*ASH'NAN*
_(LOVE AND ROMANTIC STORY)_*STORY AND WRITTEN*
_By_
*REAL ESHAA~**WATTPAD* _Realeshaa~_
*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarin sa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu Gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*SADAUKARWA GA:*
_My Aunty Baby tundaga farkon ash'nan harkarshen sa sadaukarwace agareki my son so fisabilillah._*TUNATARWA*
'''Likkafani is our last clouth.👚
Makabarta is our last home.🏬
Kabari is our last room.🏡
Makara is our last bed.😭(DO YOU THINK ABOUT KULLI NAFSIN ZA IKATIL MAUT).SO IS BETTER FOR YOU TO RECALL THIS WORD IS NOT PEMANENT THE DAY HAS COMING UNEXPECTED, THE DAY OF JUDGEMENT. '''
*PAGE 75&76* 🖊️
______________________________________📖Ba'ita tafarka daga nan'nauyan baccin daya dauketaba se misalin karfe 7:00am bakaramin mamaki tayiba ganin yanda tamakara kasancewar bata fiye irin wannan baccin ba"koda yake ba'abin mamaki bane idan Har tayi la'akari da rashin wadataccen baccin datake samu dakuma rashin kwanciyar hankali da nutsuwa.
mikewa tayi ahankali da zungureren cikin ta tashiga toilet, alwala tadaura sannan tayi sallah tana idarwa takoma toilet ruwan wanka tahada mai zafi,tagasa jikinta yanda yakama"trolley ta bude wayam tagani ba komai aciki,mamakine Yakama ta ganin babu kaya aciki,daga gefe tahango sif ahankali tamike tare da budewa"abin mamaki kayantane ajere aciki"murmushi tayi tana yaba mutunci da karamci irin nasu Mamie.Dogon Riga tasanya wacce baze takurata ba,kana tafeshe jikinta da turarukanta masu dadin kamshi,hijab tasanya tafito parlour ahankali tana tura zungureren cikin ta.
Hangosu tayi baki dayansu zaune suna hira cike daso da kaunar junansu.Momy ce tafara hangota dasauri tamike taruko hannunta fuskarta dauke murmushi takaraso wajen,tace daughter kintashi,sawu na biyu aikina bacci,bamu tashe kiba saboda lalularki sannan munsan kina bukatar hutu.kai ta jinjina cike da jindadin karamci irin nasu.zaunar da ita Momy tayi a kushin kusa da ita"gaishesu tayi cike da ladabi amsawa sukayi sunaimata yajiki,lubna da nabila ce suka gaisheta atare,da murmushi afuskarta,ta'amsa.
Breakfast mai rai da lafiya suka hada mata,zama tayi kusa da Mamie taci sosai sannan suka cigaba da hira tsakaninsu su lubna...Wani irin kula na musamman Mamie da Momy suke baiwa Ash'nan ko motsi tayi zasu tambayeta metakeso,kafin tabukaci wani Abu ankawo matashi,hakama Dady ba'abarsa abayaba"lubna da nabila nadebe mata kewa akoyaushe suna tare.Fa'iza ma nazuwa lokaci zuwa lokaci suna hiransu tare da debe mata kewa.Ayanzu ba'abinda ke damunta irin kewar mijinta tana matukar bukatansa akusa da ita,sede tun zuwanta bata sake sanya shi a idanunta ba,hakazalika ko labarin sa bataji awajen su Mamie"sede wani zubin Mamie kance mata khadija kidage dayiwa mijinki addu'a Allah yakarkato da hankalinsa garemu"Aduk sanda ta'fada mata haka yine take tana kuka tare da tausaya musu halin dauke ciki hakika suna matukar kewansa,hakan yasa tadage da addu'a Cikin dare zata tashi tana kuka tana rokon Allah yakarkato da hankalin mijinta garesu.
*******
Sosai abbu suka tsaya da addu'o'i dakuma rokon Allah duk inda yaji ana bada taimakon akan karya sihiri toh yana wajen,duk bayan kwana uku anaimasa saukan al'kur'ani mai girma tare da sadaka"Alhamdulillah sunfara ganin canji dan yakan kirasu lokaci zuwa lokaci yagaishesu anma bezuwa"kuma be tambayar ash'nan,kocewa agaisheta iyakaxinsa yagaishesu"hakan ma bakaramin farin ciki sukayi ba ganin Allah yafara amsa addu'o'insu,sede koda be tambayi ash'nan ba suma kuwa basu taba cewa gatanan sun san yanadawo wa hayyacinsa ze nemeta."Teemah tafara ganin canji daga wajen imraan,duk da sihirin begama warwareba " anma yarage tsoron ta aransa,sometimes idan yazauna seyaji tamkar yamanta Abu me muhimmanci arayuwarsa sede yakasa tuna ainihin wannan abin.
*****
Abangaren Teemah ganin Karfin sihiri yafara karyewa yasanya ta,komawa wajen bokan dasukaje anma tun kafin ta karasa wajen yadaka mata tsawa tare dacewa karki kuskura kikaraso wannan wajen,adalilinki kinsa ana konamana aljanu,sannan sunyiwa dan sarkin bakin aljanu illah,to kitabbatar idan wani Abu yasameshi bazamu kaleki mazaki bace mana dagani."Jiki na rawa Teemah tajuya tashiga mota,direct gidansu ta wuce tana zuwa ta'fada kan mahaifiyarta tare da fashewa da kuka"adame Hjy Habiba tadagota tana tambayarta abinda ke damunta.cikin muryan kuka ta zayyanewa mahaifiyarta abinda ke faruwa"tagumi Hjy Habiba tazabga tace gwanda ke Fatima ni yanzu baki daya mahaifinki yajuya min baya baya cin abincina, ko magana naimasa baya amsawa yadena bani kudi,komai na rayuwa yadena yimin"sakamakon sihirin daya karye dan nima naje wajen boka yajoreni fata fata yaimin domin de yan uwan dadynki suntashi tsaye da addu'o'i, shawaran da zanbaki kije kinemi mafita tun lokaci be kuremikiba.
Numfasawa Teemah tayi tace Momy munshiga uku idan wannan bokan beji kanmu yatemaka mana ba munshiga uku, anma nasan abinyi tana gama fadin haka tamike tare da zaran keyn ta tafice daga gidan.Tagumi Hjy Habiba tazabga tana tunanin rayuwarsa lokaci daya duniya naneman yimusu atishawan kaji.Teemah nafita direct Gidan su kubra tace,cikin sa'a tasamu kubra ita kadai agida"kubra naganinta tadaure fuska kamar bata taba dariya ba tace lafiya me yakawo ki Gidan mu?? Kokin manta wulakanci da kikayi min ne?? Dan Allah Besty kiyi hakuri nasan nayi kuskure,baki kubra ta ta'be tare da juyar da kai gefe"Ganin haka yasa Teemah durkusawa tare dabata hakuri,da kayar tahakura sannan tafadawa kubra dalilin zuwanta.Murmushin mugunta kubra tayi tace baki da matsala akwai wani boka nasan shi sosai kuma aikinsa kamar yankan wuka yake inde akwai kudi kikawo"jiki na rawa Teemah tasanya hannu acikin jaka tare da ciro kudi kimanin dubu Dari biyar ta danka mata"karba kubra tayi tace kije kidaura daga inda kikatsaya Momy nadawowa zanje wajen sa,godiya Sosai Teemah tamata sannan tatafi.
Tana tafiya kubra tafashe da dariyan mugunta tace ba gidan ubanda zanje,Allah ya kashe yabani,zama tagyara taci gaba da kallon ta."da dare kubra takirata awaya tare dacewa Besty aiki yagamu Imraan na hannunki seyanda kika juyasa"godiya tayi mata Sosai ta kwanta zuciyarta wasai Imraan yasake shiga hannu.*****
Juyi yake akwance yana karan to duk wata addu'a datazo bakinsa"zufa yake hadawa tamkar babu AC adakin afirgice yafarka,tare da furta _(AUZU BIKALMATILLAHI TAMMAT MIN SHARRI MA KHALAQA)_ Lalimen gefensa yafara yana kiran sunan ta khadija, khadija,khadija"arazane Teemah ta tashi tareda buga masa tsawa tace lafiya kake mana ihu cikin dare??hannu yasanya ya kunna haske"dafe kansa yayi yana karan to duk addu'ar datazo bakinsa,abubuwan dasukafaru yana dawo masa tamkar amafarki.ahankali yafara bude idanunsa yana binta da kallo harya gama sauke idanunsa akanta,kura mata idanu yayi kamar meson ganin wani abu ajikinta.
Wani shegen kallo take binsa dashi mecike da raini tace ina magana kawani zubamin ido lafiya zakatashi kana kiran wata shegiya acikin tsohon darennan??
Har yanzu yakasacewa da ita komai se ido daya kura mata cike da mamakin shi Fatima kefadawa wannan kalaman"bece da ita komai ba yamike tare da fita daga dakin,dasauri tamike tabi bayansa,daga bakin parlour ta tsaya tana kallon sa Har ya Isa sashen khadija, yana bude kofar yajita arufe dafe kai yayi yana furta duk addu'ar datazo bakinsa"mikewa yayi afusace kamar wani namijin zaki yatunkari sashen..._VOTE_ ✅
_COMMENT_
*And*
_SHARE_*ESHAA CE~*🤙🏻

YOU ARE READING
ASH'NAN
FanfictionLabarine me cike da soyayya ban tausay,hakuri,juriya,makirci,tawakkali