EL-BASHEER*
*Ina masoya El-bash? Na lungu dana sako, WhatApp fans a Facebook? Ku matso kusa domin yau page din naku ne, Ga duk wanda yake bibiyar Novel dinnan har zuwa yanzu Sakon jinjina ne a gareku, EL-BASHEER na muku fatan Alkhairi a duk inda kuke🤙🏻*
Na
Nuceeyluv😘65
"Wow" ummi ta furta da murmushi, a saitin kunnen ta El-bash ya rada mata, "welcome to our new home" ya fada yana kashe mata ido daya hade da murmushi, "OMG!" Ummi ta furta tana me rungume El-bash cikin farinciki,
"love birds sai a bari mubar gidan ko"
suraj ya katse su Aysha na gefen sa tana murmushi dan sun birgeta hakama sauran frnds din su suraj, dariya aka sakar musu hakan yasa ummi taji kunya tana me sunne kanta kasa, El-bash ya harari suraj,
"Ka samin bby taji kunya dan sa ido kawai"
"daga fadar gsky" Aysha ta amshe,
"au bayansa kikebi koh?"
Suraj yace,
"kaga mlm magrib na matsowa muje a gudanar da komai"
nan suka isa cikin farfajiyar gidan da aka qawata ta, bayan gaishe2 nan akaci aka sha cikin murna a hankali kowa kuma ya watse tare da musu fatan zaman lpy nahar abada. Ssai kuwa ummi sun tsinci kansu a farinciki marar misaltuwa.Kallon yanayin parlon take kai abun ya birgeta da gani komai sabo ne a gidan, El-bash ne ya rungumo ta ta baya saitin kunnen ta yace,
"Ya kikaga tsarin wajen? Komai yyi daidai ko a canja?"
Juyowa ummi tayi tana kallon shi tace,
"duk wannan abubuwan nace a canja?" Ta fada da mmki dan ita har santin kayan parlon take sbd tsaruwa da kyau,
"Girman ki ne princess"
murmushin farinciki tayi ta rungume El-bash tana fadin,
"I love you Bae."
"Love you more baby"
El-bash ya fada yana cirata sama nan yyi hanyar stairs da ita.•••••••
Kafin wani lkci tuni an rushe gidan mlm sabo an tsantsara masa na gani na fada sai kace gidan Alhji, koda yake ya kusa zama Alhjin tunda wannan layyar suna sa ran dasu za'ayi haj bisa kyautar Abba, yyi godiya harya rasa abin cewa, sukam fadi suke duk abinda sukai masa basu biyashi ba, Wani tafkeken shago El-bash ya budema Mlm sabo a kwari, shagon da ganin girman sa ya lodi dukiya me yawan gske, mlm sabo har hawayen farinciki yyi su kansu su inna abin ba'ace komai rayuwa ta canja sai sam barka sai matsala daya haryau babu manemi gun jamila, hakan yasa ummi ta bada shawarar ta shiga makarantar yaki da jahilci kuma suka amince harma da islamiyya ta hada.****
Gidan Abba yasha gyara sosai ya zamana ummah ce kadai a gidan sai sabbin ma'aikatan gidan da aka kawo mata da sabon me gadin su, tsuhuwar soyayyar su suke rakashewa da Abba abinsu cakwai.~~~
Fitowar su wanka kenan, El-bash ya jawo cream yana fadin,
"yau dai nine first tsaya na shafa miki" ummi tana dariya,
"kai Bae Allah wayo kkemin"
"Dgske Baby"
ya fada yana shafa mata a fuska, Da sauri ummi ta ture hannun sa tana toshe hanci,
"meya faru?"
Ya fada yana binta da kallo, wani abin ta jawo tana goge cream din daya shafa mata da sauri2 a hanzarce ta mike zata tashi El-bash ya kamo hannun ta yace,
"wai menene?" Cream din hannun sa ta nuna masa tace,
"wari"
"wari kuma?" El-bash ya furta da mmki, yasan ba cream din da takeson kamshin sa kamar shi, daidai hancin ta yakai cream din yace,
"Shinshina kiji fa" yyi mgnr yana kai mata dab da hanci, Ummi ji tayi cikin ta ya wani irin juyawa cikin azama ta hankadar da cream din gefe ta kwace daga hannun El-bash, ta nufi toilet, biyota yyi da sauri daidai lkcn yaga tana ta kwarara Amai, hankali tashe yace,
"baby anya lpyrki kuwa?"
Ya fada yana wanke mata baki, saida ta dan samu nutsuwa ta kama kanta tace,
"kaina kemin ciwo kawai fa, ba wani abu bane sai cream dinnan da yakemin wari harya sani amai."
"No baby we need to see Doctor" El-bash ya fada yana kama hannun ta, kayanta ya sanya mata shima ya saka kafin ya dakko ta hade da key din mota suka fito,
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...