83&84

38 1 0
                                    

*ASH'NAN*
_(LOVE AND ROMANTIC STORY)_

*STORY AND WRITTEN*
            _By_
*REAL ESHAA~*

*WATTPAD*  _Realeshaa~_

*FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( Ƴanci don cigaban al'umma, ƴan ci ya ɗara bauta, freedom writters._ )

            *( F.W.A)🖌*

https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarin sa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu Gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

*SADAUKARWA GA:*
_My Aunty Baby tundaga farkon ash'nan harkarshen sa sadaukarwace agareki my son so fisabilillah._

   *PAGE 83&84* 🖊️

____________________________________📖Kana da hankali kuwa Imraan kasan me kake fa'da??Anma ai ranan cewa kayi kuna tare?kafada min gaskiya kode yaune ka koreta,?dan bansan ka da karya ba banaso yaukuma kafara" Sunkuyar da kai yayi cike da ladabi yace Momy maganan gaskiya bana tare da Fatima tun ranan dana fahimci abinda tayi min nasaketa, domin bazan Iya zama da matar da tayi min asiriba,kana tarabani da duk wani makusanci na,Momy kiyi hakuri abisa karyar danayi muku anma maganan gaskiya nasaki fatima bazan Iya zama da ita amatsayin matataba nariga dana yanke duk wata alaka dake tsakaninmu.Duk wannan maganan dasu keyi Iya tsakaninsu sukeyi batare da Ash'nan taji me suke fada bq.Salati Momy tasanya tace son Ashe bakajin magana,yanzu duk maganan damuka fa'da maka sedaka saketa? tafada cike da bacin rai dan Sam bataji dadin sakin dayayiwa Teemah ba duk dakuwa Teemah ta tafka babban kuskure anma Sam saki bashi ne mafita ba"shiru yayi kansa akasa bece komai ba sede shi kam bega dalilin dazesa ya mayar da Fatima ba...Afusace Momy tace ba magana nake makaba kayi banza dani?? Har ya bude baki daniyyan magana kukan jariran yakarade dakin baki daya hakan ya daka tardashi"dasauri yamike yadauki baby, me matukar kama ka dashi kamar antsaga kara, bakinta da idanunta ne ka'dai kekama dana Ash'nan anma baki daya kammanin ta na Imraam ne yayinda mazan baki daya kamannin abbun Ash'nan suka dauka hanci da idanun sune ka'dai irin na Imraan.
"Misalin karfe 10:00am Kamal da lubna sukazo zuwansu ba dadewa Sega nabila da baba karami sunzo"murna awajen su ba'a magana zakiyi zaton su suka haihu dan farin ciki baki daya se jagwal-gwala baby's din sukeyi kowa nacewa kama dashi suke,Kamal ya matso kusa da lubna tare da rada mata my choice karki damu inmun koma gida zanbaki irknsu" fari tayi da idanunta tare dacewa Allah dagaske Honey? Kai ya jinjina mata alamar "eh" dariya suka fashe dashi,Wanda yajanyo hankalin mutanen parlour baki daya"harara Imraan yamaka musu batare dayace komai ba.Se bayan sallar isha'i suka tafi cike da daukin baby's din,Sosai Momy da mama jummai sukebawa Ash'nan tare da baby's dinta kulawa  acikin kwanaki shida sunyi bulbul dasu Ash'nan tayi cikowar jegu,kowa yagansu seya yaba kyau da cikowar su"tun ranan da Imraan yasanarwa  Momy yasaki Teemah bata sakeyi masa magana akaiba" bakaramin dadin hakan yajiba domin azatonsa tahakura da maganan ne"Abinda besani ba tun aranan Momy takira Mamie tasanar mata duk yanda sukayi,sannan tace tasanarwa da Dady lokacin da Mamie taji ranta bakaramin baci yayiba hakama Dady dan besan dawani ido ze kalli yar uwarsaba ko jiya ma sunyi waya anma ba tasanar masaba"hakika Imraan betaba bata masa rai irin na wannan karon ba,harya cire waya zekirasa Mamie tadakatar dashi kan yayi hakuri agama suna idan yaso seyasashi agaba suje yamaidaya"hakan akayi Dady yadauki shawaran Mamie kan cewa sebayan suna zesa Imraan yamaida Fatima.

*****
Zaune take akan praymat misalin karfe karfe 3:00am yayinda hawaye suka wanke mata fuskarta cikin muryan kuka tafara yiwa Allah kirari da kyawawan sunayensa tana kuma rokon sa daya yafemata kuskuren ta nabaya sannan yaza ba mata miji mafi alkhairi acikin rayuwar ta hakika seyanzu tasake tabbatar da irin kuskure dakuma wautar datayi abaya nabijirewa umarnin ubangiji haryakaita ga aikata shirka agaresa.
Daga cikin halayyar Teemah kashe dari na banza yanzu babu koda guda daya,tanutsu akullum azumin litinin da alhamis baya wuceta haka zalika nafilar dare baya wuceta akullum seta tashi cikin dare tana kuka tana Neman gafarar ubangiji ka yayafemata zunuban data aikata kana yacire mata soyayyar Imraan aranta,domin akullum jitake soyayyar sa nasake nukkuwa acikin zuciyar ta kowani bugu da zuciyarta keyi da soyayyar keyi"Hjy Habiba bakaramin tausayawa yarta takeba ganin yanda takoma tarame tayi wani iri da ita akullum setayi kuka tare da rokon gafarar Teemah domin duk ita tasanya ta acikin wannan yanayin datake,duk Wanda yasan Hjy Habiba da Teemah abaya yanzu baze ce subane saboda nutsuwa dakuma nadama dasu kayi "Lokacin da kubra tazo Teemah ta'fada mata halin datake ciki jikinta bakaramin sanyi yayiba dan haka itama tawatsar da duk wasu mugayen halayyarta tafitar da daya daga cikin samarinta dake mutuwar sonta matansa biyu yara goma,haka ta'amince zata auresa,haka Hjy Zainab itama tatuba ga Allah tagyara halayyarta sede mijinta yakara aure Inda ya auro irin masifaffun matan nan Wanda bazasu shiga sabgarkaba anma idan kashiga nasu basuda mutunci.
"Dady bakaramin tausayawa Teemah yakeba ganin yanda duk ta lalace kamar ba Teemah yar gayu,meji da tsiwa ba, kullum cikin rokon dady gafara take hakan yasa yake matukar tausaya mata" tare dayimata addu'ar Allah yasa tagama Idda lafiya tasamu miji nagari Wanda zeriketa amana domin yasan Imraan yamata nisa,Nisan da bazeji kiraba.

ASH'NANWhere stories live. Discover now