EL-BASHEER*
Na
Nuceeyluv😘54
A banagaren Abba kuwa koda yaji an rufe masa ido ya saki sassanyar ajiyar zuciya, juyo da ita yyi ta dawo gabansa ya rungume ta tsam a jikin sa, itama umma rungumar tasa tayi, sunyi kusan 5mins a haka suka saki juya, Abba ya zuba mata ido ko kyaftawa bayayi tambayoyi ne fal ransa amma ya rasa ta ina zai fara? Kazalika canjawar haj Hafsat shike kara narkar dashi yadda yaga ta koma kamar er 28yrs sai kace ba ita ta haifi El-bash ba, murmushin dake kan fuskar umma ya kasa gushewa ranar da ta dade tana jiran abin kaunar ta yazo, ganin irin kallon da yake mata ta hura masa iska a ido,
firgigit Abba ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, murmushi yyi yace,
"Umman Basheer kece kuwa?"
Er dariya haj Hafsat tayi tana me kamo hannun sa tace,
"muje mota tsayuwar ta isa haka kana bukatar hutu"
Abba yyi dariyar shima yace,
"hafsana kinsan kallon ki kadai ya isa ya kori duk wata gajiya dake tattare dani"
haj hafsat na driving tayi smiling kana tace,
"kana nan dai kamar yadda na sanka" Abba yace,
"a kanki babu abinda zai canja, burina yanzu naji meyasa kuka zabi boyemin gsky keda murdadden dan naki" dariya ce ta kwace ma umma, Tana me karya kwana cikin wani kerarran gida ta juyo tana kallon Abba tace,
"duk abinda yyi halinka yyi gado like father like son"
tayi mgnr tana kokarin fita a mota, Abba shima fitowa yyi yace,
"haka dai kke fada kamar kullum."
har cikin wani hadadden parlo umma takai Abba tana fadin,
"lale marhaban ya Habibi"
tayi mgnr tana kamo hannun sa suka zauna, Farinciki ya kama Abba yaushe rabon da yaji irin wa'annan kalaman? Umma tace,
"Wanka first, Abinci second, hutawa last"
tayi mgnr tana qirgawa da hannu Abba yyi murmushi yana tuna baya yadda suka kasance a zaman su, kullum cikin nishadi suke da faranta ran juna.~~'~~
Bayan Abba yayi komai ya huta, umma ta shigo dakin sa, lkcn yana duba abu a system tasha wanka sai kamshi take itama, da fara'a ta karasa inda yake ta zauna, Abba ya ture system din gaban sa yace,
"so am all ears." Haj hafsat tayi murmushi tace,
"ohk."
Sannan ta fara da....*FLASH BACK* ( _WAIWAYE ADON TAFIYA_ )
.........."Kamar yadda ka sani mu biyu ne matan ka Alhj, Bawai dan ina uwargida ba ko kuma ace kishi ba, a'a gsky kawai nakeson na fahimtar dakai, kafin nan zanso kasan cewa Alhj Rabe wanda ka maida shi mutum shine yake cin amanar ka ta karkashin kasa, abinda nakeso ka gane anan shine, Silar auren ka da Haj suwaiba ba kowa bane sai Alhji Rabe shine wanda ya taimaka har aka shawo kanka ka aureta, shima da sharadin idan ka aureta zasu hada kai suci amanar ka, karkace qage na mata No,
bayan shigowar ta gidan ina fahimtar duk wani karan tsana data doramin musamman kan *EL-BASHEER* kasan meye dalili? sbd kawai bata haihu dakai ba domin abinda ya kawota shine *GADO* abinda mafi akasarin mata keyi yanzu kenan wasu badan Allah suke auren me kudi ba saidan *GADO* kana tunanin mace na sonka nan kuwa tunani da hango ranar mutuwar ka take abinda kuma su matan basa ganewa shine Rai dayan nan dai a hannun Allah yake, babu meyi maka komai ba tare da Allah yasa hakan yana cikin kaddarar ka ba, So duk lkcn daka fita waje harkar kasuwa zai kasance Alhji Rabe na yawan zuwa gidan musamman idan yaga shima Basheer baya nan,wata rana Me gadin gidan namu yazo har part dina ya gaishe ni, bayan mun gaisa sai naga ya tsaya nace,
"lpy mlm sabo?"
Mlm sabo yace,
"haj Abinda ake a gidan nan ne naga yana muni dayawa mezai hana Kisa Bashari yasa ido a Al'amuran gidan nan?" Lkcn daya gayamin hankali na ya tashi nace,
"kai mlm sabo me ake a gidan dahar kazo kana min mgn ni dana ke ciki ban sani ba?"
Mlm sabo yace,
"Allah yaja daran haj Wato a zahirin gsky Ana bin dunduniyar Alhj a gidan nan ya kamata a farga"
a razane nace masa,
"kai mlm sabo banason soki burutsu na en aikin gida, banason gulma, dan haka fice ka bani waje kafin ranka ya baci"
mlm sabo ya mike jiki a sanyaye yabar prt dina saboda naki bashi kofar dazai warware min abinda ya kawo shi, so tinda ya tafi hankali na ya kasa kwanciya, sai zaga parlo nake, dakyar na yakice abinda ke raina na daina tunanin a ganina shaidan ke neman samun nasara a raina harya fara min huduba akan abokiyar zamana.
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...