EL-BASHEER 55

588 43 1
                                    

*EL-BASHEER*

*Wannan page din kyautace  a gareku...*

_Mrs Tajuddeen tajra, ummi sulaiman, Fatima Muhammad Abba, Queen dimple😊, My qawa Amintako🤪, qawalli Na'ima❤_

*Kuji dadin ku😍 na gode da  comments🥰*

*My Fans akwai masu comments suce Gsky Nuceey kina WUTA🔥🔥😢😢 na hadaku da girman Allah ku daina fadin haka👏🏻😦 kumin Addu'ah ko sharhi is okay🥰👌🏻*


55

Banda wani zabi sama da nabi shi, haka na fito suwaiba nabin bayana, har bakin motar Rabe mukaje dama bakin glass gareta duk wanda ya shiga babu me ganinka, daga can gate mlm sabo yana hango mu saidai da alama bazai fahimci me ake ciki ba, Haka na shiga suwaiba na banko min kofa, Itama gaban motar ta shiga sannan suka dage glass din baya yadda babu me kallon abinda ke baya, daidai zamu fita suwaiba ta dan rage glass tana kallon mlm sabo dake rike da radio tace masa kai sabo zan fita idan sakina ta shigo kace ba nisa nayi ba yanzu zan dawo, gyada kai mlm sabo yyi yana fadin a dawo lpy ya koma ya zauna yana sake kara radio a kunnen sa, naso ace nayi mgn da mlm sabo saidai ba halin haka, lkcn da muka fita a gidan na juya ina kallon gate din, naga hankalin mlm sabo ya dawo kan motar ya zuba mata ido kamar me tantance wani abu sabanin da daya nuna halin ko in kula lkcn da suke masa mgn, har muka bacewa ganinsa naga still be daina kallon mu ba, a haka har muka bar unguwar,
     

hmmm.. Haj Hafsat taja ajiyar zuciya tace kasan meya faru? Taci gaba ban sake tantance kaina ba sai a wani dan karamin daki,  cikin wani dan karamin gida, a lkcin a gigice na farka hade da salati a bakina, ina cikin salatin naga wata yarinya ta shigo da sauri tana fadin sannu Umma, binta nayi da kallo sbd nasan babu me kirana da wannan sunan sai Dana Basheer, take na fashe da kuka tunowa da nayi abinda ya sameni su Rabe shaka min hoda sukayi harta bugar dani bansan ya akai na kasance a dakin ba, Kiyi hakuri umma, naji yarinyar ta sake fadamin, hankali na ya kasa kwanciya da inda nake, nace ke yarinya a ina nake nan? Nijar, a firgice nace Innalillahi Nijar? Me kuma zakuyi min anan bayan rabani da dukkan farinciki na da kukayi? Ba kunce na bar rayuwarku ba? Kuma na amince me kuma yyi saura?

Gani nayi yarinyar tana girgiza kai tana fadin Subhanallah, Subhanallah Allah ya tsaremu da yin wannan mummunan aikin, mmki ne ya sake kamani nace ke kodai Aljana ce ban sani ba? Wara ido tayi tace Meyasa kikace haka umma? Nace kince ina nijar, banji kina hausar su ba, sannan banga wani mahaluki ya leko ba, banji motsin kowa ba, ba dole nayi zargin haka ba? Gani nayi tayi murmushi abinda ya sake tsundumani cikin mmki kenan ina jiran naji ta bakin ta, can tace, Umma Ki kwantar da hankalin ki nima er Nigeria ce, yadda kika ganki anan nima wannan shine karon farkon zuwa na kuma a dalilin ki nima nazo, Gyara zama nayi sbd abinda ke fitowa a bakinta ya daina bani mmki sai Al'ajabi nace ga dukkan Alamu akwai muhimman bayanai a tattare dake, ki sanar dani kafin na nausa wani wajen kamar yadda makiyana suka nema,

Gyara zaman itama tayi tace, da farko dai ana kirana da suna Husnah, Nima cikakkiyar er kano ce, babana shine ya turoni na kula dake sbd wasu ayyuka da suka sha kansa, amma kam tabbas shiya ceceki, ko nace tare dashi mukazo inda makiyan ki suka watsar dake, ya hadani da wani tsohon mutum yayan Abokin sa shi kuma ya tafi, yayan abokin nasa be cika zama a gida bane shiyasa baki gansa ba, kuma gidansa yadan fita daga wajen gari, abokin danki suraj yana kasar yyinda shi El-basheer baya kasar kuma ba'a samun sa a waya,
Sbd wani aiki da aka turashi, kai tsaye  babana ya kira suraj  ya sanar masa dukkan abinda ke faruwa dake, lkcn shima yaje kaduna kan wani case, a take yace ma babana ya baki mafaka kafin yazo zuwa jibi, babana beyi kasa a gwiwa ba yyi duk yadda zaiyi ya baki taimako cikin hukuncin ubangiji, duk inda makiyan ki sukabi haka muke binku a baya, har muka ga inda suka aje ki suka tafi, babana besha wahala ba da yaga inda aka ajeki ya kira wani abokin sa shine ya hadamu da yayansa dake zama a wajen gari.

Nace mata Husnah waye wannan baban naki? Sannan ina mamanki? Dan murmushi tayi tana girgiza kai tace babanta be bata damar fadar koshi waye ba sbd Allah yyi dan haka karta sake ta fadi waye shi, duk yadda naso ta fadamin ki tayi, haka na kwashe 3days muna tare, yarinyar 'yar arziki ta shiga raina sosai, duk yadda naso shan cikinta ta fadamin qi tayi, haka na hakura sbd nasan akwai special people da suke abin Alkhairi batare da sun nuna ba,

kamar yadda suraj ya Alkarwanta sai gashi a gidan da yamma, a lkcn har ya sanarma basheer halin da nake ciki dan ya samu wayarsa daga baya, hankalin basheer ya tashi matuka, ransa ya baci ainun, zuciyar sa tayi quna sosai, yana tsaka da aiki a Pakistan yace zai dawo,  dakyar suraj ya taushe shi akan subi komai asannu, badan yaso ba ya hakura sbd anason a kama masu lefin dayawa dama ana ta binciken  case din en HSK Association an rasa bakin zaren da za'a kama, wanda yyi nasarar samun zaren saidai aji mutuwar sa sun kashe shi,dan da sun fuskanci ana binciken su yanzu zasu kashe mutum, toh abin sai yazo masa faduwa tazo daidai da zama sai suka yanke shawarar shi da suraj ya karbi case din,   sun bar shawarar a haka yyinda suraj yyi duk abinda zaiyi nabar kasar batare da an samu akasi ba,

dakyar muka rabu da husna sbd munyi sabo, naso ma mu tafi tare nanma taki, tace babanta bazai barta ba, na nemi ta  fadamin me takeso tace ba komai, nace mata ta dubi girman Allah sau daya dai yadda ta faranta min ita da mahaifin ta su bani dama na faranta musu, sai a lkcn tace burinta daya tayi kr2 son samu ta karanci bangaren tsaro na sirri dan tanada burin bawa kasa gudunmawa musamman dan ganin wargaza qungiyar HSK Association, na jima ina kallon ta sbd yadda naga ra'ayin daga zuciyar ta yake fitowa bawai a baki kawai ba, murmushi nayi nace husnah banda abinki kina mace ina ke ina wani aikin jami'an fararen kaya? Karki manta fa ana iya turaki wata jahar,

husnah tayi dan jim kafin tace for once in my life zanso na bawa kasata gudunmawa, wannan kungiyar zanso ace dani aka wargaza ta da ikon Allah, wlh umma tunda naji lbrn ki naji na tsani mutanen nan tun kafin na gansu, Yadda naga ta jajirce nace Allah yyi jagora daga nan muka rabu, nabar wa suraj duk wani nauyi na university dinta da take bukata, wannan abun daya faru Basheer be sani b, dan kai tsaye mukace masa wani bawan Allah ya taimake mu, koda yaso jin ba'asi mukace muma bamu sanshi ba,

Da nazo Pakistan basheer shine ya tarbe bi,ya kama min haya sbd shi a hotel yake yana binciken wani, haka nayi rayuwata anan tare da basheer dan daya samu hutu wajena yake zuwa wani lkcn shi da suraj a haka yasai min wannan gidan muka dawo ciki.

         sosai basheer ya tsananta bincike akan su, dan hausawa sunce idan baka iya kama barawo ba sai ya kama ka shiyasa yake binsu ta karkashin kasa, kwatsam ranar basheer ya kirani yaga kullin da suwaiba ita da kaninta sukeyi akan su haukatar dashi,  daidai lkcn kuma aka bashi ragamar case dinsu, a ranar da sukace zasuje gun boka ayi masa aiki, aranar bamu rintsa ba kwana mukai muna kai kukanmu wajen Rabbil Izzati, kwana biyu da zuwan nasu sukayi plan kawai yyi haukar karya dan aikinsu yafi tafiya successfully b tare da an fahimci hakan ba, haka kuwa akayi ya maida kansa mahaukaci, sai murna suke zaton su magani ne yaci basu san cewa ba hakan bne, a haka yyi ta zama dasu yana samun nasara a kansu sosai.

Wannan shine karshen Boyayyen abinda baka sani ba, haj hafsat ta karasa mgnr tana jan zuciya sbd kukan da tayi har muryar ta na dashewa.

Jawota Abba yyi jikinsa ya rungume tsam yana dan buga bayanta, dauriya ce kurum irinta namiji dan duk wanda ya kalli idon Abba zaiga yadda ya  kada yyi jajir.

*CIGABAN LABARI*

......oh ko su el-bash an farka?😂

EL-BASHEERWhere stories live. Discover now