EL-BASHEER*
Na
Nuceeyluv😘64
"Matsoraciya" El-bash ya furta yana dariya, "eh naji" ummi tace tana murguda masa baki.
****
Bayan duba su haj suwaiba an cire musu bullet har anyi dressing wajen, yyinda sakina kuma ta samu rabon ciki inda hankalin ta ya tashi matuka, cikin tashin hankali haj suwaiba ta kama sakina tana fadin,
"wanne dan iskan ne ya dirka miki ciki?"
Ba wni alamar tsoro a ranta tace,
"Rabe"
"Whatttt....?"
Haj suwaiba ta fada tana dafa kai,
"yau na shiga uku na lalace ya akai duniya take neman juyamin baya ne?"
Haj suwaiba ta fada cikin kuka tan me dora hannu akai,
"mlm ki mana shiru"
wani ya leko ya musu mgn sbd ihun da take, ana haka ma sai gasu El-bash, sawa akai aka fito dasu, duk kunya da dana sani ya lullube su, haj suwaiba basu sake shiga rudani ba saida suka ga Ummah tsaye gabansu, a gigice ta kamo sakina ta boye bayanta, ita kuwa sakina jikinta ne ya fara bari tunda ita a matsayin ta mutu ta sani, Rabe kuwa kasa tsayuwa yyi ji yake kamar a tsaga kasa ya shige haka yakeji musamman daya ga har Abba a wajen, Da murmushi umma ta karasa gabansu tace,
"toh ya kukaga ikon Allah? Kun dauka na mutu ko? Koda yake baku manta wannan ba ta nuna ummi dake gefen El-bash, Lkcn da kukai watsi dani Allah ya turo min su, dake Allah shi yake hukuncin sa harta zauna tsawon lkci tare daku baku san tanada masaniya da mummunan nufin ku ba, hmm.." Ummah ta tabe baki,
"Suwaiba da Rabe kenan a har kullum ku dinga tunawa hassada ga mai rabo taki ce"
tayi mgnr tana murmushi ta koma gefe,
Abba ya matso yace,
"suwaiba tun bayan barina kasar nan na tsinke igiyoyin aurena dake, koda can banyi ra'ayin auren ki ba Qaddara ce ta shigo ciki, dan haka indai duniyace yanzu kika fara ganin yadda take juya miki baya, kai kuma Rabe hmm....."
Abba ya sauke ajiyar zuciya ransa na zafi, Dama akwaishi da zuciya amma tun a gida ummah ta tause shi, Kwafa yyi dan ji yake kamar yyi kwallo dashi, can yace,
"irinku kune masu sarewa mutum gwiwa akan taimako, kanaso ka taimaka amma sbd gurbatattu irinku wasu keqin yi, Rana dubu ta barawo, Rana daya tak tamai kaya Sbd Allah nayi maka sannan a dalilinka bazan daina taimako ba, kai kuma abinda kamin na barka da Allah wanda ya tsareni daga sharrin ku."
Yyi mgnr ransa na baci, zai juyo kenan yaji an dafa masa kafa cikin yanayi na nadama, Rabe yace,
"na rokeka da girman Allah ku yafemin karka barni da Allah, wlh iya lefin dana aikata ma na daukar hakkin wasu da wanda basuji ba basu gani ba na cutar dasu na kashe rai dayawa na lalata farincikin wasu shi kadai ma masifa ne a gareni bare yanzu kacemin baka yafe ba ai na shiga uku, dan Allah ka tausayamin Alhj ku yafemin Dan Allah"
yyi mgnr yana kallon su daya bayan daya. Su kansu su haj suwaiba dukawa sukai suna neman gafara.Kusan few seconds Ba wanda yace komai, can Abba yace,
"Allah ya yafe mana gaba1"
yana gama fadin haka ya fice, Zuciya me rauni ummah kanta girgiza kai kawai tayi ta tafi, sai ya rage suraj, El-bash da ummi, ummi ta kalli El-bash da fuskar sa take a hade tun dazu tayi sa'a kuwa sun hada ido, ta kama hannun sa ta matsa a hankali kafin tayi masa signal da ido tanaso taji shima ya yafe, ita yake kallo gefen zuciyar sa na sanyi yyinda dayan side dinta ke zafi idan ya tuna abinda sukai masa, Sake matsa hannun sa tayi da dan karfi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, kallon su sakina yyi ta zuba musu ido kuwa kamar ta cinye su hardai data ga sunyi kyau kuma sun dace da juna, sake hade fuska yyi kafin ya girgiza kai shima, be bata lkci ba yaja ummi suka fice.
Suraj ya matso wajen su suma, ya kira sauran jami'an yace a hade su da sauran members irinsu Mudi, Dama su kadai aka kira tunda abin na family ne sauran kuma na hukuma. Haka aka tisa keyar su zuwa wajen, haj suwaiba da sakina na kukan nadama.~~~~~~
Direct kotu aka wuce dasu inda koti tayi zaman farko dasu tun daga wajen aka samu kwararrun shaidu babu bata lkci Alkali Ya fara karanto hukuncin su.
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...