SANADIN MATAR UBA
Oum.... Now and old
4
Bayan Ummi ta fito daga cikin gidan alhaji sauban nehh ta hango janah wadda tun dazun ita kadai take jira janah tana ganin ta ta taho da Sauri tare da fadin komai dai ya tafi yarda akeso koh Kawata
Cikin kwarin gwuiwa ta kalleta tana fadin komai ya kammala dan nasan tarkona ya kama babban kifi kedai kijira babban sakamako dan nasan alhaji sauban ba zai taba bari mutunchin sa ya zube ba
Tana kaiwa nan ta ka hannun janah suka bar kofar gidan alhaji sauban
Suna tafiya suna dan taba fira har suka isa kofar gidan su janah kawai Ummi taja ta tsaya taki shiga cikin gidan janah tace hmmm su Ummi yau kuma gidan namu nehh baza'a shiga ba to Mu kuma me mukayi
Ummi ta kalli janah tace lalle yau natabbatar da kin samu matsala kisani munayin wani sake Maman Ku saita gano ina da ciki kisani dole saina dauke kafa da xuwa gidan indai munaso asirin Mu ya rufu
Jinjina kai janah tayi sannan tace tabbas maganar ki haka take kawata to yanzu ya za'ayi kenan ummi
Ummi tace kawai gidan Mu zan koma da xama baki daya idan yaso sai ina amfani da kudin da alhaji sauban ya bani kafin lokacin da zanji sakamakon sa
Ummi tana gama fadin haka tayi wa janah sallama a zuwan zatazo gidan su anjima
Ummi tafe tana Yan wake waken ta ga file din ta a hannun ta tana tafiyar ta tamkar ba abinda ya dameta kwatsam sai ganin mota tayi a gaban ta ta tsaya gilas din aka zuge ba kowa bane acikin wannan mota ba illah PA din alhaji sauban kallo ya fara bin ummi dashi sama da kasa kallon raini da kuma me kike dashi da alhaji zai damu a kanki haka tabbas kinyi babban kuskure dan alhaji ya fiki shu'uman ci
Murmushi ummi tayi mai sauti kafin tace Malam PA mai kuma ya kawo ka nan da har zaka tare min hanya ina gargadin ka da ka yi maza ka matsamin GU na wuce koh na baka mamaki a gurin da
Cikin mamaki ya kalleta wata yarinya da ita amma take fadin zata masa wani abu a wulakance ya kalleta kafin yace idan naki matsawa mai zaki iya
Cikin tsiwa tace kanason kaga abinda zan yi nehh yaro
Cikin zafin rai ya fito yana fadin ke uban wa kike cewa yaro
Tace ubanka mana
Da sauri ya kawo hannu zai zabga mata mari ta sunkuya bai sameta ba tana dagowa ta zabga masa mari har biyu tana Marin sa tayi sauri ta dame kunchin ta tare da durkushewa kasa ta fashe da kukan karya
Wasu mutane nehh sukazo wucewa suka tadda abinda yake faruwa da sauri suka ruks PA dake shirin yin boll da ita yana wuce nan suka fara bashi hkr da sauri ummi ta taso ta chakumi wuyan rigarsa tana janya tana fadin ni ka kamara koh to wlh sai ka San ni ka Mara kuma zan baka mamaki wlh sai ka San ni ka Mara
Sakin baki yayi yana kallon ta kamar wani gaula mutanen nan nehh suka kallesa suna fadin haba bawan Allah wai Marin ta ma kayi gsky baka kyauta koh kadan Marin mace akan titi gsky Allah zai saka mata ai basu gama rufe bakin su ba ta kuma kwada masa mari ya dafe kuncin sa dai dai saitin kuncin sa tazo a hankali ta furta indai na shiga gidan alhaji sauban to ka rasa matsayin ka nasan shi yaturo ka to kaje ka fada masa nace yazo da kansa idan ma mgn zamuyi sai muyi bata kuma bi ta kansa ba ta shige tayi tafiyar ta
Gogan naku koh sai huci yakeyi inda mutane ke ta bashi baki haka ya hau motar sa ya koma inda ya fito
A harabar gidan ya samu alhaji sauban sai kai kawo yaketayi yana ganin PA ya taho da sauri yana fadin komai ya gama kammaluwa koh PA nasan ka na daga nan ba maza fadamin ina nehh idan nasu
Murya kasa kasa PA yace banga gidan da take ba amma nasan gidan su kawar ta na bi bayan ta nehh a hanya ta tareni tace wai idan kanason magana da ita to kaje inda take kasame ta
Kamar wani mahaukaci alhaji sauban juya yana fadin jirani PA ina zuwa babban Riga ya dauko ya shiga mortar yace suje gidan kawar ta ta
Janah na tsakar Gida tana wanki yaro yayi sallama yace wai ana kiran janah
Janah tace kaje kace wai injiwa
Bayan mintuna yaron ya dawo yace wai inji PA din alhaji sauban wai yanzu zaki koma tana jin haka tayi saurin dauko hijab din ta tayi waje
A mota ta samesu shida alhaji sauban tana ganin alhaji sauban tasha jinin jikin ta kuma nan da nan tasan aikin gama ya gama maganar farko da ta fara fitowa daga bakin alhaji sauban shine inane gidan su ummi
Janah tace chan nesa kadan nehh ba nisa yace zaki iya rakamu tace mai zai hana nan ta shiga motar har gidan su ummi wannan kangon ta rakasu alhaji sauban ya kalli janah yace inane gidan nasu tace gashinan ina zuwa bari na kirama ita bata jira amsar sa ba tashige gidan
Kallon suka bi gidan dashi alhaji yace wai yanzu mutum nehh yake rayuwa nan tap bai gama rufe bakin sa ba saiga ummi da janah sun fito a gidan ummi na sanye da gyalenta Wanda ba abinda ya rufe mata a jikin ta illah kirjin ta
Suna isa bakin motar janah tace to ni fahh aiki nake ummi ni natafi sai anjima bata jira amsar ta ba tayi tafiyar ta itako ummi jatayi ta tsaya a gaban motar batace kala ba
Alhaji sauban yace haba gimbiya shigo mana mgn zamuyi ta fahimta dan Allah ki shigo
Kallon sama da kasa ta masa Tukun ta kalli PA dake cikin motar ta kauda kai nan take alhaji ya gano manufarta dan haka ya kalli PA yace jeka waje zamuyi mgn da sarauniya ta ba musu ya fita a motar zuciyarsa cike da bakin ciki da kuma jin haushin wannan yarinya
Yana fita ummi ta shiga motar tare da zuge glass sannan ta kalli alhaji sauban tana fadin nasan zakazo alhajina shin wace mafita ka yankewa kanka iye
Bata rai yayi sannan yace to ke vazaki chanza wani abu ba gsky sharadin da kikasa yayi tsauri banda ra'ayin mata biyu ki chanza wani abun koh meye shi a duniya zanyi
Wani banzan kallo ta masa kafin tace hb alhaji an fada ma ina mgn biyu ka sani idan nace yes to kawai haka amsar take bata chanzawa ni zabi na baka idan kuma bai ma ba banma dole ba dan haka kaga tafiya ta duk sanda ka shirya nima a shirye nake tana kaiwa nan ta bude murfin motar zata fita
Da sauri ya kamo hannun ta yana fadin haba ummi to kuma ina zakije dan ki tsaya ki fahimceni mana
Tace ba wata fahimtar kasa zanyi nidai na gama mgn sabida haka ka sake ni na tafi idan wa'adin dana dinar ma ya cika banjika ba to zanyi abinda ya kamata
Da sauri yafurta shikenan ummi naji zanyi duk abinda kikace shikenan
Juyiwa tayi a hankali da murmushi a fuskarta hannu biyu tasa ta kama kumatun sa sannan tace gsky kayi tunani mai kyau alhajina shiyisa nake sanka to yanzu yaushe za'a daura auren yace koh yauma idan kin shirya
Tace ba yauba saidai nan da sati daya yanzu zan kaika gurin babana ka nemi aurena sai kusa sati daya ayi komai a wuce gurin ba musu ya bita kai tsaye gidan su janah suka wuce sukabar PA anan gidan su janah ta shiga har gun abban su tayi masa bayanin komai kuma tace sati daya za'a ba tare da tunanin komaiba ya fito a matsayin sa na uban ummi suny mgn da alhaji sauban inda suka sa sati daya daurin aure kamar yarda ummi ta bukata anan kofar gidan su janah za'a daura auren.............
WANNAN KENAN

YOU ARE READING
SANADIN MATAR UBA
RomanceLbr nehh akan wani azzalumin uba daya yi sanadin gurbata rayuwar yarsa ta cikin sa