EL-BASHEER*
*Afuwan fans, hakuri, a kara hakuri, ni nasan kunmin uzuri👏🏻*
_Mom Asas, sumy, mom maheer, billy chocolate, Amina maradun, hadiza, ummi apipa,_
Kunada yawa fa...😨 wannan page naku ne saura zamu hadu a next page Insha Allah.
*SONSO FISABILILLAH😘*
Na
Nuceeyluv😘57
Saida ta saisaita kanta kafin tace, "kikace me?"
"Abinda kunnen ki yaji momy"
haj suwaiba tace,
"ke kinada hankali kuwa? Uban me zakici da yaron nan kika nace masa haka?"
Sakina tace,
"sonsa nake burin aurensa nake, kuma haukan da yake ba kowa bane sila sai ke momy wlh kunmin buqulu da kuka haukatar dashi, kuma wlh idan ba'a.......," kauuuu.. taji an kwasheta da mari momy na huci kanta sbd takaici tace,
"ni zakiyiwa tijara sakina? Dan ubanki nawa kike? Ki rasa wanda zaki so sai yaron da nafi tsana a duniya? Kuma da kike mgnr hauka, d ban haukatar dashi din ba kin isa kikai lbri? Ko kuwa duk abinda nake dan wa nakeyi? Inada 'yar data wuce kine? Idan an samu yadda akeso waye zaifi jin dadin? Kul na sake jin bakin ki kan lamuran nan kona saba miki wlh."
"Yiiii...,"
Sakina ta fashe da kuka tace,
"ni wlh bakya sona momy inda kina sona zaki so abinda nakeso, harma wai ni za'a rainawa hankali a gidan nan? Gadara fa takemin dashi wlh bata isa ba dan El-bash nawa ne."
ta karasa mgnr tana kara fashewa da kuka. Haj suwaiba ta matsa jikin kujerar ta zauna a nutse tace,
"ita wa din?"
"Ummi mana"
Sakina ta fada da sauri tana me kara jin takaici a ranta, shiru haj suwaiba tayi ta tafi zurfin tunani, wani murmushi mugunta tayi sbd tunowa da_haduwar su meeting da zasuyi next week da gobe ne sai aka daga kuma a wannan meeting mai kano zaizo wato gang leader a ranar dazai sauka dayawa ana kai masa kyawawan enmata yyi fasikanci dasu a daren ranar washe gari a bawa dodon tsafi jinin yarinyar da ya gama lalata da ita yasha to a cikin members duk wanda yyi dace yarinyar daya kawo mai kano ita ya zaba ana masa karin girma sbd martaba abin da suke, sannan su wa'annan emmata sato su ake wanda ba'a zaba ba su zama bayi masu bauta, toh ita duk wanda take kaiwa bata nasara dan haka zata kai ummi ko zata dace ta samu tambarin girma ta hannun dama a cikin members._
wannan shine gajeran tunanin da tayi kuma tayi na'am dashi, kafin ta dafa kafadar sakina tace,
"yanzu wannan er yarinyar ce dama ta daga miki hankali shine nima kikeso nawa hankalin ya tashi?"
Sakina na jan zuciya tace,
"ke kike mata wannan kallon amma yanzun kam kan mage ya waye taci jar miya."
Haj suwaiba ta danyi murmushi tace,
"idan a kanta ne sai mu batar da ita ya zama naki ke kadai"
"yeeeey...."
sakina ta juyo ta rungume momy tace,
"shiyasa nake yinki wlh kinsan takan makirci, toh amma taya zamu btar da ita batare da kowa ya farga ba?"
Haj suwaiba tana dariya tace,
"kibar wuqa da nama a hannu na kawai."
"Na bar miki"
sakina ta fada tana mikewa tsaye hade da shafa ciki tace,
"yunwa nakeji wlh."
Haj suwaiba tace,
"toh nima baki barni nayi nawa karin ba sai kije kitchen ki debo mana muci."
"Toh momy" sakina ta fada tana yin hanyar kitchen yyinda momy ta bita da kallon yarinta dan kam wayo tayi mata dan nata buqatar badan ta yadda da auren ba.******
Saida ya bari ta shiga kitchen tana abincin rana ya koma dakinsa da sauri, kiran suraj yyi suka gaisa ya sanar masa meeting fa sun daga sai next week,
"kaiiii....."
Suraj yafada yace,
"wlh mutanen nan sunada matsala har mun gama zama ready zasu canja lamari?"
"Mtwsss.." El-bash yaja tsaki dan yana ganin shi akafi cuta so yake ya gama aikin nan ya huta dan ya gurji amarcin sa me lasisi yanada maganganu dayawa da yakeson furtawa ga ummin sa amma babu dama sai zaman kurame "mtwsss" ya sake jan tsaki a karo na biyu. Suraj yace,
"mgn muke naji sai jan tsaki kke"
"Bazaka gane bane suraj amma kam ni sukafi cuta."
Suraj yace,
"hakuri zaka kara kasan aski yazo gaban goshi yafi zafi."
"Hmmmm..." El-bash yaja ajiyar zuciya yana kara hango nisan 1week a wajensa,
"Bye"
kawai yace a takaice ya kashe wayar yana maida ta inda ya saba ajewa ransa duk a bace.~~~~~~
Knocking suke na fitar hankali kamar zasu balla kofar, gam...gam..gam..., Haruna dayake dakinsa kwance yanajin ya samu salama yau ya taso rai a matukar bace zaiga yau wanne mahaukacin ne yake buga masa kofar gida, inna na jikin kofar tana surfa bala'i yyinda jamila ke gefe, basu san ya taho ba, shi kuma haruna da biyu yazo buda kofar yana zare sakata dake ta baya ne budewa ya hankada kofar da karfin sa yadda koma waye me nacin bugun shima yaji inda da dadi, luuuu..., inna tayi taga-taga zata fadi sbd turawan da yyi ya sameta har tayi baya, duk yadda jamila taso tareta saida inna ta zame ta fadi hade da gangarawa cikin wata kwata dake gefen hanya,
"Yeeeey.... iya ruwa fidda kaii, Hhhhh"
wasu samari dake nesa dasu suka fada suna sheqewa da dariya da alama irin marasa kunyar nan ne. Kunyace ta kama jamila tace,
"Innalillahi"
ta fada tana dora hannu akai,
"Ke rikemin hannu na tashi bawai ki tsaya kallona ba"
Inna ta fada tana yunkurawa dakyar, duk yadda haruna yaso mazewa kasawa yyi saida ya dara, dariyar sa ita ta fargar dasu da tsayiwar sa a wajen, cikin borin kunya suka haushi da fada, jamila tace,
"ashe dai baka da mutunci ban sani ba? Uwata ta fadi kana mata dariya?"
"Ke kuma meye hadina dake?"
Ya fada yana yatsina fuska kamar be taba saninta ba, Cikin jin haushi inna tace,
"kai haruna idan kai ba shege bane ka haifu cikin iyayen ka na sunna ka karasa sakin da kayima 'yata ya zama uku kaga idan kwantai zatai a gari."
Ran haruna ya baci yana kallon inna da dan guntun mutunci a idon sa sbd ummi dan duk wanda ya rabi ummi yana ganin darajar sa to amma da alama so take ta kankare sauran, Ba tare da bata lkci ba yace,
"taje na tsinke sauran igiyar dake tsakanin mu shikenan?"
"Ahayyye Rasss..." Jamila ta fada tana rike qugu tace,
"daidai kenan dan wahala inna muje"
ta fada tana kama mata hannu. Sun danyi nisa haruna ya daga murya yace,
"azo a kwashe sauran kaya ko na watso su waje."
Inna ta juyo tace,
"aiko baka fada ba wannan dole ne tunda bada kudin ubanka aka siya ba."
Rufe kofar gidan yyi yana fadin,
"gayyar tsiya."
Su inna sunzo daidai gun samarin nan sukaji an sake kwashe musu da dariya wani ya sake duban zanin inna dake digar ruwan kwata har yanzu yce,
"wa yaga kaza a ruwa"
yyi mgnr sauran na kwashewa da dariya,
"uwarku ce kazar shegun yara marasa tarbiya"
inna ta juyo ta fada musu hakan. Dariya suka sake kwashewa da ita da alama ta zamar musu abin dariya. Yyinda jamila ta sake jawo hannun inna dan suyi sauri subar unguwar.••••••••
Koda ummi ta fito kitchen sai taga el-bash baya wajen data barshi, dan haka itama ta haura saman dakinsa ta wuce tana budewa ta ganshi ya kwanta yyinda ya nade hannun sa baya ya dafe keyarsa dasu, idanunsa na kallon sama kamar me tunani bacin ran dazu be gama gushewa a fuskar sa ba, a sanyaye ta karasa gaban gadon ta zauna a gefen sa tama rasa me zatace, to mema zatace mutumin da baida hankali?Zamanta kusa dashi shiya fargar dashi zuwan ta, tausayi ta bashi dayaga ta zauna tayi jugum yasan baya rasa nasaba da halin data tarar dashi ta fahimci yana cikin damuwa, ita ya zubawa ido daidai lkcn itama ta juyo suka hada idon, gani tayi ya mata murmushi wata boyayyar ajiyar zuciya ta saki tana maida masa da nata murmushin ta rasa meyasa batason ganinsa cikin damuwa, gani tayi ya wara hannun sa alamar tazo, da murnar ta kuwa ta fada saman qirjinsa yasa hannayen sa ya rungume ta tsam, a tare suka sauke ajiyar zuciya.
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...