*ASH'NAN*
_(LOVE AND ROMANTIC STORY)_*STORY AND WRITTEN*
_By_
*REAL ESHAA~**WATTPAD* _Realeshaa~_
*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarin sa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu Gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*SADAUKARWA GA:*
_My Aunty Baby tundaga farkon ash'nan harkarshen sa sadaukarwace agareki my son so fisabilillah._*PAGE 69&70* 🖊️
____________________________________📖Tun wayewar gari take sa ranganinsa anma Har zuwa wannan lokacin shiru bashi ba'alamarsa hankalin ta bakaramin tashi yayiba,kasancewar koda be kwana adakintaba yakanzo ya
tasheta da asuba,anma gashi yanzu harkusan 11:00am bezoba kuma motarsa nanan bare tace koya fita"tanason shiga sashen Teemah taduba ko lafiya anma tana tsoron zagi da cin mutun cin daza tayimata hakan yasa takwanta batare data jeba daha bacci yai gaba da ita cike da tunani kala-kala aranta...kiraye kirayen sallan azahar ne yatasheta daga nannauyan baccin daya dauke ta batare data shiryaba"ahankali tamike tanufi toilet alwala tadaura sannan tazo ta tayarda sallah tana idarwa, taji wani maza kwakurin yunwa na barazanan kwakwale mata 'ya'yan hanji,Cikin sauri tamike tare da nufar kitchen dannenan abinda zatasanyawa cikinta" simple din abinci tahada Wanda zata Iya ci cikin karamin lokaci tahada,zama tayi tacika cikinta sannan takwashe plate din takai su kitchen.hamdala tayi ga ubangiji sannan tamike tanufi,sashen Teemah zuciyarta na dukan uku uku ahankali tasanya hannunta ta murda kofar jinsa tayi arufe"cike da mamaki tasajeyin knocking kasancewar bata fiye rufewa ba."tashafe sama da minti goma tsaye awajen anma ba'a bude ba,sake knocking tayi akaro na barkatai"jin karan bude kofar yasan tamaida hankalinta kacokam kai.
Ayatsine Teemah tafito cikin wasu shegun sleeping dress,tana huhhura hanci kamar tanajin warin iskar datake shaka"Cike da ladabi ash'nan tace ina kwana aunty Fatima,ya kwanan mai jikinta??" wani matsiyacin kallo ta watsamata tace da ban kwana zaki ganni??shiru ash'nan tayi batare datace komai ba se kallo datake binta dashi, tama rasa me zata mata"tsawa tabuga mata tace badake nake magana ba nace daban kwana ba zaki ganni??Har tabude baki da niyyan bata hakuri taji karan bude kofar"shiru tayi tamaida hankalinta kan kofar"Imraan ne yabude kofar yafito,cikin sanyin muryan sa yace sweet sis lafiya naji kina daga murya?? Kuka Teemah tafashe dashi tare dacewa yanzu duk abinda nakewa khadija agidan nan bata gani,kawai dan ta tambayeka shine nace bacci kakeyi,kuma bakason atasheka"shine kawai tahau zagina tana cemin munafuka wai ban isa naraba tsakaninku ba, inacewa ta tsaya tasaurareni ma anma taqi ta inda take shiga batanan take fitaba.
Rai amatukar bace imraan ya kalli ash'nan karo na farko daya kalleta dan tun fitowarsa be kalli inda takeba. Ashe bakida hankali khadija?? Fatima sa'arkice dazaki tsaya kina musayan yawu da ita hqrkina ki ranta da munafuka??shiru tayi tarasa abin cewa,se idanunta dataji suna kawo ruwa,cikin rawan murya tace wallahi Yaya bahaka bane banzage taba kawai ina tambayar Kane shine....'karan saukan marin dataji akun cintane yasa ta kasa karasa maganan datayi niyya,arazane tadago kanta tana kallon sa cike da dumbin mamaki"ita imraan yamara batare datayi masa komai ba.Kiwuce kibar wajennan kafin kisa na yi miki abinda bakiyi zato ba banza mara kunya karamar ki dake kin Iya fitsara"hannunsa Teemah tarike tare da langwabar dakai tace haba Darling brother bekamata ka mare taba kasan akwai yarinta atattare da ita,takarashe maganan tanakashewa ash'nan ido,hannunsa taja tace Darling brother mu shiga ciki kahuta ko bekamata kakulata ba,bece komai ba yashiga tare da banko kofa"dariyan mugunta Teemah tasheke dashi kamar bazatadena ba, tace daga yau kifara irga kwanakin kunci da tashin hankali dazakici gaba da fuskanta acikin wannan gidan!!duk wani walwala,farin ciki, nisha'di,yakare miki tunda ga jiya shawara daya dazanbaki shine karki kuskura kisake kwasomin wannan kafafun naki asashena inba haka ba tayi kwafa tare da cewa inkunne yaji toh jiki ya tsira tana gama fadin haka tashige tare da banko mata kofa...Dagudu ash'nan tashige sashen ta kan 3siter ta'fada tare da fashewa dakuka metsuma zuciya,cikin kuka tace _(Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un)_ wai shin meke shirin faruwa da rayuwatane??kuka tayi sosai Wanda yayi sanadiyyan sanyamata ciwon kai.
Da daddare misalin karfe 8:00pm tana kallon tashar sunna TV taji anturo kofar sashenta,dasauri tamayar da kallon ta wajen,kamshinsa yariga sanar mata wake shigowa"Dawani irin sauri tatashi tarungumesa sakamakon jin mayatetten kamshin sa datake mutuwar sanji akoda yaushe.Cikin muryan kuka tace Yaya am sorry innayi maka lefi kayafemin,anma bazan Iya juran fushinka ba pls forgive me,ta'fada tanasake rungume sa tamkar za'akwace mata shi"kasa ce mata komai yayi se kallon ta dayake,so yake ya rarrasheta anma yarasa ta yanda zeyi,atakaicema wani irin haushinta yakeji Wanda yarasa na meye,hannunsa tadauka tadaura akasan mararta tana shafawa tace everlasting kaji babyn ka yayi missing dinka soyake yaji dumin jikinka,still shiru yayi bece komai ba kana bejanye hannunsa daga cikin taba se bakinsa dayake motsawa"ahankali tarankwafo da kansa tare da hade bakinsu waje daya tashiga kissing dinsa kamar wacce tashekara bata gansaba"Jin karan bude kofar yasanyi shi tureta daga jikinsa cikin sauri, anma yamakara domin Teemah tagansu"Cike da takaici tace wato abinda yakawo ka kayi ko ta fa'da cikin tsawa,cikin rawan murya yace daman...dalla rufemin baki kawuce kayi abinda yakawo ka cikin rawan jiki yashiga yadauko wayarsa da da duk wani Abu daze bukata dayake bangaren ash'nan seda ya kwashesu"sannan tatisa keyarsa kamar wani danta"harara tamakawa ash'nan tace jarababbiya kawaita.Fadawa khadija tayi akan kushin tafashe dawani irin kuka metsuma zuciyar me sauraro cikin kuka tace innalillahi wai shin meke shirin faruwa da rayuwara ta ne??Kuka taci sosai da haka bacci mara dadi yadauke ta batare data shirya.******
Soyayya me 'karfi ne yasake shiga tsakanin lubna da Kamal"yayinda nabila da baba karami suka dedeta kansu,Har manya suka shiga maganar tasu"Sosai suka kulla soyayya me tsafta atsakaninsu tare da mutunta juna"Inda akasanya watanni biyar masu zuwa za'ayi bikin,murna wajen iyayensu ba'a magana domin bakaramin farin ciki sukayi ba yanda 'ya'yansu suka dedeta kansu domin sake kulla dankon zumunci.
Kamal da lubna baruwansu ko agaban kowa nunawa junansu kauna suke kamar zasu cinye junansu basa shakkan nunawa junansu so ko agaban kowa ne"sabanin nabila dasuke kunyar junansu Wanda bakasafai suka fiye hiraba ma kamar 'yan da, _(cewar lubna wai tun shekaru 'dari baya akadena irin wannan soyayyar aduk sanda tafa'di haka sede nabila tayi murmushi batare data tankamata ba)._*******
Yau kimanin sati uku rabon da ash'nan tasanya imraan acikin kwayar idanunta"tun ranan dayashigo Teemah tasanya shi agaba suka fita bata sake kallon sa ba koda takirasa awaya baya picking,koda massage ta tura babu replay,ba'abinda yasake sanyata cikin damuwa kamar daga jiya zuwa yau intakira wayar sa switch off.
Zaune take tazabga tagumi idanunta na zubar da hawaye tarasa yazatayi dole tana bukatar mebata shawara akai"dan haka tamike ahankali tasanya dogon hijab tafito dan zuwa tanemi izininsa asashena Teemah,aharabar gidan tahango Teemah da Kubra na magana suna ganinta suka kwashe da dariya suna nunata"Fasa zuwa tayi ta tambaya,sema dauke kai datayi daga kallonsu batare datace dasu komai ba tafice da gidan.
direct bakin titi tanufa taxi ta tare sannan ta fa'da masa inda ze kaita"tafiyar minti talatin yakaita "Sallamar mai taxi tayi sannan tashiga cikin gida da sallama dauke abakinta" Zaune tahango Ummi itada abbu suna shan hantsi dawani irin gudu tafada kan abbu tare da fashewa dawani irin kuka me tsuma zuciya,cike da damuwa abbu ya'dago kanta yana kallon ta,ahankali yace mamana ya'akayine daga zuwa se kuka??cikin muryan kuka tace abbu na kewarka nake ina matukar kewanku"murmushi abbu yayi tare da dagota daga jikinsa yana rarrashinta"shiru tayi tare da gaishesu,amsawa sukayi cike da kaunar yar tasu.
Hira sukayi sosai Har abbu yamike yatafi yabarsu"bayan fitar abbu ne Ummi tamaida hankalinta kan ash'nan cike da nazarinta tace khadija meke damunki??Domin tun zuwanta tafahimci akwai abinda ke damunta,sunkuyar da kai ash'nan tayi cikin rawan murya tazayyanewa Ummi komai "kai Ummi tajinjina tace da farko haka yake miki kokuma daga bayane yasauya?cikin muryan kuka tace a'a Ummi bahaka yakemin kuma natambayesa kowani lefi naimasa anma yace ba komai.
Kai Ummi ta jinjina cike da nazarin maganan ta tace toh kidage da addu'a kidinga yawan tashin dare kina mikawa Allah lamuranki sannan kirike sirrin mijinki,karkibari kowa yasan halin dakuke ciki ko ita abokiyar zaman taki karkidinga nuna damuwarki agaban idanunta koda abin yana damunki ki daure sannan kicigaba da addu'a kar ki gajiya.sosai Ummi tabaiwa ash'nan shawara masu kyau" sun Dade suna hira harse bayan sallan isha'i tatafi ahakama da kyar tatafi domin cewa tayi seta kwana sedataga Ummi tanuna fushinta sannan tafice tatafi.
Me taxi na ajiyeta akofar tangqmemen gidansu ta sallameshi sannan tashiga cikin gidan"kofar sashenta tabude tashiga,zubewa tayi akan 3siter"Arazane tajuya jinkaran bude kofar da karfi kamar za'acire"mutum tagani tsaye a kanta yana huci kamar wani namijin zaki....._VOTE_ ✅
_COMMENT_
*And*
_SHARE_*_ESHAA CE~_*🤙🏻

YOU ARE READING
ASH'NAN
FanfictionLabarine me cike da soyayya ban tausay,hakuri,juriya,makirci,tawakkali