*ASH'NAN*
_(LOVE AND ROMANTIC STORY)_
*STORY AND WRITTEN*
_By_
*REAL ESHAA~*
*WATTPAD* _Realeshaa~_
*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarin sa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu Gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*SADAUKARWA GA:*
_My Aunty Baby tundaga farkon ash'nan harkarshen sa sadaukarwace agareki my son so fisabilillah._
*PAGE 73&74* 🖊️
__________________________________📖Baka jin karan komai acikin motar se AC tamkar bamahalukin dake numfashi aciki. kowa da abinda yake sakawa azuciyarsa,dahaka suka Isa gida batare dakowa yace da dan uwansa komai ba.
Drive na parking lubna tafice dagudu,direct sashen Mamie tanufa tana shiga tafada kan Mamie tare dafashewa da kuka.Cikin sauri Mamie tadago kanta tace ke lubna lfy??shiru lubna tayi sejan zuciya datake kamar wacce tayi race"Wani abin yasamu imraan ko iyalinsa?? Mamie tasake tambayar ta cike da tashin hankali ganin yanda take Jan zuciya....Dede nan Momy da nabila sukashigo,dakin jiki asanyaye.Ido Mamie takura musu tana kallon yanayinsu hakika akwai wata matsala koda basuce da ita komai ba fuskarsu yanuna suna cikin yanayin damuwa.
Ahankali Mamie tace kusanar dani abinda ke faruwa Kunbar ni cikin duhu"numfasawa Momy tayi tace a gaskiya akwai matsala"ido Mamie takura mata kana daga bisani tace wani irin matsala??.
Tiryan tiryan Hjy Adama ta fada mata duk abinda yafaru batare bata boye mata komai ba.Rai abace Mamie tadauko wayarta tare da kiran layin imraan anma abin takaici akashe,kwafa tayi tace lalle dan yau wato imraan haryayi matar dazata sanya yadaki yar uwarsa sannan ya wulakantaku,wallahi zezo yasameni wato abinda yahana shi zuwa gidan kenan?"kai lubna ta dago wacce tunda suka shigo batace komai ba"tace Mamie Momy Ku kalli abinda idon Basira wlh ya imraan ba acikin hayyacinsa yakeba dan natabbatar dayana cikin hayyacinsa baze aikata hakanba.Harara Mamie tamaka mata tace kee banason shashanci,wato duk abinda yaimiki bakiganiba harkida bakin kareshi ke adole gamai dan uwa ko??Allah dagaske nake Mamie bawai sonake inkaresa ba sede gaskiya da zan fadi,Dan ranan da mukaje duba aunty khadija,da aunty Fatima tafito tana tafiya ba tagaisheda Momy ba..... Tiryan tiryan ta zayyanewa Mamie dakuma yanda imraan yanuna bacin ransa akan abinda tayi sannan damatakin dayace ze dauka"sannan tadaura dacewa wlh Mamie Yaya baya sakewa aunty Fatima ko kadan bare harya bata daman rainasa Ku kanku shedace"anma wai yau itake masa tsawa tana bashi umarni kamar dan ta,kuma datayi masa magana zakuga jikinsa yana rawa.Dan Allah Mamie kudubi magana ta da idon Basira karku yankewa Yaya hukunci akan abinda bashi ya'aikataba muddin kuwa kukayi haka kunshiga hakkinsa"tana gama fadin haka tamike dagudu tashiga daki tana kukan takaicin abinda Fatima tayiwa dan uwanta,itama nabila mikewa tayi tace Momy Mamie ku yi tunani akan abinda lubna ta'fada dan nima nagaskata maganan ta Yaya baze taba aikata haka dan sanransaba,tana gama fadin haka tabi bayan lubna.
Da kallo Mamie suka bi kofar, shiru parlour yadauka na wasu mintuna,Momy ce tayanke shirun tahanyar cewa a gaskiya Mamien twins na yadda da maganar lubna domin son bazetaba yin haka yana cikin hayyacinsa ba dole da abinda Fatima tashirya Wanda muba musan dashiba.
"Numfasawa Mamie tayi tace toh yanzu meye abinyi??ni aganina addu'a yakama mudage dayi sannan kuma sadaka,inyaso se asanarwa da dadynsu yasa atayamu da addu'oi a masallacai domin na lura kamar akwai sihiri" kinsan Hjy Habiba ba tsoron Allah ne da itaba zata Iya akaita komai dan cikan burinta"kai Mamie tajinjina cike da gamsuwa da maganan momy.Hakane insha Allah komai zedawo dai-dai koda kuwa ace wani abin ne,sosai suka tattauna tareda jajantawa junansu...
" Koda Dady yadawo Momy tasanar masa,da abinda kefaruwa dakuma shawaran dasuka yanke,se yabata rai tare dacewa shibaya son kananun maganganu da daukan jita jita ai lubna bata kyautaba dole imraan yahukunta ta koba aure tsakanin imraan da Fatima, ai Teemah yayartace taya zata daga mata hannu.Duk yanda Momy taso fahimtar dashi kin fahimta yayi haryaso yajanyo musu bacin rai ganin hakan yasa Mamie cewa tarabu dashi"ranan Dady fushi yayi dasu Wanda ko abinci yaki ci"Momy da mamie kuwa sharesa sukayi batare da sunshiga sab garsaba,washe gari da wuri yafice daga gidan ko break fast be tsaya yiba dan bakaramin fushi yadauka dasuba....
YOU ARE READING
ASH'NAN
FanficLabarine me cike da soyayya ban tausay,hakuri,juriya,makirci,tawakkali
