EL-BASHEER*
Na
Nuceeyluv😘43
Kamar yadda yace hakan kuwa tayi komai ta kwashe shi, sharp2 ta hada masa ruwan Lipton da lemon tsami, bayan ta zuba a cup ta saka sauran a flask ta dauka tayi sama dashi.
Batare da tayi knocking ba ta tura kofar, daidai lkcin el-bash yana zaune ne gefen gado kansa a duke ya rike kasan cikin sa, ummi mmki ne ya isheta ainun, wai meke damunsa haka? Ta tmbyi kanta, a hankali tà karasa wajen ta dan dafa kafadar sa ya dago kai yana kallon ta, ummi ta girgirza da ganin yadda manyan fararen idonsa suka canja kala zuwa ja kamar me fama da ciwon ido,
Lipton din hannunta ta mika masa sai taga ya karba ba musu, dukda yanada zafi amman haka taga yana kurba da sauri2 kamar ya samu abin dadi, tass ya shanye ta sake tsiyaya masa na flask taga ya sake karba wannan karon rabi yasha ya mika mata sauran,
yana gama sha ya koma kwanciyar sa yyi luff, yyinda ita kuma ummi ta fita da kayan taja masa kofar sa.*****
"Sale kyi wani abu akan wannan lamarin Alhaji fa musu ya fara min," cewar haj suwaiba.
Sale yaja tsaki "yanzu so kke yaci gaba da rayuwa ko a kashe shi?"
Haj suwaiba tace,
"zamansa baida amfani a aikashi lahira kawai."
Wata mahaukaciyar dariya sale ya saki yana tafa hannu yace,
"yanzu kika shigo gari hajjaju makiratu, karki damu duk sanda zai fito ki sanar dani sbd mu zama cikin shiri ko cikin dare zamu duro mu kashe shi?"
Haj ta danyi shiru can tace, "kuzo cikin daren zaifi sauki kar a kashe shi da rana a sami matsala na shiga uku."
"Toh shikenan ni zan wuce"
haj tace, "madalla saina jiku,"
nan sale ya fito yana murna burinsa ya kusa cika.
*****
3am wato tsakiyar dare lkcne da kowa yake surnana bccin sa, yyn da wasu suke tsaye kan kafafun su suna ibada dan neman yaddar ubangi, Allah ya sanyamu cikin yardaddun bayinsa Ameeen.
Dake sale yasan takan gidan shiyasa abokan nasa 'yan fashi basu sha wahalar shigowa ba dan ya musu kwatancen komai, shi be biyosu ba sbd kar Al'amari ya baci Allura ta tono garma.
Basu tarar dame gadi ba a wajen sai basu wani damu ba suka shige.
Sidaf2 suke taku har suka gifta ta bangaren el-bash, yana jikin window yana kallon su daya bayan daya, yadda ma suke wani sanda ma sai abin yaso bashi dariya a fili yace,
"aikin banza ashe ma kananun kwari ne mtwssss."
Saida suka gama shigewa tsaff kafin el-bash yyi mgn wani dan karamin abu ne a kunnen sa yace,
"you guys are u ready?"
"Ever ready Sir!"
Yaji sun bashi amsa, facemask yasa ya sake rufe idonsa da glass ya fito.
****
Haj suwaiba tasan mezai faru bata cika kwana dakin Abba ba koda basu samu sabani ba, bare kuma ace an samu, koda taje da niyyar kwana Abba yyi mmki dan beyi zaton zuwanta ba yanzu tunda sun samu sabani, be kara mmki ba saida yaganta da kwalliya tana masa murmushi, Abba bece komai ba yana kallonta kawai, haj suwaiba ta sake fadada murmushin ta tace,"haba Abban Bashir kamar bakayi farincikin zuwana ba,"
Abba yace, "no bance ba" yyi mgnr adan dake dan be gama hucewa ba, haj suwaiba tace, "haba mana Alhaji na idan kan abinda ya faru ne dazu kayi hakuri kaji? Yanzu kam na gane gskyr ka kuma zan gyara ai bashir dana ne"ta karasar mgnr tana murmushi, Abba yadan murmusa kadan kawai beyi mgn ba, haj suwaiba tace, "dgske nake fa na gyara" Abba da er dariyar sa yace, "ya wuce amman nasihar da zan miki itace 'ya'ya da dukiya ba'a ketar su bakasan wa zaka mora ba koda bayan na mutu ne El-basheer ai abin ki kula dashi ne dukda ba yaro bane."
Haj tace, "kayi gsky Alhji za'a kiyaye" Abba yace, "Good for u" yana me gyara kwanciyar sa yace ta kashe wutar dakin bcci yakeji kuma da wuri zai fita gobe. Haj tace, "toh" tana me tashi ta kashe.
Dake cikin duhu ne sai doka masa harara take tana dariya kasa2 tace masu yaro kaida ganin mahaukacin danka ai sai a barzahu tasa dariya tana toshe baki.Tsakiyar daren sukaji an banko kofa lkcin ma Alhji yana kan sallaya salla yake, ya sallame kenan yaga mazaje a kansa,
"Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un Alhji ya furta yana karema samarin 'yan fashin kallo.
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...