EL-BASHEER*
Na
Nuceeyluv😘44
Wata irin dariyar basawa 'yan fashin suka bushe da ita suna tafa hannu, daya daga cikin su yyi mgn cikin muryar tatattun 'yan daban nan yace, "kai ka rike salatin ka watakila zai maka amfani zuwa an jima kadan"
"Subhanallah"
Abba ya furta yana fadin "kudi ya kawo ku ko me kuke nema?" .
Babban cikinsu yace,
"Ashe tsohon kansa na ja, saidai ba kudi ne ya kawo mu ba ranka zamuyi awun gaba dashi" yyi mgnr yana saita bindiga a kirjin Abba,
Abba cikin karfin hali yace,
" 'yan samari kenan banda abinku wake daukar ran mutum idan ba Allah ba? Saidai ko ya zama sanadi, mutuwa koyaushe na riskar mutum yanzu ko anjima so koda na mutu a yanzumutuwa ba kune kuka sa na mutu ba illa kaddarar mutuwa tane a sanadin ku wanda hakan baya faruwa sai Allah yaso...."
"Dallah yi mana shiru"ogan nasu ya dakama Abba tsawa yana kokarin danna harbi dan still bindigar na kirjin Abba,
Daidai lkcn haj suwaiba ta farka dama ba bcci take ba, a razane haj tace,
"yau mun shiga uku mun lalace mezan gani da mugun ganin Alkaba'i Alhji?"
Tayi mgnr tana dora hannu a kai, ran Abba be tashi baci ba saida yaji furucin haj, a hasale yace,
"ke wacce irin mutum ce daga tashi ba salati ki dinga fadin an shiga uku?"
"Alhji sbd Allah kashe ka fa naga ana shirin yi? Wayyo jama'a taimako, yau ga ranar mahaukacin danka be isa yazo ceton ka ba sbd yana hauka ta karasa mgnr tana matse hawayen karya, dan mgn take me kama da gugar zana farincikin ta yau za'a kawo karshen komai ta huta.
Rintse ido Abba yyi sannan ya bude ya kalli samarin yace,
"what are u waiting for? I said what are u waiting for??? Ku harba manaa...." Yyi mgnr da karfi,
ogan ciki yace,
"kut***mar uba tsawa kke min?"
Ya daga bindigar zuwa goshin Abba yace, gwara na tarwatsa maka kwakwalwa mekan kifi, ji kke tassss.........,"
haj suwaiba dake kan gado saida ta diro kasa a matukar tsorace, dakin yyi shiru na wasu 'yan dakikai, ga Alhji a gefe guda.
Cikin taku irin na kwararrun jami'i yake yi a tsakiyar su fuskar sa ya rufe da facemask yyinda ya sake sa bakin glass ya toshe idonsa, yanda ya rufe jikinsa gaba1 da wuya ka gane shi, *EL-BASHEER* kenan gaba1 sun zagaye 'yan fashin sai ga 'yan fashi sun zube a kasa yyinda jami'ai suka zagaye suka zagaye su el-bash a tsakiyar su, kallon idon su yyi yaga sunyi wuqi-wuqi girgiza kai yyi yana mejin bakin cikin yadda samari matasa ke lalata rayuwar su a wannan zamani musamman a kasar nan tamu ta naija, komai sake tabarbarewa yake,
Haj bakinta na rawa tace,"suwaye ku dan Allah?"
Babu wanda yyi mgn a cikinsu suna jiran umarnin ogane kawai, El-bash ya kalli abokan aikinsa da suka sha facemask yyi masu alama da hannu, wani anace dashi musa yace,
"haj da zakiyi shiru tabbas da hakan zaifi maki Alkhairi,"
haj da bakin ciki ya isheta sbd ba'a kashe Alhji ba tace,
"Ai dole nayi mgn tunda anzo cecen mijina da ace tun wuri an harbeshi basu tsaya shirita ba da tuni ya sheka ai"
tayi mgnr tana matse hawayen bakin ciki saidai wannan bakin cikin na takaici ne, a yanayin mgnrta me hankali ne kawai Zai fahimci da biyu tayi mgnr,
Wato tana mgn ne da harshen damo,dan murmushi el-bash yyi me ciwo tsaf ya fahimci inda ta dosa wato tanaso tace meyasa 'yan fashin basu kashe abbansa da wuri ba suka tsaya shiririta har aka kamasu?
Girgiza kai yyi yama suraj alamar a fitar da samarin waje, dama duk an damqe su nan aka tisa keyarsu gaba.
Shi suka bari karshe, yana cikin dakin hannayen sa a Aljihu ya kalli side din Abba, wato ya juyawa haj baya kenan, cire glass dinsa yyi yadan zamo da mask din murmushi ya sakar ma Abba yana me daga masa hannu ya sake maidawa ya rufe sannan ya maida hannayen sa Aljihu ya fice cikin takunsa na isa.
Tsabar mmki ma kasa motsi Abba yyi, shi kadai yagan shi anya dansa ne *EL-BASHEER?* kodai mafarki yake? Tabdin wato akwai sarkakiya a wannan Al'amarin baida masaniya, to yana nufin ba mahaukaci bane ko me?
Sbd mmki ma kasa mgn yyi dan kansa ya kulle matuka. haj ce ta matso kusa dashi tace,
"meya maka daya juyamin baya? Ko ka sanshi ne? Koshi ya sanka?"
Sauke ajiyar zuciya Abba yyi daya fahimci bata gane waye ba dan tunda yaga wannan sarkakiyan yasan akwai wani boyayyen Al'amari wanda el-bash yasan shi...
"mgn nake kamin shiru. Alhji...."
"ke dallah rufamin baki" Abba ya fada cikin fada-fada.
Haj ta tsorata matuka, gefe ta samu ta zauna tana dafe kai hankalin ta a matukar tashe.
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...