POLICE

579 60 7
                                    

'''💞HEARTBEAT💞'''
             *JIDDAH*

NIMCYLUV

'''CHAPTER 36-37
      POLICE'''

'''Wattpad@nimcyluv'''

              Chapter

         Waro ido Jiddah da Amrah sokai domin abin ya fara basu mamaki,kallon Jiddah Amrah tayi tare da faɗin"Zonan Jiddah yau ina kallon ikon Allah"idon Jiddah fal hawaye sai ƙifƙitasu take zuciyarta cike da rauni ta ƙarasu bed ɗin da yake zaune ya cure waje guda ko mutsi ba yayi,zama tayi kusansa tare da kama hannunsa lokacin hawayen idonta ya gama wake mata fuska,lumshe  manyan narkakkun idonsa yay tare da taune red lips ɗin masu ɗan tudu gaba ɗaya ya jiƙe da sliver ɗinsa,yana jin yadda ɗumin hannunta amma baisan wace itama bai san tayaya zai fara magana da ita ba,gaba ɗaya kallonsu yake kamar ba mutane ba amma su kaɗai ya sani cikin rayuwarsa dasu ya fara tozali bashi da wanda ya fisu,ƙoƙarin zare hannunta tayi daga cikin nasa yay saurin damƙe hannunta ba tare daya buɗe idonsa ba,kafin suyi magana dr ya shigo cikin saurin ya ƙarasu wajan Irfan ɗin, Irfan yana ganin zaika mutsa yay saurin miƙewa tsaye tare nufar wajan da Jiddah take yana ya maƙale jikinta daga baya ya shiga girgiza kanta,kuka Amrah ta fara tare da faɗin"wai dr what is going on ne,na kasa fahimtar komai kada abinda nake tunani ne ya rabb ka kawo mana ɗauki"yarfe gomi dr yay tare da faɗin"Madan dole sai munyi bincike akan brain ɗinsa zan iya fahimtar abinda yake faruwa,kuma naga da ƙyar zai yarda a duba lafiyarsa"kuka Jiddah ta fara tare da ƙoƙarin cire Irfan daga bayanta amma yaƙi yarda,muryarta na wara ta juya gabansa sukai parcing ɗin juna kallonsa take shima ya shiga kallonta a hankali ta shiga magana dai² kunnansa tace"Ir..fan"kwaɓe fuska yay  tare da langwaɓar da kansa a shoulder ta shima yace"Irfan"damm zuciyarta ta bada sauti mai ƙarfi hawayen fuskarta ya ƙaro ta rasa abinda za tace sai kawai ta faɗa jikinsa ta saki kuka ta shiga mgn"no kada hakan ya faro dakai Ni Anty Amrah Twinst Buddy Mom Dad duk muna buƙatar rayuwarka da tunaninka kada kayi mana haka ba zamu jure ba"lamu yay jikinta yana sauraran abinda take cewa amma babu kalma ɗaya daya fahimta kamar yadda itama bai fahimci wacece ba,da wannan damar dr ya samu damar bashi injection lokaci kaɗan jikinsa ya saki numfashinsa ya fara fita a hankali alamar bacci zai ɗaukesa,cikin dr ya kamashi tare da kwantar dashi a kan bed ya bawa su Amrah umarnin barin ɗakin,dake Jikin Jiddah da sauƙi sai rashin ƙwarin jiki babu musu Amrah ta kama hannun Jiddah suka fita waje.
        Suna fita dr ya junawa Irfan wani abu a kansa ya shiga bincikensu na likitoci,lokaci kaɗan ya kammala murmushi dr yay tare da cire masa abinda ya juna,wayarsa ya ciro daga aljihu wata number ya shiga ringing biyu tayi a kai picking call  ɗin,shuru dr yay yana sauraran abinda ake faɗa  daga can ɓangaran,gyara tsaiwa yay tare da faɗin"Madam inaga basai anyi masa wannan Allurar ta hauka ba,da alama yay loosing  memory kinga aikin zaizu  da sauƙi"shuru yay da alama ana masa mgn daga can ɓangaren kafin ya numfasa yace"gsky Madam abinda Irfan yake ya huce ace masa pretending kawai dai kushirya plan ɗinku kafinsu bar asibitin"daga haka sukai sallama ya kashe wayar.

       

        Aryan pov
    Hankali tashe ya ƙarasu asibitin domin Amrah ta gama gaya masa komai a waya,yana zuwa ya gansu zaune lokacin hadda Dad da Abu suna zaune suna tattaunawa,bai tsaya ko ina ba sai office ɗin dr a zaune ya sameshi yana waya,katse kiran yay ya miƙawa Aryan hannu suka gaisa ya bashi wajan zama"no thank basai na zauna ba inason ta kaddar sallama  yanzun nan"da mamaki dr yake kallon Aryan kafin yace"a wannan conditon ɗin da Irfan ke ciki kakeson a baka sallama kayi tunani kowa?"cije baki Aryan yay tare da kallon dr yace"ni bana tunani ai abinda na yake shi nake aikatawa tunda nace kabani kawai kabani tun kafin fushina ya kufce a kan ka"dr baice komai ba ya shiga rubuce² a papper saida ya gama sannan ya  ɗaga kai yace" ga sallama nan as long as your wish"daga haka bai kuma cewa komai ba yaja P.c ɗinsa yaci gaba da latsawa,Aryan na karɓar takaddar yay waje hankalinsa kwace ya nufi wajansu Dad ya durƙusa har ƙasa ya gai dasu tare dayi masu bayanin komai amma a nan zasu bar Jiddah zuwa gobe ta ƙarasa karɓar drip ɗinta,gaba ɗaya sukai na'am da abun duk da Irfan ɗin ba wani lafiya garesa ba,nan suka shirya tafiya Dad da kansa ya ɗauko Irfan tare da sashi a bayan mota shima ya shiga Abu kuma ya shiga gidan gaba Aryan ya zauna mazaunin drever,suka bar Amrah da Jiddah acan itama anjima zata koma gida a hankali yaja motar suka bar harabar asibitin suka nufi jan Bulo gidan Dad.




             Hospital pov
   Misali 11 na dare wata mota tayi parking a bakin asibitin,mutane uku ne suka fito daga motar cikin manyan kaya na alfarma,babu inda suka tsaya sai emagency a ƙofar wani office suka sami dr da alama jiransu yake cikin sauri yay masu jagora zuwa room ɗin da take ciki,baka ganin komai a ɗakin sbd hasken ɗakin da aka kashe,kwance take flat numfashinta na sauka a hankali hannunta ɗauke da drip sauranne suka tsaya a harabar ɗakin guda ɗaya kuma ya nufi bed ɗin da take kwance hannu yasa da nufin ɗaukanta yaga an kunna fitila bai kawo komai ba dan haka yaci gaba da ƙoƙarin ɗaukanta kamar daga sama yaji ance"don't toch her"sauri ɗaga kai yay tare da juyawa nan yay tozali da samari guda 2 Irfan ne tsaye sanye t.shirt ash colour sai wando three gauter ya zuba hannayensa cikin aljihun wando haɗi da lumshe idonsa haiba da ƙiba da izzarsa sun ƙara fitow idan ka ganshi ba zakace shine yay magana ba,gefe guda kuma Aryan sanye da jallabiyi black colour mai ƙaramin hannu,ƴan sanda ne suka shigo tare da kama mutane  sannan sukayo kan dr cikin tashin hankali yace"ni...ni kuma me nayi?" Irfan ne ya taka zuwa inda dr yake kallonsa yay sosai tare faɗin"kaga nai maka kama da wawa ne,a zahiri na riga 4eyes farkawa amma abinda naji kana faɗe a waya lokacin daka shigo zaka duba ni shine ya tayarmin da hankali,kasu ganin baya nan sannan ta dalilin hakan a ɗaukemin mata wanda da alama duk wanda ya saka hakan yana da wani plan ne,shi yasa dana farka nayi wannan abinda kaga nayi hakan yasa ka fasa yimin wannan allurar daka shirya yimin ita,nine da kaina nasa Buddy yazu ya amshi sallamar kuma ni nace abar 4eyes nan ta hakan zan kama wanda sukeson raba zuciyoyinmu"yana faɗin hakan ya nufi bed ɗin Jiddah da take kwance tattausan hannunsa ya saka ya ɗauketa zuwa jikinsa,ajjiyar zuciya ta sauke ta ƙara shigewa jikinsa tana fitar da numfashi da alama bacci yay mata nisa,a hankali yakai bakinsa saitin kunnanta cikin lion voice yace"i'm sorry jerryn no mattet what we are to getter"ƙara mannata da ƙirjinsa yay tare juyawa suka bar room shi da Aryan,dr kuma ƴan sanda suka tisa keyarsa zuwa mota inda sauran suke,a hankali Aryan ke juya kan motar kallon titin yay yaga saho duk ya ɗauke hakan yana nufin dare yay sosai dan sha biyu saura,"Buddy nifa an cugeni yaseen"cewar Aryan taɓe baki Irfan yay kamar bazai magana ba sai kuma yace"like how"lumshe ido Aryan yay kafin ya buɗe baki yace"Amrah a gida zata kwana ita da twinst fa nida nasu jin ɗumin matata"banza Irfan yay masa ba tare daya tanka saba gaba ɗaya hankalinsa nakan Jerrynsa wacce take bacci hankali kwance"mtwws wai kana jin ina mgn"still idonsa na kan Jiddah yace"to ubanka kakeson nace ma,daman aikai manyan mata ne"wani wawan birki Aryan yaja a tsakiyar titi wanda yasa Jiddah tsorata harta ƙanƙame Irfan ta kwaɓe fuska da baki zatai kuka,naushi Irfan ya kaiwa Aryan ya goce shima kamar zai kuka yace"Allah yasa bamu yafe ba ko Jerryn ka firgitamin matana haka nan,sleep well my jerry kina jikin mijinki notin happen"saida Aryan yay dariya mai isarshi sannan yaywa motar key yaci gaba da dreving suna tafe yana mitar an masa kwacan mata a wannan lokacin yayinda Irfan yay masa banza,a haka suka ƙarasa jan Bulo a parlo suka tarar da Mom da kuma Dad hadda Amrah twinst kam sun daɗe dayin bacci,da sallama suka shiga parlon babu inda Irfan ya zarce sai ɗakin Amrah yana zuwa ya shimfiɗeta saman bed kayan bacci ya ɗauko ya sauya mata tare dayi mata addu'a yaja mata balget ta ƙaro gudan A.C sannan yay waje yana zuwa yaga babu Aryan shima sallama sukai da iyayen nasa ya nufi flat ɗinsa na gidan,a nan ya sami Aryan harya kwanta tea ya haɗa mai zafi tare da matsa lemon tsami wajan biyar a ciki ya shanye,ruwa ya watsa jikinsa sannan ya ɗaura bathrop ya faɗa bed bakinsa ɗauke da addu'ar bacci tunaninta fal zuciyarsa bacci ya ɗaukesa.. Asuba ta gari kwarzun namiji inji Jiddah😂

      *Afuwa Afuwa Afuwa nima ba a sanraina hakan ba,amma lafiya tafi komai gaba ɗaya bansa inda kaina yake ba,bana da ƙarfin yi maku typing kunsan da ai ba haka nake baku ba kuci gaba da hƙr a ƙara sani cikin addu'a i luv u all😍🥰ina gdy da addu'ar kuma inajin daɗi sai mun haɗe a next page...*

JIDDAWhere stories live. Discover now