EL-BASHEER 29-30

536 41 1
                                    

EL-BASHEER*

Na
Nuceeyluv😘

*I'm so sorry my fans nasan kunsha jirana dukda nace amin uzuri amman nasan kauna ce tasa still anamin mgn prvt naci gaba, to ga el-bash ya dawo zamu ci gaba da gashi...*🔥🔥

_WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA CE GA DUK WANI ME BIBIYAR EL-BASH_

29-30

Har cikin gidan aka shiga da motocin abinka da taron mata sai ihu ake ana guda, nan dai aka kamo hannu ummi akayi bangaren El-bash da ita.
   El-bash tunda ya dawo ya cire manyan kayan dake jikinsa ya sauya kanana kamar kullum, zama yyi ya harde kafa daya kan daya ransa a matukar bace sai lankwasa yatsun hannun sa yake, tun kafin yabar gidan ransa yake bace har kawo yanzu Yana a wannan yanayin aka kawo amarya.
    Masu kawo amarya sai gulma ake ana yau za'a ga mijin ummi mahaukaci, jamila ce kan gaba wajen bude kofar parlon ta tsoma kafarta ciki, wanda suka rike amarya na biye, kafin ummi tasa kafarta ciki saida tayi bismillah, sannan sauran en baya aka shigo yuuuu...., jamila da tayo gaba tayi turus ganin mutum a zaune fuska a daure, sauran ma da suka shigo tsaye sukai, jamila tayi matukar girgiza da ganin el-bash da tayi, ba haka taso ganin sa ba, kai anya wannan handsome guy din shine El-basheer mijin ummi? Wata kawar jamilan ce da suka shigo daga baya tace, "yadai jamcy kinyi shiru ko bakiga mahaukacin bane?" Jamila tayi saurin wayancewa ta kwashewa da dariyar yake tace,      
     "kedai bari sailuba ai ban zaci haukar takai haka ba, wannan irin kasumba kamar an shuka ciyawa,"
  nan sauran jama'ar aka kwashe d dariya, ummi dai wani qululun takaici ne ya kulle mata a qirji, wai ace mijin da take aure yau shi aka zagaye ana kallo kamar wani sabon halitta?
   Basu dade ba suka fara tafiya dan raka jamila, jamila dai har suka bar gidan tana juya abin a ranta, sai kullawa take tana kwancewa, babban tashin hankalin ta ma shine yadda taga ana barin gidan aka koma yaba kyau da tsari irin na halittar el-bash.

    Kowa anan ya barta a tsaye sanye da lullubi tana kallon kasa, ko sanin fuskar wanda aka daura matan ma batayi ba,  
   ganin sun watse yasa ta zauna nan tsakiyar parlon tana jiran ikon Allah dan batasan mezai faru ba nxt, kanta ta kifa tana ci gaba da share kwallar da taki tsaya mata tuntuni,
    Oga el-bash kuwa yadda aka shigo aka same shi, haka aka tafi aka barshi dan babu abinda ya canja baya ga rashin annurin sa daya karu.

Kwas...kwas...kwas...ummi dake zaune ta fara jin takun takalmi, kirjin tane ya bada wani dam...kafin tayi wani tunani taji anja wani wawan tsaki, Sakina ce ta shigo tana tauna chewing gum, kafin ta fisge gyalen ummi, ummi tayi saurin dukar da kanta sakina ta sake jan tsaki a karo na biyu tace,
    "ke dan ubanki warning nazo na miki tun wuri dan haka ki bude kunnen ki kiji, wasu zafafan hawaye ne suka sake wanke fuskar ummi yau ga ubanta dake kabari an zagesa batare da tayi lefin komai ba,
    sakina taci gaba tace, "kina mgn ne da Sakina matar da el-bash zai aura idan ya samu lpy, tun wuri kiji dawai ban yadda ki bada kai ga mahaukacin nan ba, dukda nasan zai tsaremin kansa amma ki sake kula, kada maitar ki ta tashi kiyi masa fyade....
  
_Yah Subhanallah_

ummi ta furta jikinta na rawa sai a lkcin ta bude ido tana kallon sakina, bakinta narawa tace, "ni wlh anti ko yanzu ma kikeso ki gaya masa ya sakeni banason wannan zaman ki taimaka."
   Sakina ta tabe  tana murmushin gefen baki na mugunta ta kalli el-bash dake bayan ummi dake ta juya masa baya, tsurawa pink lips dinsa  ido tayi tana lashe baki ta lumshe ido kafin ta dawo da kallon ta kan ummi data sunkuyar dakai kasa tace,    
    "matukar kika kiyaye sharuda na zaki samu sakin ki a hannu yana samun lpy dan ba irinki yake da burin aure ba," 
  ummi ta girgiza kai tana share hawaye, Sakina ta mike tsaye tana tauna chewing gum tace,

"Good."

Sake kallon el-bash tayi taga yanzu ita yake kallo sabanin da dayake kallon wani directon wani irin durar ruwa cikin ta yyi ganin yadda fuskar sa take a matukar hade, ko second bata kara ba tabar parlon da sauri.
   da ummi zata lura da ita tabbas data hango tsantsar rikicewa da rudewar da tayi.  jawo gyalenta kawai tayi ta lulluba.

Ba'afi minti biyar ba sai ga haj suwaiba ta shigo parlon ita d wasu frnds dinta, ummi najin su batace komai ba, wata kawar haj ana ce da ita sahaba tace, "hajjaju masu surukai," haj suwaiba ta yatsina fuska tana zama kan daya daga cikin kujerun paron tace,   
   "sahaba kenan ina kika taba jin aure da mahaukaci? Ai wanda ya aureshin ma shima tababben ne," sauran suka sa shewa wata tace, "kinsan aikin masu gidan rana yanzu sai ya maidaka marar hankali," 
   haj ta dan ja tsaki tana kallon ummi da kanta ke duke kasa tace,

   "ke baki iya gaida manyan ki bane?" Ummi da tun dazu qirjin ta ke dukan uku2 bakinta na rawa tace,
  "ina yinin ku,"

"mwtsss"

haj taja tsaki tace, "Alhj ma dasa kai wahala yake ko mene amfanin wannan auren oho,"
  tayi mgnr tana juyawa direction din da el-bash yake, yanzu kuma kansa duke yake yana matsa hannun sa, juyo da kallon ta kan ummi tayi tace,
   "yadda makwadaitan  iyayen ki suka ji suka gani wajen baki mahaukaci haka kema zaki ji ki gani, a tsarina banason mutum me sa'ido, banason mutum ya shiga sabgata idan ban sashi ba, banason gulma duk abinda kika gani a gidan nan kiyi kamar baki gani ba, kazalika duk abinda kikaji a gidan nan kiyi kamar baki ji ba,, matukar kika kiyaye wa'annan zaki zauna lpy dani, kiji da mahaukacin mijin ki kawai dan dama dan shi kikazo ina fata kin gane?"

   Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci ummi, ita kuma wacce irin kaddara ce take neman nufota kuma? Bayan wacce take ciki ta auren mahauka...,

"kinyi shiru"

haj ta katse ta, da sauri ummi ta shiga girgiza kanta tace, "toh haj Insha Allah zan kiyaye" nan haj ta mike tana fadin "dadai yafi" sauran frnds dinta uku suka bi bayanta nan suka bar part din.

Suna fita ummi ta dafe kanta a fili tace,   
"Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un" na shiga next level.... Taku again taji ana nufo kofar ta, abin fa ya daina bata mamaki ya koma bata tsoro toh kuma waye zai shigo? Dama haka auren yake? Kodai dan ta auri mahaukacin ne?....bata ida tunanin ba taji anyi sallama.

EL-BASHEERWhere stories live. Discover now