EL-BASHEER*
*NUCEEY LUV NOVEL HOUSE FACEBOOK* wannan page din kyauta ne a gareku naji dadin yadda kukemin Sharhi❤
*EL-BASHEER FANS GROUP* wanna page din tukwice ne a gareku, yadda kukemin comments abin na birgeni Allah yabar kauna❤
Na
Nuceeyluv😘50
Saida sukayi nisa da airport me driving din ya sake daukar wata hanya daban, saida sukayi tafiya me dan tsawo suka iso wani makeken gida, har a lkcn babu wanda yyi mgn, ba tare da bata lkci ba me gadin gidan ya wangale kofa, habawa tun daga gate din gidan mutum ya kalla yasan an zuba naira sosai bare ace ya shigo, abin ba'ace komai, parking yyi ya kashe motar nan suka fito hannun me driving din rike da system, da dan sassarfa suka karasa cikin gidan, suna shiga ya yaye fuskar sa, sai ga fuskar *EL-BASHEER* ta bayyana, suraj ya sara masa yana fadin,
"Gwaska"
dan hararan sa yyi yace,
"ni da Allah zauna muyi abinda ya kawo mu inason komawa gida" suraj yace,
"kodai kanason komawa wajen little baby?"
Yyi mgnr da sigar tsokana,
"Mtwss....."
El-bash yaja tsaki yana fadin,
"kanada matsala wlhy"
yyi mgnr yana operating system, zama suraj yyi yana er dariya kawai. Kusan mintina ya dauka yana danne2 a system din har ya gama kafin yace,
"kaga duk wasu bayanai da muke son samu muna samunsu sannu a hankali, mutanen nan zasuyi meeting nan da jibi kuma a wannan ranar babban nasu zaizo Alhji mai kano da kaji suna fada, so zamu sa ido sosai a kansu, Mgnr kamfanin Abba kuma Alhji Rabe ne yasa a kashe Abba sbd yanason kamfanin ya dawo hannun sa gaba1 kuma yana ganin banda hankali ba komai zan iyayi akai ba, and again....,"
dol..dol..dol. Wani red abu ya fara signal daga gefen system din, da sauri el-bash ya danna tare da manna karamin abu a kunnen sa, mgnr Alhji rabe yaji da haj suwaiba suna mgn, Dan haka ya tsaya sauraro, ji yyi Alhji rabe na fadin,
"ke suwaiba Mahaukacin gidan ki kuwa na gske ne?"
Haj tace,
"ban gane ba me kkeso kace Rabe?"
Alhji rabe yace,
"keni je ki dubamin part dinsa yana nan?"
Haj suwaiba tace,
"Ina gidan kawata haj sadiya yanzu Amma bari naje na duba tunda ba nisa"
Kit Alhj Rabe ya katse wayar yana huci dan ya dade yana shirya yadda zai kashe Abba amma rana daya an wargaza masa shirinsa daya dau tsawon lkci yanayi.Da sauri ya fisge abin kunnen sa ya mike tsaye yana kashe system, suraj yace,
"me kaji?"
Cewa yake,
"suraj muyi sauri aikin mu zai baci"
"Innalillahi"
suraj ya fada shima yana mikewa, suna tafe el-bash na zayyane masa komai, a hanzarce suraj ya karbi car key wajen el-bash, shi kuma ya rufe jikinsa kamar dazu, a 360 suka manni motar a guje, tsakanin su da gida kusan tafiyar minti 25 ce, yyind haj suwaiba befi 15mins ta isa gidan ba, A bangaren Alhji Rabe ma kasa nutsuwa yyi ya zari motar sa ya fito da sauri shima tafiyar sa be wuce 20mins ba da gidan.Ana wata ga wata ko waye zai fara isa.?
******
Abba yana cikin jirgi abin duniya duk ya ishe shi, zaro takardan nan yyi ya fara karantawa kamar haka:_Assalamu Alaykum, Abba nasan a yanzu da kake karanta wasikar nan kana cikin rudani da tashin hankali, saidai inaso kayi hakuri bisa tarin abubuwan da na boye maka, badan komai nayi hakan ba sai dan sbd ku iyayena, Abba kisan da aka zo yi maka da dare ba kowa bane yasa a kashe ka ba sai matarka haj suwaiba wannan shirin tane,._
Wani jiri ne yaso kwashe Abba sbd shiga tsananin rudani da tashin hankali, Lalle hausawa sun iya mgn da sukace Ashe makashin ka yana tare dakai, yanzu zaman cin amana take dashi be sani ba? Kaiii duniyaaa..., sake ci gaba da karatun yyi,
_mgn ta biyu kuma Alhji Rabe daka dauki Amanar dukiyar ka ka bashi har ka dorashi bisa kamfanin ka na kano shine yasa a kashe ka dan kamfanin ya dawo nasa ya dade yana wannan kullalliyar yana shakkar yi ne sbd yana kallo na da kuma yanayin aiki na, a lkcn na zarge shi sai dana maida kaina mahaukaci na tabbatar da zargina ya zama gsky, Hmmm Abba kasan meyasa na maida kaina mahaukaci? I know zakaso kaji amsa, to wannan amsar tana wajen ummana ka gaishe min da ita idan ka isa kasar Pakistan, itace ma zata tarbe ka tana jiranka a airport, yanzu bayanan dana maka a dunkule suke ummana ita zatayi maka fashin baqi uwa uba zata gaya maka meyasa ta zabi boye kanta tsawon lkci a matsayin ta mutu? Fatan Alkhairi Allah ya saukeku lpy Abba._
Wata irin zazzafar zuface ta dinga ketowa Abba ta goshi ta cikin jiki,mamaki da Al'ajabi ne suka taru sukayi masa dirar makiyiya, wai meyasa yanzu Amana tayi karanci ne a duniya? Kowa kokarin gyara kansa yake, baya manta haduwar sa da rabe turin baro yake lkcn ya gama secondary baida halin ci gaba,
idanuwansa na zubda hawaye yazo neman taimako gun Abba mahaifiyar sa ba lpy zai biya kudin mgni, Alhji usman akwai tausayi ya dauki kudi ya bashi, bayan taji sauki yazo da mahaifiyar tasa yi masa godiya, Alhji usman yace ai ba komai dan Allah yyi musu badan su gode ba lkcn El-bash na jss3, sunji dadi matuka, har zasu juya ya sake kiransu yace yama sunan ka? Yace Rabe, yace dakyau ka gama kr2 ne? Eh na gama ban samu ci gaba ba ina sana'ar turin baro, Alhji usman yace Eyya kace babanka baya raye? Eh ya fada yana risina kai, okay yanzu me kkeson karanta idan ka samu hali?
Rabe yace Business Admin, wow good choice Alhji usman ya fada, yace ka kawo min takardun ka zan nema ma buk Insha Allahu zan dauki nauyi, da murna shi da babarsa kande suka hau masa godiya. Nan dai suka tafi. Tun daga wannan rana Alhji usman ya dau nauyinsa kuma yana masa Alheri sosai, babar rabe tana girmama Alhji usman kullum tacema danta duk sanda kaci amanar mutumin nan ban yafe maka ba,
a haka ya gama kr2 Alhji usman ya jawo shi ya dora kan kamfanin sa na kano, Rabe an koma Alhji, sai gashi hasada da kyashi sun fara masa yawo a zuciya, ji yyi a ransa yanason yafi Alhji usman kudi da matsayi saidai babu hanya, Suwaiba itace me musu sharar office ita taja Alhji Rabe kungiya tunda taga yanada zalama, kuma itama so take yyi mata hanya ta auri Alhji usman, ba bata lkci kuwa ya zubawa Ahji usman mgnin Asirin da ta karbo dan ya aureta, sbd haka kurum jininsa be hadu dana haj hafsat ba da kuma danta El-bash.
Wani dogon numfashi Abba yaja sbd tunanin da yyi lalle ya kara yadda dan Adam butule ne ba duka suka san Alheri ba.
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...