LOST

652 69 12
                                    

'''💞HEARTBEAT💞'''
           *JIDDAH*

'''NIMCYLUV'''

CHAPTER 30-31
       LOST

Wattpad@nimcyluv

           Chapter

   Bai daɗe ba ya isa asibitin Aminu kano yay hanyar emagency cikin sauri nurses suka ɗurata gadon marasa lpa,ciki suka ƙarasa da ita ɗakin marasa lpa tare da juna mata Oxygen  sbd numfashinta daya tsaya taimakon gaggawa suka shiga yi mata amma gaba ɗaya abin na neman basu matsala hakan baisa sun karaya ba suka ci gaba da dubata.
   Irfan banda safa da marwa babu abinda yake a ƙofar room ɗin zuface kawai take yanku masa duk da A.C'n wajan amma kamar ana irin zafinan haka ya dinga goge fuska,idonsa ya kaɗa yay jaa jijiyoyin kansa sunyi raɗa² wayarsa ce ta shiga ƙara banza yay da ita bai ɗaga ba,ƙaran taci gaba dayi tsaki yaja ya zura hannunsa cikin rigarsa ya ɗauki wayar ganin sunan Boddy na yawo saman fuskar wayarsa yasa yay picking tare da mannata a kunnasa ba tare da yay mgna ba,daga can ɓangaren Aryan yace"kana ina" shuru yay masa ba tare daya tanka ba tsaki Aryan yaja daga cikin wayar kafin yace"Jidda fa Amrah tace dalilinta kabar gida ko" uhm..shine amsar da Irfan ya bashi kafin ya ware laɓɓansa yace "Aminu kano hospital emagency"yana faɗin hakan ya katse kiran tare da zama kan ɗaya daga cikin kujerun da suke jere a harabar wajan.

    Ya shafe 2hours zaune a wajan amma still drs ɗin da suka shiga da ita basu fito ba,hankalinsa ba ƙaramin tashi yay ba zuciyarsa ta shiga bugawa da ƙarfin jin an taɓashi ne ya sashi ɗago dakai yay yana kallon mai taɓashin cikin sauri ya miƙe tsaye ganin Mom ɗinsa tana sakar masa murmushi gefe guda kuma Aryan ne da Amrah tsaye sun zuba masa ido,jikin Mom ya faɗa tare da sakin Ajjiyar zuciya bayansa ta shiga bubbugawa tare da faɗin"don't worry son everyting will be ok"kaiya jinjina mata tare da zare jikinsa daga nata dai² lokacin likitocin da suke kula da ita suna zare gomi kallonsa sukai kafin ɗaya daga cikinsu yace"follow me"cikin sauri Irfan yabi bayansa shida Aryan zama dr ɗin yay kan kujera tare da zare farin glass ɗin dake manne saman fuskarsa numfashi yaja kafin yace"bansan me zance maka ba sir Irfan amma kayi haƙuri da wannan yarinyar dan abune mai wahala tayi rai zuciyarta ta buga wadda ya haddasa mata fituwar jini da hancinta kuma ko amai tayi za'a iya ganin jinin dalilin daya saka numfashinta ya ɗauke amma bansan ikon Allah ba damu da ita mara lafiyar ba'asan gawar fari ba amma dai munyi duk ƙoƙarinmu munbarwa Allah nasa ikon"table ɗin dake gaban dr irfan ya buga tare da shaƙar wuyansa yace"ƙarya kake wlh noting happen to my jerry"yana faɗin hakan ya hanka ɗasa tare da ficewa da sauri yabar office ɗin,numfashi dr ya shiga fitarwa tare da shafa wuyansa kallonsa  Aryan yay tare da faɗin"i'm sorry he can't contral his self yana mata matsanacin so dat why kayi hkr pls"jinjjina kai yay tare da furta"babu damuwa mun saba fiskantar irin wannan ai Allah ya bata lafiya"gdy Aryan yay masa tare da barin Office.

  Irfan na fita ya nufi room ɗin da aka kwantar da ita,a kwance take flat  hancinta ɗauke da Oxygen tana shaƙar iska daga cikinsa yayinda hannunta yake ɗauke da drip wanda aka sakawa injection,ƙirjinta sai sama da ƙasa yake an maƙala mata wani abu a ɗanya tsanta ƙarasawa wajan gadon yana zuwa yaja kujera ya zauna tare kama hannunta,cike da mamaki yaji ta damƙe hannunsa ɗaga kai yay ya kalleta sosai fuskarta ta ƙara haske yayinda idonta yake a rufe sai zubar da hawaye yake hannu yasa ya shiga goge mata hawayen dake zuba tare da ɗura kansa bisa kafaɗarta"pls wake up jerry i hate dat sleepyn beby gril dan Allah tashi"ya faɗa idonsa na zubar da hawaye jin ana shafa sumar kansane yasa ya ɗago da kansa mamaki ganin ta buɗe ido yay kanta ya shafa yace"Allahmdllah"hannu tasa ta zabe Oxygen ɗin bakinta da hancinta bakin na rawa tace"Ir...fan..it's my tym to go zuciyata zuciyo take i'm away"riƙeta yay tare da ƙoƙarin mayar mata da Oxygen ɗin,hannunta tasa ta ture hannunsa wuyan rigarsa ta riƙe tare da jawosa sosai numfashinta ne ya shiga ɗaukewa tare da dawowa matsesa ta ƙarayi sabida azabar data keji laɓɓanta ta shiga warewa kafin ta samu damar faɗin"Na..jeeb..bata gama faɗin abinda zata faɗa ma numfashinta ya shiga sharking ta fara tari cikin sauri ya mayar mata da Oxygen ɗin hannu yasa ya share hawayen fuskasa juyawa yay zai tafi yaji ta riƙe hannunsa juyowa yay wata farar papper ta ɗago masa tare da rubutu a jiki da manyan baƙi I NEED YOU IN MY LIFE FOREVER AND EVER ,saurin sakin hannunta yay tare da fita daga room ɗin da sauri yana fita yaci ƙaro da Aryan jikinsa ya faɗa tare da sakin kuka,bayansa ya shiga bubbugawa sosai kukan abokin nasa ke taɓa masa zuciya,zare jikinsa yay tare nufar compound ɗin asibitin da gudu yana zuwa yasa key ya buɗe motarsa tare da faɗawa cikin da gudu yay  wajan get cikin sauri mai getman ya buɗe masa get ɗin kamar zai tashi sama haka yabar harabar asibitin.


JIDDAWhere stories live. Discover now