EL-BASHEER*
Na
Nuceeyluv😘*Wannan page din naku ne en grp dina EL-BASHEER FANS, na gode da kauna😘*
34-35
Ko kallan kofar d ummi take beyi ba ya shige dakinsa da yake bangaren dama, yana shiga ya fada toilet wanka yyi kafin ya fito, kulle dakinsa yyi kafin ya dauko system dinsa dake gefen gadon sa koyaushe, zama yyi kasa ya bude ta wasu danne-danne yyi saiga hoton su haj suwaiba ya bayyana, yana kallon duk abinda sukeyi kamar kullum, camera ya manna musu a parlo batare da sunsan da zaman ta ba, duk abinda ya faru yana ganin su, haj ce zaune da wa'annan frnds din nata d suka zo parlon sa dazu sai hira suke, wacce ake kira sahaba tace, "kuna sane da wannan meeting din ya matso nan da sati biyu?" Haj tace,
"ai Alhj Rabe ya fada min nima" dayar da ake kira ziyada tace,
"aini tunda babu oga kwata-kwata a wajen sai naji meeting din ya sane min," haj suwaiba tace,
"kefa matar nan akwai son maiko ya kike da Alhjin ki ne sanata bello?""Mtwss.."
ziyada taja tsaki
"toh me ake da wannan? Kullum aiki, meeting baida time din gida kina ganin bazan kosa ba nima na fito? Ai yadda yake neman yara mata ya huta to haka nima nake haduwa da Alhazai irinsu Alhji Mai kano.....," kifff taji an danqe bakinta, haj suwaiba jikinta na rawa
"tace baki da hankali ne ziyada?" Ziyada ta kwace bakinta tace,
"da nayi me fa?" Sahaba ta karbe zancen da fadin
"Komai ma kinyi kina nema kiyi mana barota banda hauka waya fada miki ana fadar sunan oga a ko'ina?" Haj suwaiba tce,
"sbd Allah fa tayani bata amsa." Ziyada ta dafe kanta kafin tace, "banda abinku waye na cikon hudun nan da kuke jin tsoron kar yji? Inace mu uku ne a parlon?" Haj suwaiba tace,
"a'a tsautsayi da bacin rana ake gudu,"
"mtwss" ziyada taja tsaki tana saba gyalenta a kafada tace,
"kunga nayi nan tunda ku a tsorace kuke," haj sahaba tace, "daga fadar gsky," haj ziyada tace,
"gwara na tafin kawai" nan ta musu sallama.Tana fita haj suwaiba tace, "aikin bnza kome oga zaiyi da ita? Da fuska kamar tawa a wajen," haj sahaba ta kwashe da dariya tace,
"bakida krki fa," haj suwaiba tace, "yo ai itace da abin haushi ai irin wanda oga yake so sune yara emmata matasa masu jini a jika, ba irinta ba data bushe arziki ya boye tsufan ta,"
dariya sahaba tayi tace, "wahala ce bata isheta ba. Nan suka koma wata hirar.~~~~
"Next level," El-bash ya furta yana kokarin rufe system din yanzu yasan zasuyi meeting, saidai ba ogansu, toh amma waye Alhji Mai kano? Wannan ai ba suna bane ya fada yana dafe kansa, wayarsa dake kasan pillow ya jawo kiran suraj yyi, suraj dake shirin bcci ya daga yace, "kai ango lpy?""Mtwsss" el-bash yaja tsaki "kaifa dan iskane wani lkcin k manta aikin dake gabanmu ne?" Suraj yyi dariya "afuwan oga ashe zancen na aiki ne, inajin ka akwai wani improvement ne?"
El-bash ya sanar masa duk abinda yaji, suraj ya numfasa yace,
"tabdin, wannan mutumin ya boye asalin sunan sa ne, amma hakan ma an samu ci gaba zamuyi kokari mu binciko waye mai kano?"
El-bash yace, "hakan yyi,"Suraj yace, "toh mezai hana mu kama su a wannan meeting din da zasuyi?" El-bash yace,
"kana manta yanayin aikin ka, kana tunanin idan mun kama yaransa zai fito ne? Saima ai ya sake boye kansa sannan ya dasa wasu sabbin en qungiya, kuma kaga wanda muka sani en kungiyar sune target dinmu a wajensu dole zamuji komai,"
Suraj yace, "hakane, amma idan abin zai jamu dayawa zamu fara musu damqi dai-dai."
El-bash yace, "wannan ma point ne." nan sukayi sallama.
Bayan sunyi sallama El-bash ya jawo abincin sa yaci,bayan ya gama ya wanko bakinsa yazo ya haye gado, saida ya lumshe ido ya tuno ashe fa yau ango yake? Wni takaici ne ya kama shi badan Abba b gsky bazai yadda ba, a rasa wacce za'a bashi sai jaririya? Kai da gani ma raino aka bashi, mtwss yaja tsaki a fili yace, "ranar da zan gama wnnan aikn ranar zan datse aurena da ita dan bazan yadda na takura ba gwara na samo type dina," haka dai yyita sake-sake karshe dai yyi Addu'a bcci ya sace shi.
****
Amarya ummi, tunda ta shiga dakin ta tsaya kallon yanayin sa, dakin dai gashin nan dai, akwai gado sai wardrobe da mirror ko kan mirror babu irin jeren nan na kayan kwalliya, akwatinan da aka kawo mata ma gasunan a gefe, abin dai gashi nan dai kamar ba dakin amarya ba, ummi dai ta rasa me yake mata dadi a duniyar nan, lalle ta cika marar gata, toilet ta fada tayi wanka ta fito daure da towel tasan ma ba shigo mata za'ayi ba dan haka ta zauna ta shafa manta hankali kwance, akwatinan ta shiga budewa nan ta dauko rigar bccinta, ta saka, saida ta gama shirinta tsaff ta jawo ledar d aka bata dan wata iirin yunwa takeji rabonta da abinci tun safe shima bana kirki taci ba, tana budewa taga gasassiyar kaza da fresh milk, hankali kwance ta fara cin kazar ta, bayan ta gama ta aje sauran cikn fridge data gani a dakin, wanko bakinta tayi itama tazo ta kwanta, harta lumshe ido ta tuna angon nata fa ba hankali ne dashi ba, shin ko yaci abinci? Ko yana can ma kasa oho, to itafa har yanzu bata ga kalar fuskar sa ba, kuma itama batajin ya ganta, ko ya yake nema oho, taso tashi ta fito taga ko yaci wani abin tunda baida hankalin tmby taji wani nannauyan bcci ya kwashe ta sbd yadda ta tara bcci dayawa a kanta, dan tunda bikin y karato bata bcci cikakke koyaushe tana kuka tana salla tana neman zabin Allah gareta.Asuba ta gari Umm-El-bash😂
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...