SANADIN MATAR UBA

756 6 0
                                    

SANADIN MATAR UBA




Oum.... Now and old



_Sakamakon qorafi na wasu masu qarancin fahimta yasa dole badon munaso ba zamu mayar da littafin nan na kudi akan farashi daidai aljihun kowa just 100 kawai idan kinaso tuntubi wannan number zaayi Miki bayanin yanda zakici gaba da samunsa cikin sauqi._

_09013718241_




29







Sun jima a gidan kafin kalid ya tashi yana fadin ya baban soyayya zamu iya tafiya ina da abinda zanyi yanzu nehh






Cike da mamaki imran ya kalli kalid sabida bai saba hakan ba kuma duk abinda kalid zai yi imran yana fara sani kafin yayi amma sai gashi yau yana fadin akwai abinda zaiyi Wanda shi bai San dashi ba cike da mamaki ya kalleshi yana fadin





Abokina me zakayi haka Wanda yafi antinmu muhimmanci haka ya fadi haka yana kallon jamsy da ita ko ya kalid din ma batayi






Shima kalid din kallon ta yayi kafin ya ruke fuskarta ya yi murmushi tare da fadin ai duk duniya ba abinda yafi wannan a guna a kullum addu'a ta na kasance tare da ita har abada


Tabbas taji dadin kalaman Sa ammabata nuna hakan ba ko kadan Dan bataso ya gane taji dadin hakan





Mikewa tayi tare da fadin nikam na gaji bacci nakeji kallon safna tayi wadda har yanzu tana jikin imran tace bestyna idan an gama shan soyayyar sai kizo ki tayani baccin Dan kinsan bazan iya ba ba tare da ke ba







Murmushi safna tayi tare da fadin OK bestyna nima yanzu zan taho Dan nasan tunda uncle kalid ya tashi to baby shima tafiya zai yi so ganinan nima yanzun nan






Jamsy bata jira abinda zasu kuma fadi ba tayi gaba abinta daki ta shiga tabi lpyar gado ta lafe ita kadai tana tunani da yawa gaba daya bata jin dadin jikin ta Dan ji take kamar yau wani Abu yana shirin faruwa da ita ko bestyn ta addu'a ta farayi tana Neman tsari da taimakon uban giji da haka bacci ya kwace ta safna bata shigo ba









Imran kam da yaga jamsy ta shiga ciki yasan komai ya kare Dan safna bazata zauna ba kuma ba haka yaso ba bai gama kallon abar kaunar sa ba badan yaso ba ya mike sukayi sallama irin ta masoya sannan suka tafi ita kuma safna saita zauna a falon ta dauki wayarta ta hau chat tama manta da gayyatar baccin da jamsy ta mata









Tafiya suke Inda kowa zama kurma kalid nehh ke Jan motar inda imran yayi shiru yana tuna abubuwa da yawa gaba daya kuma tunanin nasa akan safna nehh yayi nisa sosae da sosae yaji muryan kalid yana fadin abokina ina zamuje nehh wai yanzu






Da sauri imran ya juyo yana fadin na'am safna ai duk inda zamuje muje muddin ina tare da ke bana gajiya





Marin wasa kalid ya masa cike da jin haushi yana fadin imran wlh idan baka ragewa kanka wannan abin ba ko to wlh sai ya maka illah na fada maka







Bata rai imran yayi tare da fadin ka fara ko ka fara ko na fada ma ka ba ruwan ka da sha'anina da safna amma kaki yarda to Dan nayi tunanin ta tunanin budurwar ka nayi tawace fa kuma ina Santa tana sona kuma auren ta zanyi ta aure ni so dan Allah banason sa ido








Sosae kalid yaji maganar nan amma sai ya danne yana mai kauda kansa gefe a ransa yace zaka aureta ko to xanga ta yarda hakan zata faru kaiko ka aureta saidai ka auri fanko wlh Allah








Wani gidan sa ya nufa dasu dake nan cikin badawa layout ba laifi gidan kato nehh yaji komai da komai na more rayuwa Dan haka suna shiga tare kai tsaye imran lambu ya nufah Dan dama shi idan suna nan to anan nehh gurin zaman sa





Abin sha kalid ya je hada musu kamar yarda ya saba amma wannan karon sai ya dauko wata kwayar bacci ya zuba a cikin abunshan imran ya kawo musu hadawa sukayi sannan suka faa sha imran nashan nasa yaji dandanon ya chanja amma bai kawo komai aransa ba Dan wani lokacin kalid na sa musu wasu kwayoyin Dan suyi Chaji amma kuma abinda ya dan rikitashi dan danon wannan ba irin na ko yaushe bane kawai dai ya basar shiko kalid ko kallon sa bayayi dan karya gano wani abu sabida imran akwai gane Abu da wuri








Bayan minti goma da shan lemon imran yaji bacci yakeji sosae dan har ya fara gyan gyadi kalid na ganin haka yace abokina ya dai lpy





Bude manyan idanun sa yayi da suke lumshewa da budewa yace nrml abokina bacci dai nakeji dan taimakamin zuwa daki mana





Ba musu kalid ya dan rukeshi har daki ko takarmin sa bai cire ba ya baje ya kama baccin dolen diya






Kalid na ganin haka yace yes Allah yasa shiri na yayi aiki waya ya dauka ya fice tare da janyo kofar ya sa mata keyyy y number safna ya kira tana falo azaune har yanzu tana chat da wasu kawayen ta da suka Dade basu hadu ba ganin kira tayi ya shigo saidai number din private number nehh da bazata daga ba amma sai ta daga tare da yin shuru tana addu'o'i a ranta kamar daga sama taji an fashe da kka kuma muryan namiji nehh






Sunan ta ya fara kira yana fadin safna wayyo safna abokina zai mutu safna dan Allah kizo





Ai nan take ta dauki murya a matukar rikice ta fara fadin meya faru da imran kalid plz karka sa zuciya ta buga dan Allah meya sabe shi ka fada min tana magana hawaye na kokarin xubowa daga idanun ta







Kara sautin kukan yayi yana fadin bashi da lpy sunan ki kawai yake kira dan Allah kizo idan bai ganki ba zai iya mutuwa plz Ki taimaki abokina safna dan Allah






Kuka nehh ya kwace mata ta fara fadin kuna ina yanzu dan Allah kuna wani asibiti nehh kalid








Kalid yace muna gidana dake badawa layout kina shigowa layin Gida na uku shine mai milk din gate







Da gudu ta shiga daki ta na fadin ganinan zuwa yanzu wayar ta kashe ta wullata kan gadon da jamsy take kwance saura kadan ta dira a fuskar ta mukulli ta dauka ta ja wani mayafi tayi waje da gudu ko takalmi bata daukaba






Mai gadi na ganin ta yayi saurin bude kofa tun kan tazo tana shiga motar ta fige ta da gudun tsiya kamar zata tashi sama Allah nehh kawai ya kai ta lpy amma ko gaban ta bata gani sosae tana zuwa taji Horn mai gadin ya bude mata dan Dama kalid ya fada masa zuwan ta kuma yace tana shigowa ya rufe ko inada ina nan gidan aiko tana shiga ya cika umarni






Tana tsayawa ta kashe motar bata tsaya cire keyy ba ta fito kai tsaye ciki ta nufa idan ta ja zubar da hawaye






Kalid najin knocking ya taso ya bude yana bude wa ta shige cki kawai tana kwallawa imran kira ko ta kalid batayi yana ganin ta shiga ya sawa kofar key ya tare da zare shi ya sa a aljihunsa kawai ya tsaya yana kallon ta.............






WANNAN KENAN AFUWAN AFUWAN AFUWAN INA FATAN XAKUMIN DAN DAMA NA NEMI AFUWAR KU TUN A BAYA KUSANI KO KADAN TYPING BAYA WAHALAR DANI SOSAE KAWAI DAI WANI LOKACIN NEHH BA TIME SOSAE DAN HAKA NAKE MUKU 2 PAGE A RANA DAYA RANAN DA KUKA SAMU 1 PAGE KUMA INA BAKU HKR JIYA MA BANA NAN SHIYISA BAN YI TYPING BA NGD







plx shared

SANADIN MATAR UBAWhere stories live. Discover now