EL-BASHEER 45

622 46 0
                                    

EL-BASHEER*



*_Shimfidar fuska ta wuce ta tabarma tallafamana kar so ya samu yin kuka 🎤Idan gamu gaki sae muji muna farin ciki yake nusy love ki taemakemu.🎤🎼🎼🎼🎼ga Yan group suna bidanki🎤silar bash muke kiranki😘😁😁_*

_Wannan page din naki ne Qawata Amintako😛me waqa🤣🤣🤣 dake da sauran en group EL_BASEER FANS masu amshi da rawa😂wanga abu ai dole na garzaya da gudu🏃🏼‍♀na muku typing sbd ya burga ni😍 inayin ku irin sosai sosai dinnan😘_

Na
Nuceeyluv😘

45

Dakinta haj ta koma hankali tashe ta dauki wayarta sam bata damu d cewa dare ne ba ta danna kiran sale dake bcci ya daga kiran yace,

"yaya da fatan ya sheka koh?" Wani wawan tsaki haj taja tace,
       "sale wa'anne irin sakarkarun yara ka turo?"
Sale ya mike zaune yace,
"dur***n uwa su babawo ne sakarkaru?"

"Toh idan ba sakarkaru ba dolaye kke so nace?"

Haj ta katse shi cikin takaici, sale yace, "bur*** uba wai me kike nufi ne?"

Cike da tsantsar takaici haj ta sanar masa abinda ya faru, mikewa sale yyi tsaye ya malmalo ashar

"kut***r ubannan kayyasa billahillazi bamu ga ta zama ba duk yadda za'ai kiyo asubanci muje gun boka dan tsito a rufe mana bakinsu karsu ambaci sunan mu dan ban shirya mutuwa yanzu ba."

Wata nannauyar ajiyar zuciya haj ta sauke sai yanzu taji fiye da rabin tashin hankalin ta ya ragu, cikin sauri tace,

"ka saurari zuwana" tana gama fadin haka ta kashe wayar.

****
Koda ya koma daki canja kaya yyi zuwa na bcci, cikin lallausan bargon sa ya shige ya jawo pillow ya kifa kansa a kai, ji yyi kamshin pillow ya canja, take Al'amarin daya kasance dashi dazu ya dawo masa, anya shine kuwa? Wai meya hau kansa dazu ne daga kallon yarinya duk ya rikice? Duk shige da ficen na kasashe daban2 dayake akan makamar aiki ga mata nan iri2 be taba rikicewa a kansu ba sai wannan little babyn?

Why only her? Sake rungume pillow yyi yana feeling kamar itace a wajen kamshinta data bari a wajen yake sake sashi hangota lkcn da take ta mutsiniya tana neman tsira, zumbur ya mike daga kan gadon ji yyi jikinsa kamar yana shirin komawa gidan jiya mmki yake dama shidin har haka yake da feeling ko kuwa dan haduwa da ita ne? Yes yanajin feelings time to time dan shidin lafiyayyen namiji ne saidai ba kamar irin yadda yakeji yanzu ba.

   Hanyar toilet yyi nan ya dauro Alwala dan ya lura idan ya kwanta tunani ne zai cika masa Brain maimakon yyi bcci, nan ya tada kabbarar sallah, dake har hudu tayi asuba ta kawo jiki anan yyi sallar asubar sa, bayan ya idar ya haye gadonsa wani irin nannauyan bcci yyi awon gaba dashi.

~~~~
Ko takan Abba haj batayi ba ta fice a gidan, tana zuwa dama sale a shirye yake nan suka tafi a motar haj, dake asuba ne akwai sauran duhu haka haj tayi ta tsala gudu har suka gangara wani daji dake gaba da kano kadan, a gefen hanya ta aje motar suka fito da hanzarin su, dama tunda suka hadu babu mewa kowa mgn har sukaje.

  Can sukaje wata er bukka dake kwaya daya jal a dajin, zuwansu keda wuya sukaji dajin an kaure da dariya meban tsoro saidai ga mmki su haj ko a jikinsu da alama dai sun saba d zuwa wajen. Wani dan siririn baqin tsojo ne ya fito hakwaren sa jajaye zaqo2 shima yana dariyar, can kuma sai dariyar ta dauke ya tsuke fuska yana muzurai da wani mitsitsin idanun sa, daidai lkcin su haj sun zauna gabansa kenan sale yace,

    "An gaishe da boka dan tsito duk wani boka meji da kansa a bayanka yake sha yanzu mgnin yanzu, dama wata buqa......."

"Na sani"

boka dan tsito ya katse sale yana daga masa hannu wato ya dakata, sannan yace,

"Badai a rufe musu baki ba?"

Haj bakinta na rawa tace,

"Eh tabbas hakane"

wata irin dariya ya kwashe da ita kafin ya gimtse yace,

"An gama."

Farinciki ya lullube haj ta zuge jaka nan ta dire masa rafar kudi bugun abuja, boka dan tsito yace,

"kunsha da kukazo da wuri yanzu kuwa duk tmbyr da za'ayi musu bazasu taba fadar sunan ku ba"

da murna suka hau godiya yace, su tashi su tafi.

A guje kuwa haj suka iso cikin gari sbd sharara gudun da take, sauke sale tayi tace zasuyi mgn idan sun natsu, sannan ta karaso gida lkcn gari be gama haske ba gidan shiru kowa ya koma bcci, hamdala tayi da taga komai ya taf successfully,

cikin sanda tayi wuf ta fada dakinta, gyalenta ta jefar batare da canja kaya ba ta zube kan gadon ta nan bccin da batayi ba yyi awon gaba da ita.

*******
Dake komai an aje musu a kitchen yasa ummi tana gama gyara dakinta tayo waje, leka dakinsa tayi taga yanata bcci, zuba masa ido tayi a ranta tace kamar a tashe shi ya amsa yadda taga yana bccinsa hankali kwance, batasan meyasa takejin tausayin sa ba all the time musamman idan tana kallon sa, saje da gemun daya cika masa fuska take kallo duk yyi yawa gashin yana buqatar gyara, sa hannu tayi tadan shafo afili tace,

   "Bari na gama aiki nazo na aske gemun nan kamar ciyawa kuma duk rigimar da zakai saidai kayi saina aske"

tayi mgnr still hannun ta nakan gemun tana shafawa, saida ta gama jagwalgwala gemun ta fito tana ja masa kofa tunda taga bcci yake.

Oh! rashin sani akace yafi dare duhu domin tun lkcn data shigo yasan da zuwanta kawai likimo yyi yana jiran yaji me zatayi, shi abin nata ma ya daina bashi mmki saima dariya lalle yarinta me dadi wai shi za'aima aski? Lalle wannan little din akwai karfin zuciya, zaiga kuwa ta inda za'a masa gyaran fuska. Nan ya sake nadewa a gadon yana jiran tsammani.

EL-BASHEERWhere stories live. Discover now