EL-BASHEER*
Na
Nuceeyluv😘40.
Shigar su parlon kenan suka tarar da tarin aika-aikar da El-bash yyi, da sauri Abba ya isa gareshi yana rike hannun sa yace, "Subhanallah haj tayani gyara kujerar can na zaunar dashi," haj suwaiba tadan yatsina fuska, ita fa batason a takura mata kan mahaukacin nan mtwss, Abba ne ya juyo ya kalleta tana tsaye kamar dazu daga bakin kofa yace, "bakiji bane.....," be ida mgnr ba yaji ana kokarin gyara kujera,
Ummi ce ta gyara kujerar tana sunkuyar da kai sbd kunya tace, "Abba sannun ku da zuwa ga waje nan bari na gyara sauran ku zauna," kallonta Abba yyi yana me jin dadi a ransa lalle da alama be yiwa dan nasa zaben tumin dare ba ya kara yabawa da nutsuwar ta kwarai,
zaunar da El-bash yyi yace,
"sannun ki kinji Allah yyi maki Albarka"
tace, "Ameen" cike da kunya d kuma jin dadi rabon da ace mata Allah ya maki Albarka tun iyayenta na raye.
Tabe baki haj tayi tana kallon su a ranta tace,
_oho dai sai kuyi ta fama da mahaukaci._
Takowa tayi ta zauna kan wata kujerar da ummi ta gyara, zuwa lkcin ummi har ta kusa share inda ya zubar da abincin. Abba ya kalli El-bash cike da tausayawa har lkcn yana rike da hannun sa yace,
"Allah ya baka lpy Basheer"
Haj tanaji ta sake mere baki tana me ayyanawa a ranta indai El-bash ne shi da warkewa sai a kiyama.
Shigowar ummi yasa Abba ya dago da kansa yana amsa sallamar ta da tayi, wajen su ta iso tana me durkushewa a gabansu tace,
"barkanku da safiya Abba da fatan kun tashi lpy."
Abba da murmushi dauke fuskar sa yace,
"Lpy lao ummi ya kwanan bakunta"
Ummi cike da kunya tace,
"Alhamdulillah"
a yatsine haj tace,
"ya akai mutum na hauka baki iya zuwa ki kamashi ba har saida mukazo a haka zakuyi zaman?"
Ummi na tsugunne ta kasa banbance halin da take ciki, shin kunya ne ko mmki? Itadai tasan ba itace ta tsokalo shi ba hasalima sai gani tayi ya mike yana zabgar matar datazo dazu wacce ta kasa fahimtar mene alakar ta da El-bash da take ikirarin mijinta ne, kanta ya kulle sosai lkcin da taga yana jibgar ta shin dama masoya ne tun asali ko makiya?
Abba ne ya katse shirun da fadin,
"haba haj baki ganin kokarin da tayi ne? Be kamata ki jefeta da wa'annan kalaman ba, ko banza idan kika duba parlon nan da kyau kinsan ya fara dawowa hankalin sa."
Haj tace,
"Daga fadar gsky Alhji baka gnin yadda take gudunsa? Da bamu zo ba saidai yyi ta hauka har ya gaji da hauka ya daina haukar......"
"Enough"
Abba ya fada d dan kaushi yaci gaba da fadin,
"Hauka..hauka..haukaaa sai fada kike sbd Allah wannan wacce irin kalma ce marar dadi? Idan baki sani ba kisani wannan kalmar tafimin kowacce irin Kalma me daci a duniyar nan ya kamata ki dinga saisaita kalaman ki akan El-bash zan iya yin komai idan nace komai ina nufin komai ma a kansa."
Tashi tsaye haj tayi tana me rage sautin muryar ta cike da dan kukan munafurci tace,
"yiii... Alhj sai kace min gori kkson min, iyakata kkeson nunamin, matsayina akan Bashari kkeson isar min ba lefinka bane nawa ne dana nuna kulawata a kansa, tana gama mgnr ta fice."
Girgiza kai Abba yyi yana mejin daci a ransa, tsaf ya fahimci irin tsanar da suwaiba take ma dansa, yanason rabuwa da ita amma ya kasa, ya rasa me ta tsare masa ita ba haihuwa suka hada ba, gashi bason tilon dansa take ba, yana tunanin lkci yyi da zai rabu da ita.
Ummi hankalin ta ya tashi matuka, batason ganin manya na sa'insa agabanta, bare yanzu sa'insar akwai rabon sunan ta a ciki, itakam ta tsorata gsky, adan tsorace tayi ta maza tace,
"Ab...Abba.. Dan Allah kayi haku..ri"
tayi mgnr bakinta na rawa, murmushin dattako Abba yyi yace,
"karki damu kinji? Karki sa wannan a ranki kinji?"
Ummi a ladabce tace,
"Toh."
Abba yace,
"good, kinci abinci?" Ummi ta girgiza kai, Abba yace, "Subhanallah inace suraj ya kawo muku?"
Ummi tace, "eh gashi can ma," Abba yace,
"me kike jira bakici ba ko so kke ulcer ta kama ki?"
Ummi ta mike ta jawo basket din dazu Allah yaso ma da saura sosai a ciki ta gayawa Abba yadda ta kasance dazu saidai bata fadi zuwan sakna ba. Cike da tausayi Abba yace,
"sannu kinji, Insha Allahu zai warke daga wannan cutar, yanzu zuba kici sai ki zubo nasa na gwada bashi ko zaici,"
Ummi tace,
"Toh"
nan tayi yadda yace.
El-bash duk yana sauraran su saidai a jima ya hura iskar bakinsa yana me jin zafi a ransa, dazu ji yake kamar ya kama haj suwaiba ya gwarata d bango irin yadda yama diyarta, saidai taci darajar Abba, Amma muddin taci gaba da tunzura shi tofah yana dab da gwada haukansa a kanta.
Koda Abba ya bashi yaci sosai, ummi dake gefe tanacin nata a hankali taji dadi kwarai da taga yaci, koda ya koshi Abba ya mike tsaye ya kalli ummi yace,
"Zan wuce office inada baki na makara idan na dawo zan biyo tanan Insha Allah"
ummi a kunyace tace,
"Toh Abba a dawo lpy Allah ya tsare."
"Ameeen"
Abba ya amsa yana mejin dadin Addu'ar ta.
****
Hankali tashe ta fada dakinta, wayarta dake kan gado ta dauka number kaninta sale ta dannawa kira, bugu biyu sale ya dauka yace yadai yaya ko ta samu ne? Haj suwaiba hankali a tashe tace kai wanne samuwa? Muna zaune ruwa zai balle mana ya kamata duk inda kke kazo dan mgnr bata waya bace, sale yaja tsaki yace nifa matsala ta dake kenan yaya kwana-kwana ki fito direct kima mutum mgn yadda zai gane mana, haj suwaiba tace toh kullin da mukayi ma Alhaj na rufin baki fa da Alama ya fata sakwa2 mutumin da be iyamin musu dazu ya karamin tanadi, ya kamata ka hanzarta kazo musan nayi. Sale yace dole ma nazo, ki jirani zuwa gobe,haj tace toh sai naji ka, nan suka katse wayar.
Sauke ajiyar zuciya tayi tana tunanin da alama zata karbi shawarar sale a aika Alhji lahira kawai, dan yana neman hanata rawar gaban hantsi.
YOU ARE READING
EL-BASHEER
General FictionEL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na...