*ASH'NAN*
_(LOVE AND ROMANTIC STORY)_*STORY AND WRITTEN*
_By_
*REAL ESHAA~**WATTPAD* _Realeshaa~_
*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )*( F.W.A)🖌*
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarin sa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu Gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
*SADAUKARWA GA:*
_My Aunty Baby tundaga farkon ash'nan harkarshen sa sadaukarwace agareki my son so fisabilillah._*PAGE 79&80* 🖊️
____________________________________📖Ta dauki sama da mintuna tana jujjuya takardan takasa budewa,sewasu hawaye masu zagin gaske dasuka shiga zuba daga idanunta Wanda harsun 'kan'kance saboda kuka da take,kife kanta tayi da jikin kushin din inama mutuwa yazo yadauketa,datayi rayuwar kunci"muddin babu Imraan acikin rayuwar ta tobabu amfaninsa,hakika Imraan shine farin cikin rayuwar ta"bata sake tabbatar da hakanba seda ya tsinke igiyoyin dake tsakaninsu,tasan tayi babban rashi,wasu zafafan hawayene suka shiga bin kuncinta..
"dD 'kyar ta Iya mikewa tadauki hijab tasanya tareda daukar handbag dinta l,da kyar take tafiya saboda tsami da jikinta keyi ga yunwa dake addabarta" Har tafito coumpaund din gidan adurkushe take takasa tafiya me kyau,da kallo me gadin yabita hartafice"aransa yace hmm aidaman ramin karya kurarre ne.Tafiya tayi sosai kafin tasamu taxi"seda ta galabaita matuka,anma cikin rashin sa'a duk mai taxi data tare seyace baze dauke taba"ta tare taxi yafi biyar da kyar ana shidan tasamu,shima bakaramin kudi yatsula mataba,haka ta amince ta hau."Cike da zumudi ya danna hong mai gadi yabude masa,yana gama parking yafito karo sukaci da Dady dake shirin zuwa masallaci,l"dasauri ya karasa kusa da mahaifinsa yarungumesa cike da kewar mahaifinsa,yaushe rabon dayajisa ajikin mahaifinsa haka,hakika idan yakoma yasamu Teemah agida seya kusa kasheta tayi matukar cutur da rayuwar sa baya fatan ko alahira baya bukatar Allah yasa ya sake ganin fuskarta.Ahankali yaraba jikinsu yace Dady dan Allah kayafemin lefin danayi maka dakuma rashin zuwa gaisheku dabanayi dama abubuwan Dana maka acikin rashinsa"murmushi Dady yayi cike da farin ciki,yana godewa Allah daya dawomasa da dansa cikin hayyacinsa, yace bakamin komai ba Imraan Allah ubangiji ya maka albarka yakuma kiyaye gaba" ameen ya amsa,sannan yarike hannunsa kamar yaro suka nufi masallaci dan gabatar da sallar isha'i.Bayan sun idar da sallah ne suka wuce sashen Dady direct kasancewar yanason magana dashi.
Suna shiga sukatar da Momy da Mamie zaune asashena Dady suna jiran dawowarsa,bayan yashigo ya tsugunna tare da gaishesu"amsawa sukayi cike da farin ciki.
Gyaran murya dady yayi Imran yakira sunan sa cike da so"Na'am Dady ya amsa cike da ladabi"Daman kan maganan aure kannenka, ne da'anyisa tun abaya anma sanadiyyan halin dake ciki yasa aka'daga,yanzu kuma tunda Allah yasa komai yayi dai-dai za'adaura auren nan da sati biyu so duk wani shirye shirye daya kamata muyi munyi sa saura kai akejira kuma, kaima Allah yadawo dakai lafiya"kai ya jinjina cike da ladabi yace insha Allah Dady daga gobe zanfara gudanar da duk abinda Yakama insha Allah " toh Allah yamaka albarka" ameen ya amsa sannan yamusu sallama yafice,yayinda Momy Mamie da Dady suka cigaba da tattaunawa kan yanda tsare tsaren bikin zekasance.
Zaune yatarar da lubna da nabila na kallo acikin tashar zee TV,suna ganin sa suka yashi dagudu suka rungume sa"murmushi yayi tare da basu peck a goshinsu yace my lovely sisters I love, sake rungume sa sukayi tare dacewa muma munasanka yaya.Kallon parlour yayi yace ina khadija??tana ciki tace yau bacci takeji da wuri"murmushin gefen baki yayi yace nabila jeki bedroom din Momy kidauko min key part dina,sekuje tare da lubna kugyara min"toh yaya suka amsa tare da mikewa.Yana ganin fitarsu yamike tare da nufar dakin khadija,kwance yatarar da ita tana baccin ta cikin kwanciyar hankali se dan yamutse fuska da take alamar batajin dadin kwanciyar"murmushi yayi tare da kwanciya agefenta soft lips dinsa yasanya akaran hancinta yafara tsotsa yana lasan saman labban ta"bakinta ta bude tare da turo harshenta wajen tana kokarin kamo harshensa"murmushin gefen baki yayi tare da sake dauke harshensa daga saman labbantaba yamayar saman lulu eyes din ta yana lasa,Cikin baccin ta tura baki tare da kwabe fuska.Hancita ya lakuce mata yana murmushi,ahankali tafara bude dara daran idanunta masu matukar haske da kashe jikin me kallon sa,akan kyakykyawar fuskarsa me cike da kwarjini tasauke dara daran idanunta wani lallausan murmushin sa tsada da tafiya da imanin duk wata 'diya mace yasakar mata"hannayenta ta sakala awuyarsa cikin muryanta irin na me bacci tace shine se yanzu zakadawo babyn ka yayi fushi dakai bakazo da wuriba"wani killer smile yasakar mata yace taso muje inbaki wani abin mamaki"Ina zamu?kede taso muje kigani"ahankali tamike tare da sanya hijab hannunta yarike suka fita.fitarsu yayi Dede da shigowar lubna da nabila, key lubna tamika masa tace gashi yaya angama"thanks Allah yaimuku albarka yabaku yaya masu biyayya.Ameen lubna ta'am yayinda nabila tayi murmushi batare data ce komai ba"bece dasu komai ba Yakama hannu ash'nan sukafice,suna fita taja ta tsaya tare da kwabe fuska!! menene?? Ya tambayeta cike da kulawa nagaji tace dashi,hannun rigarsa yanade tare da daukar ta kamar baby hannu tasanya tasakalo wuyarsa tare dabashi light kiss asaman labbansa.Murmushi yayi yace zan rama nima "suna shiga ko ina tsaftsaf se kamshin room freshener yake,direct bedroom din sa yawuce da ita yana shiga ya kwantar da ita akan makeken gadonsa,hijab din yacire mata tare dazama akusa da ita mikewa tayi takoma kanciyarsa tasakalo hannayenta awuyarsa tana kokarin hade bakinsu"dasauri yajanye kansa yana tura baki" hannu tasanya yajuyo da kansa,kwayar idanunta ka'dai yagani ya fahimci halin datake ciki.
Cikin muryan ta dayafara sauyawa tace I want kiss u,please allow me kiss u"sekin yimin alkawarin zaki barni mugaisa da babyn na"kai ta gyada masa alamar zatayi"kafin yasake cewa komai ta hade bakinsu waje daya tafara kissing dinsa cike da kewarsa,hannunta tashiga yawo dashi asasan jikinsa tana romance dinsa"burkicewa junansu sukayi suka shiga aikawa da junansu sakonni masu wuyar fassarawa,daganan kuma labari yacanza salo awannan Daren Imraan yanunawa ash'nan zallan so dakuma yanda yayi kewarta"itama anata bangaren hakan yakasance...*******
Me taxi na ajiyeta tafito ahankali tanufi cikin gidan su,shigarta yayi Dede da fitowar mahaifinta daga sashen ta"tana kallon sa tazube akasa tare da fashewa da Wani irin kuka me ratsa zuciyar duk wani mai sauraro,takasa furta koda Kalma dayane se ajiyar zuciya datake saukewa"Ahankali Dady yanufi inda take tare da dagota zuwa jikinsa,direct sashen Hjy Habiba yanufa da ita yana kallon yanayinta baki daya haliitar fuskarta yacanza"Hjy Habiba na kallon halin da yarta ke ciki tafashe da kuka tare dacewa mezangani ni habiba waya miki wannan danyen aikin??Wani matsiyacin kallo Dady yawatsa mata yace aiduk abinda kashuka shizaka girbe"kallon sa yamayar kan Teemah, yace Fatima me yakawo ki??hannu tasanya Cikin jaka taciro masa takardan karba yayi yabude,abinda yake furta face innalillahi wa'inna ilahiri raji'un"ganin saki biyu da Imraan yarubutawa Fatima.ba'abinda Dady ke fitarwa ajikinsa se zufa tankar ba AC adakin,wani irin razananniyan mari yasakewa Teemah Wanda seda ta dungura daga saman kushin din,yace Fatima me wannan?? Auren ki kika kashe,cikin rawan murya tace wlh Dady sharrin...aibe Bari takarasabe yasake kwasheta dawani Marin dayafi Na farko yace dan uwarki kinyi zaton bansan makircin dakuke 'kullawa bane keda uwarki ,wato seda takeshe miki auren hankalinku ya kwanta ko toh kinyi ganganci fatima kinbiyewa sakaryar uwarki takai ki tabaroki atunaninku bansan mekuke aikatawa aboye bane??saboda bakida cikakkiyar hankali shine yanzu zakidawo min gida..Toh Wallahi tunda kika yadda ki ka kure Imraan duk hakurin sa haryakai ga sakin ki sekinemi gidan wani uban ba wannan ba maza tashi kifice kafin na illataki,dan bazan zauna dake ba........
Not edertting🙏🏻🙏🏻🙏🏻
_VOTE_ ✅
_COMMENT_
*And*
_SHARE__*ESHAA CE~*_🤙🏻
![](https://img.wattpad.com/cover/247267095-288-k925901.jpg)
YOU ARE READING
ASH'NAN
FanfictionLabarine me cike da soyayya ban tausay,hakuri,juriya,makirci,tawakkali