EL-BASHEER*
Na
Nuceeyluv😘36-37
Sai around 9 ta farka da salati a bakin ta dan tun bayan da tayi sallar Asuba ta koma bcci, wanka tayi tasa atamfar ta riga da skirt da hijab dinta iya gwiwa ba wata kwalliya tayi ba ta fito, dakin dake kallon nata ta zubawa ido, tana kyautata zaton ko dakin mijin nata ne tunani take ta shiga taga halin da yake ciki ne ko ta tafi? Yi tayi kamar ta shiga sai kuma ta fasa ta wucewar ta, sakkowa kasa tayi, nan tayi tsaye ta rike qugu tana karewa parlon gidan kallo, parlon dai babu datti amma yana bukatar mopping sbd kura yo dama yaushe zaiga gyara mutumin ciki ba hankali ne dashi ba? Taji wata zuciyar tana fada mata, hanyar wani corridor tayi taga wata kofa tana budewa taga ashe kitchen ne, ganinsa tayi shima ya hada kura sosai saidai inda aka jera plate a wanke suke, banda wajen ko'ina kurace dashi, dafe kanta tayi tana hango toh inaga dakinsa kuma? Uwa uba toilet? Ya tsaftar wajen zata kasance? "Oh Allah! Ummi ta furta tana rolling eyes dinta, tana tunanin akwai babban aiki a gabanta, fitowa tayi ta danyi gaba da tafiya a corridor din nan ta hango wani fili a gabanta, a ranta tace so gidan haka yake da fadi? Garden ta gani a gabanta tsuntsaye sai shawagi suke, garden din ba wani girma ne dashi ba dan karami ne sadai zaka shaki ni'ima awajen sbd sanyi me dadi da iska ke kadawa, inda aka aje kayan mopping da shara ta gani, abinda take nema kenan, dan haka ta kwaso dawowa parlo tayi ta fara sabuwar shara duk kujerun kifesu tayi ta fara sharo duk wani lungu da sako na parlo,Cikin few minutes ta share ko'ina har kitchen dama ba wata shara ce ssai ba be wuce en ladodu ko paper, dawowa tayi tahau mopping tadan jima kafin ta gama kitchen ta koma nan ma tayi, tana bakin corridor dazai fitar ka waje ta kofar baya ta dafe bayanta tana fadin "washh," gsky ta gaji ainun mopping dacin rai yake, dukda itace me aikin duk gidansu bata taba yin irin mopping din yau ba, toh inama zatayi tsakar gidansu iya simintine rabi kuma kasa? Dakyar ta sake dukawa ta kwashi kayan aikin tayi gba, can ta zubar d komi ta dauraye kayan da tayi amfani dsu dake akwai tap a wajen, inda ta dauka ta mayar, hijab dinta data nade ta wareshi ya koma yadda yake, dan zagawa garden din take tana kara kallon wajen dan so take inda tayi mopping ya bushe dukda ta sakarma wajen fanka ta bude Windows dan ya bushe da wuri, kusan 10mins tana wajen, ta tashi tadawo parlo, ya bushe din kuwa, nan ta rufe windows ta sakar da labule sannan ta rage gudun fanka kujerun data kife ta dawo dasu daidai, daga gefen inda aka aje TV taga freshener ta dauko tahau fesawa lungu da sako, saiga parlon yadau kamshi, zama tayi kan kujera tana lumshe ido kai gsky a rayuwa tana son tsafta da kamshi, bude idonta tayi ta zubawa ko'ina na parlon ido hatta Plasma ma sheki yake sbd yasha mopping, komai dai kyalli yake, duban agogon parlor tayi taga har 10 yanzu, a ranta tace ko ya tashi? Bata ida tunanin ba taji taku daga stairs,
wani irin bugawa qirjinta yyi toh idan yana duka fa? Ya ilahi, ta furta jikinta na dan shaking.
***
Tunda ya tashi ya fada toilet yyi wanka, dama shi sai wajen 9:30 to 10 yake farkawa, harga Allah daya tashi ya manta ma da wata mace a gidan, saida yazo yana saka kayansa ya tuna da ita, dafe kansa yyi yanajin wani bacin rai na taso masa wannan shi ake kira a daki mutum a hanashi kuka ba damar mgn, cike da kasaita ya fara takowa daga sama dan ko kallon dakinta ma beyi bama yanzu zaton sa tana ciki, saidai tun kafin ya karasa parlon yaji wani baqon Al'amari ya zayarce shi, be ida mmkin ba saida ya karasa sakkowa, wannan changes daga ina? Yyiwa kansa tmbyr, ssai yyi mmkin ganinta a wajen a zaune dukda wa'annan tarin mmkin nasa sam babu alamar sa afuska, dan fuskar nan a daure take tamau kamar hadari a kasaitance yazo ya zauna a kujera ya dauke kallon sa daga kanta.
Sauke ajiyar zuciya tayi sai ynzu hankalin ta yadan kwanta, zaton ta tunda hauka yake yna ganinta zai iya dukan ta ko wani abin. Ji tayi ana knocking tashi tayi taje ta bude tana tsammanin ganin en gidan, sai taga sabanin haka, Suraj ne hannun sa dauke da basket, taji dadin ganinsa kwarai dan taga yafi kowa hankali a duk wanda sukazo mata jiya, ita mutanen gidan ma tsoro suke bata, da er fara'a ta karbi basket din tana gaishe shi, suraj shima da fara'a yace,
"Amaryarmu da kanki?"
dan murmushi tayi batace komi ba ta shigo da basket din ciki, suraj ya karaso yna fadin,
"Ashe ma tare kuke da angon na katse muku lkci,"
yyi mgnr yana kallon El-bash a sace, aiko ya samu tsarabar harara daya mako masa shima a sace. Er dariya suraj yyi yana kallon ummi data sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta yace,
"Amarya ni zan wuce office yanzu sauri nake ga breakfast nan kiyi sannan dan Allah ayi kokari a bashi shima yaci kinji."
ummi cike da kunya da tsoro tace,
"Toh."
suraj yamike yana kallon El-bash yace, "bye," El-bash kamar an hura mai wuta dan bacin rai, a ransa yace, _lallema suraj ka raina ni wannan jaririyar ce zata bani food? Mtwssss..._ Yaja tsaki kasa2 suraj har ya fita yana er dariya dan ya fahimci inda fushin frnd din nasa ya dosa.
Tsoron ummi ne ya karu tana tunanin ta ina zata fara bawa zabgegen saurayi abinci? Dagowa tayi ta kalleshi daidai lkcin shima ya juyo suka hada ido ya sake tsuke fuska sosai, yyinda hantar cikin ummi ta kada ssai sbd tsabar firgitar ganin yanayin sa.
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...