65&66

25 2 2
                                    

*ASH'NAN*
_(LOVE AND ROMANTIC STORY)_

*STORY AND WRITTEN*
            _By_
*REAL ESHAA~*

*WATTPAD* _Realeshaa~_

*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )

            *( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarin sa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu Gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

*SADAUKARWA GA:*
_My Aunty Baby tundaga farkon ash'nan harkarshen sa sadaukarwace agareki my son so fisabilillah._

'''HAPPY JUMA'AT KUTBAH ALLAH YASADAMU DA ALKHAIRIN DAKE CIKIN WANNAN RANA👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 YAKUMA TSAREMU DAGA SHARRIN DAKE CIKINSA'''

   *PAGE 65&66* 🖊️

__________________________________📖knocking din kofar Teemah tayi,tare da gyara tsayuwarta tana jiran taji anbude mata
"imraan dake kitchen yana hadawa ash'nan breakfaat yaji knocking, dakatar da abinda yakeyi yayi ya kalli ash'nan data 'daura kafa daya kan daya tana kallon sa,marereci fuska yayi yace my pretty nagaji barin kira Momy se tayi miki me dadi Wanda yafi nawa ko??,kukan sangarta tasanya tana bubbugu kafa kamar wata baby tace nide Allah naka nakeso inkuma bazaka min ba nahakura"Rungume ta yayi yana bubbuga bayanta cike da lallami yace wasa nake miki baby na kidena zubar min da tsadaddun hawayenki akan karamin abu"sake knocking din kofar Teemah tayi tanajan tsaki acikin ranta ganin yanda aka shanyata"My pretty barina duba waye ko?kai tagyada masa tare dacewa nima zanbika everlasting,murmushi yayi yarike hannunta sukanufi kofar yana goge saman goshinsa da flour yabata" ya lura wannan cikin yakara mata shawagwaba da sangarta ba gaira babu dalili seta hau yimasa koke tare da zabga masa shagwaba son ranta, tun wayewar gari ta addabeshi kancewa ita gurasa takeson ci kuma shitakeson yaimata"ba rarrashin dabeyiba kan tabari yakira Momy suyi mata anma samt aki yarda wai nashi,babynsa keson ci banasu Momy ba,ganin yanda ta tayar da rigimane yasanyashi lallashinta tare dacewa zeyimata,shinefa yafito yaketa tikar aiki duk yai kaca kaca da kitchen din dakuma jikinsa" itako tasanya shi gaba se dariya take, yana magana zatasanya masa kuka hakan yasa yabiye mata dan azauna lafiya.
Yana bude kofar yaci karo da Teemah tsaye,Up and down yakare mata kallo,cikin shigar dogon hijab take wanda yarufe mata baki daya ilahirin jikinta, gefen fuskarta akumbure yake inda yamareta jiya,'daure fuska yayi kamar beta ba dariya ba yace meyakawo kinan??Zubewa tayi akasa tare da rike kafafun sa cike da kissa tace ya imraan natuba dan Allah kafayemin hakika nasan nayi maka badai daiba anma,wlh nayi maka alkawarin bazan sake aikata lefi agarekaba wannan ma sharrin zuciyane dakuma shaidan Anma duk sanda kasake kamani dawani kuskure nayadda kayanke duk hukunci dake ganin yadace akaina,takarashe tana mefashewa da wani irin kuka me ratsa zuciyar duk wani mai imani da tausayi"Sake sa tayi takoma tarike hannayen ash'nan dake rakube abayan imraan tace dan Allah khadija kiyafemin abinda naimiki insha Allah hakan bazesake faruwaba nayi alkawarin zamu zauna lafiya.Tuni ash'nan tafara hawaye kasancewar ta mesaurin kuka,tace bakimin komai ba aunty Fatima inma kinyimin nayafemiki,wani miskilin murmushi tasaki  tare da rungume ta tace ngd kanwata aranta kuwa jitake kamar wuta tarike tsaban tsana"cikin wata raunanniyar murya tace dan Allah kitayani rokon mijinki ya yafemin lefin dana aikata agaresa bazan sake bijerewa umarninsa ba.Murmushi ash'nan tayi tare da langwa'bar dakai  tace Yaya dan Allah kayafewa Aunty lefinta tace baza tasakeba kuskurene.

Wani farin cikine ya ziyarci zuciyar imraan,domin yalura harga Allah Teemah tayi nadama,Hakan kuwa bakaramin dadi yamasa ba domin bashida burin dayawuce yaga kan iyalansa yahadu suna zaman lafiya tare da mutunta junansu"murmushi yayi yace Allah yayi muku albarka,ya bamu hakurin zama dajuna"nayafe miki Allah ya yafemana baki daya"rungume sa teemah tayi tace nagode Yayana Allah yakara dankon soyayya da kauna atsakaninmu kuma insha Allah bazan sake wani abinda zesanya kayi fushi daniba takarashe tana zubda hawayen munafurci"bubbuga bayanta yayi yace is Ok kukan ya Isa haka "hannunta ash'nan tarike tace mushiga ciki aunty Fatima,bamusu sukashiga imraan nagaba suna binsa abaya,direct kitchen ya nufa yayinda suka zauna a parlour,Ash'nan farin ciki yacika mata zuciya ganin Teemah tasauko zasuyi zaman lafiya abinsu" se hira suke da juna tamkar wasu kawaye,Teemah tasaki jiki kamar ba itaba.

Hannunsa dauke da plate yafito daga kichen Wanda ke shake da gurasa yaji albasa,tumatur,da cabbage,gayajin kuli da mai yawada ceshi"khadija nagani yawunta ya tsinke dasauri tamike taje takarba dan bazata Iya jiran shi yakarasoba,tana karasawa takarbi plate din zama tayi awajen dabas tasanya plate din agaba tafaraci,daga imraan har Teemah ido suka zuba mata cike da mamakin yanda takeci,kowa da abinda kesakawa aransa"imraan natausaya mata cikin dake jikinta dan yasan shi yasanya mata wannan ci dan yasan da bahaka takeda ciba"yayinda bakin ciki ya mamaye zuciyar  Teemah domin daganin girkin shakka babu imraan ne yayi ma wannan yar matsiyatan girki.
Muryan ash'nan yadawo da ita daga duniyar tunanin data lula,tace gaskiya Everlasting yayi dadi sosai anjima irin shi zakasake yimin ko??wani irin kallo yamata mecike da zallan so yace,naki ba gashi ko testing baki bani nayiba kincinye yafada yana nuna plate din da ba komai akai"Ido tazare tare da langwabar dakai tace sorry banice nacinyeba babyn kane,aikuwa sena hukunta wannan baby daya hana dadynsa mikewa tayi dagudu yabita suka fara zagaye parlour.
Wani malolon bakin cikine yaturnuke Teemah anma seta daure tace haba Darling brother so kake ka wahalarmin da baby na  ta'fada tana boye ash'nan a bayanta "
Dariya ash'nan tayi Wanda ke kara mata kyau akoyaushe tace,sosuke suwahalar dani ai"ido teemah tazare tace aiko bazan bariba"imraan bece komai ba yazauna atsakiyansu yana mejin dadin yanda Teemah tasauko suka hada Kansu.
Ahankali Teemah tace y imraan inaso muyi magana hankalinsa yamayar kacokam kanta yace inajinki!! mikewa ash'nan tayi dan basu waje suyi magana,hannunta Teemah tarike tace inakuma zaki??murmushi tayi tace zan shiga cikine harara Teemah tamaka mata mecike da tsantsar tsana aranta tace munafukar banza kawai wannan dariyar dakike yakusa zuwa karshe"anma afili setace aimun zama daya khadija kizauna dan Allah"zama ash'nan tayi agefenta tana murmushin jin dadin yanda Teemah tasake da ita.
Kallonsa yamayar kan Teemah yace ya'akayine sweet sis??wani dadi ne yaziyarci zuciyarta jin sunan daya kirata dashi,marereci fuska tayi tace daman jiya abinda yasa nadade bandawoba Momy ce ba lafiya zazzabi kedamunta seda akamata Karin ruwa shine natsaya natai makata da wasu abubuwa,inkabani izini inason zuwa indubata yanzu takarashe idanunta nazubda hawaye.

Wani irin tausayinta ne ya mamaye zuciyar imraan ahankali yace,kiyi hakuri nahukun taki batare danaji dalilinkiba,kishirya yanzu  muje mugaisheta"sake marerece fuska tayi tace no ya imraan baseka jeba,kazauna kakulamin da kanwata,dan badadewa zanyi ba jikinta kawai zanduba indawo"aunty Fatima nima zanbiki ingaisheta,murmushin dabe wuce saman labbanta ba tayi tace karkidamu sis nima badadewa zanyi ba zandawo wani lokacin maje tare,ta'fada tana mikewa.

"Mikewa imraan da ash'nan suma sukayi Har bakin mota suka rakata,tashiga,hannu suka 'daga mata harta fice daga gidan.sungumar ash'nan imraan yayi yanai mata cakulkuki harsuka shige cike se kyalkyale dariya take kan kushin yadireta ya tattare parlour,sannan yadawo sukaciga dawasan su irin na ma'aurata .

Teemah nafita takara gudun motar ta farin ciki fal ranta"Tana zuwa,kofar makeken gidansu tazabga hong dasauri megadin yawangale mata gate ta tura hancin motarta zuwa ciki.

Tana parking tafito da gudu tashige parlour Hjy Habiba, Hjy Habiba nakan dining tashigo dagudu tare da fadawa kanta cike da farin ciki tace Momy na dauko min maganin da'akabani,cike da murna Hjy Habiba tace gaskiya nayi farin ciki,domin banyi zaton zaki amince  ba yanda naga kinyi burus dashi"murmushi Teemah tayi tace ba lokacin bayqni yanzu Momy daukomin intafi zakiji komai daga baya" jiki na rawa Hjy Habiba tadauko mata,tana karba tafice daga gidan dasauri dankomawa ta aiwatar da kudunrinta kasancewar yau ita zata amshi girki....


_VOTE_
_COMMENT_
  *And*
_SHARE_


         *_ESHAA CE~*_🤙🏻

ASH'NANWhere stories live. Discover now