ya ilahi wannan wacce irin yarince da bata tausayin kansa ji yay inama bai santa ba inama bata shigo rayuwarsa ba,dukkan ƙoƙarin da zaiyi danya fahimci waye namijin amma ya kasa fahimta ya ringa daya sunkuyar da kansa yana aikata abinda ya haramta gareshi,wayarsa ce ta fara ƙara alamar ankira tsaki yaja tare da ɗaukan wayar ya manna a kunansa yay shuru tare da sauraran abinda za'ace masa.

  Daga ɓangaran wanda ya kira ya kwashe da dariya saida yay mai isarsa sannan ya haɗe fusksa tamkar yana gabansa yace"malam Irfan zance ko Alhj Irfan ko kuma mashayi kuma manemi mata zan kiraka dashi,forget duk ba wannan ba inason nace maka a yau zan shiga gonar da kaima ka shigeta idan harka isa ɗan halak kuma zaka iya dakatar dani akan abinda nayi niyya to bisimillah kafin nan da zuwa 8 na dare zamu gani tsakanin ni dakai,ka sani dukkan abinda na aikata a gareta kaine sila domin na lura hankalinta baya wajena yana gareka kuma banyi tunanin hakan the choice is yours mutuncinta ko kuma ta zama matebed ɗita bye"

Yana faɗin hakan ya kashe kiran,sumar tsaye Irfan yay yayinda dukkan wani tunani nasa ya tsaya ta ina zai fara ina take wannan shine abinda yak mas yawo aka,agogon hannu ya duba wanda yake ɗaure jikin tsintsiyar hannunsa 6:30 shine abinda ya ganni,zirga zirga ya fara tsakiyar parlor amma gaba ɗaya ya rasa mafita,zama yay kan sofa tare da zubawa A.c ɗakin ido sosai yake sauraran bugun zuciyarta wacce ke sauri,tunaninsa gaba ɗaya tsayawa  sai ya zama kamar butun butumi ido kawai yake rarrabawa tare da ƙiftasu,sannu a hankali idon keyi masa nauyi tare da zafi nan bacci mai nauyi yay gaba dashi.
ƊAN LADI NA SIDI

  Sakin baki Amrah tayi tare da bin wayar da kallo domin bai taɓa yi mata hakan ba,kallo Aryan tayi wanda ya ɗauki Huda ya ɗura saman cinyarsa yana faman yi mata snap vedio,yayinda Taslim kuma take ɗaga gefen nasa tana sharara bacci tsayawa yay da snap ɗin ya zuba Amrah ido sosai ya gano damuwar da take ɓuyewa,Huda ya ajjiye tare tamƙa mata wayar a hannunta ta shiga game,wajan Amrah ya ƙara daf da iya har suna iya jin numfashin junansu,tsira bata ido yay kafin yasa hannu da niyar riƙo hannunta sai kuma ya fasa cikin sanyin murya yace "meye?"ɗauke kai tayi daga kallonsa cikin raunin murya tace"akwai damuwa wajan Irfan muryasa ta fallasa abinda ke cikin zuciyar blood ya kashe min waya ba tare da yaji abinda zance masa pls Aryan jeka duba lafiyarsa kaga Abban twinst na jirana domin rakiya zuwa airport"ta faɗa cikin tashin hankali gaba ɗaya jiyaye babu daɗi ganin ta shiga cikin halin tashin hankali inama yana da ikon da zai rarrasheta saman ƙirjinsa inama yana da ikon da zai ɗauke damuwar dake zuciyarta ta hanyar nuna mata zallar soyayya da kuma ƙauna amma ina babu dole zai hkr da ita domin ya fahimci tayi masa nisa tunda har rabo ya shiga tsakaninta da mijinta babban raboma kowa domin haihuwar twinst a wannan lokaci sai ɗan baiwa ga kuma wani cikin manne a jikinta "take it easy"shine abinda bakinsa kawai ya iya faɗa juyawa yay tare da ɗaukan Huda ya saka a shoulders suka fice daga gidan.

  Ajjiyar zuciya ta sauke meyasa take rasa kuzari da kuma sukuni a dukkan sanda numfashinsu ya haɗe waje guda,meyasa kalaman bakinta keyin hijira ya ƙaurace mata,sautari tana yawan yiwa kanta wannan tambayar amma babu amsa,wajan Taslim ta ƙarasa tare da ɗaukanta suka isa cikin bedroom ɗin nasu,a tsaye ta sameshi cikin kyakyawar shigarsa mai kyau,murmushi yay tare da ƙarasawa wajanta ya amshi Taslim dake bacci ya manna mata peak saman goshi cikin sanyin murya yace"my luv i gonna missing u dear"ya faɗa yana shafa gashin kanta,wajan Amrah ya nufa wacce take tsaye tana kallonsa gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi hakanan ta kejin fargaba na shigarta,jikinsa ta faɗa tare da fashewa da kuka bubbuga bayanta ya shigayi tare shafa sumar kanta a hankali ya furta"beb what happen?"girgiza kanta tayi ba tare data tankashi ba,hannu yasa ya shiga goge mata hawayen fuskarta,murmushi da baya ƙarewa a fuskarsa yay kafin yay saurin haɗe bakinsu ya shiga bata lafiyayyan kiss mai tsayawa a rai,sosai ya rikita mata lissafi harta fara inda take,bakinsa ya zare daga nata Taslim ya ɗauka sannan ya riƙe hannun matar tasa suka nufi waje domin shiga mota ardy kayansa yana ciki daman.

  Compund na gidan suka ƙarasu suna kyalkyala dariga kwanin sha'awa,rumfar ajjiye motoci suka nufa tare da shiga wata lafiyayyiyar mota,side ɗin drever ya shiga yayinda da Amra ta koma ɗaya side ɗin,motar yaywa key yaja a hankali Taslim na jikinsa tana  bacci,daman baiyi tunanin tambayar Huda ba yasan da wuya ace bata wajan uncle Aryan,a haka yaja motar suka fice daga gidan.

FARAWA

Bacci yake wanda kana ganinsa kasan wanda yake baccinsa ba daɗinsa ya keji ba,dukan kafaɗarsa da ake ita ta dawo dashi cikin haiyyacinsa,a hankali ya shiga ware manyan idonsa wanda zuwa yanzu suka koma ƙanana sabida zafin da suke masa,gaba waresu yay akan Aryan wanda yake tsaye kansa hannunsa duk ruwa da alama alwala yay amma alwalar mece haka,jajayen laɓɓansa ya cije tare da dafe forehead ɗinsa wanda ya keji kamar zai tarwatse,Huda ce cikin kwarancinta tace"uncle Ancii sallah"kallonta kawai yay ya ɗauke kansa,gyaran murya yay tare da faɗin "oyya wake up buddy we alrdy late za'a shiga sallah u sleep more ai"cikin sauri Irfan ya tashi tare duba lokaci yaga 7:44 sallar issha za'ai kenan kansan yaɗan buga tare da faɗin"damn sleepy"Aryan ya kalla yace "there's a big problm 4eyes missed jeka masallacin zanyi a gida"yana faɗin hakan ya juya zuwa kan steps ɗin benen Huda kowa zama tayi tana shan ice cream ɗin da Arayan ya bata dan haka bata damu da zaman kaɗaicin ba.

  A gurguje yay wanka tare da ɗaura al'wala ko cream mai saka jikinsa ba,sai turare daya fesa akan black naked skin ɗinsa,wata dakakkiyar shadda ya saka Amy colour sosai ta amshi jikinsa kasancewarsa mai baƙar fata sallah ya gabatar dayin addu'ar neman sa'a kansa ya gyara tare da ɗaukan farin bluetooth ya manna cikin kunansa wayarsa ya ɗauka mai kirar iphone 11 pro tare da ɗaukan key yay waje ya fara sauka daga ƙan steps ɗin.

Tsaye yaga Aryan ya gaba shirinsa cikin baƙin yadi mai kyau ya amshi farar fatar jikinsa,yayinda yaywa Huda wanka ya sauya mata kayan jikinta cewarsa dole uba ya kula da ƴarsa😅rungometa yay ajikinsa yayinda take kwarar baccinta sai munshari take dariya yay yace"wlh wajan ubanki kika ɗauko wannan abun bebna ba tayi wannan"ana haka yaga Irfan ya tsaya gabansa cikin sauri yace"muje"tafiya suka fara suna tafe yana labartawa Aryan abinda ya faru har suka isa motar shiga sukayi gaba ɗaya yayinda suka saka Huda a side ɗin baya.

  Dukkan inda suke tunanin marasa gasky na zama saida sukaje amma babu wani news akan Jidda,gaba ɗayansu hankalinsu ya tashi musamman Irfan da yaga 8:5 wayarsa ya ɗauka tare da ƙara shiga vedio da aka turo masa kallon vedio yay nan ya fahimci ɗakin da suke ciki ba nrml ɗaki bane na Hotel ne,a hassale ya juya kan motarsa ya harbata akan Titin Nasarawa kowa yaga gudun da yake sai ya matsa ya bashi waje.

  Cikin ƙaramin lokaci suka isa TAHIR GUEST PLACE kashe motar yay tare da fita da gudu,babu inda ya nufa sai wajan ma'aikatan Hotel nan ya labarta masu abinda ya faru C.C.TV camera suka shiga nan sukayi sa'ar ganin mota tayi parking sannan mutum ɗaya leƙo ya duba yaga babu kowa sannan ɗaya ya ɗaukota ya fara hawa da ita saman bene,har lokacin daya tsaya gaban wani ɗaki,baki Irfan ya saki ganin wanda ya fitu ɗaukan Jidda ba Sameer bane to waye?ganin babu lokaci yasa suka dugun zuma gaba dayansu suka nufi section ɗin da suke.

  Tsayawa sukai gaban ɗakin ana jiran buɗe ƙofar,runtsa idonsa Irfan yay sabida nishi da kuma kurnanin mutum haɗe da sumbatu da yake jiyowa ta cikin ɗakin.

Da master key sukai using ana buɗewa Irfan ya faɗa ciki"innalillahi wa'inna ilahir raji'un"shine abinda ya fitu daga bakin Irfan zubewa yay a ƙasa wanwar.

  *Team Jidda sai haƙuri ina baku haƙuri😥👏🏻bakai kake tsara labari ba,labarin shike tsaraka indai kana son kayi aceving abinda kake dai² so sad guys*

JIDDAWhere stories live. Discover now