EL-BASHEER 11-15

637 48 1
                                    

EL-BASHEER

Na
Nuceeyluv😘

11-15

Da saurin sa yyi parking a gidan sbd wani aiki daya rikeshi yau sam ya sha'afa be kawo masa food ba, dukda dare yyi kusan 9pm yanzu bayajin zai kyaleshi tunda yasan idan be bashi ba bazaici komi ba Suraj kenan yyi hanyar part din frnd din nasa, kamar yadda yasan zai gani haka yaga parlon komai ya koma upside down aje ledar hanunsa yyi ya fara gyara wajen dama babu me gyarawa idan bashi ne yazo ba, cike da tausayi ya isa cikin dakinsa dake sama, be samesa a dakin ba amma yaji karar zubar ruwa a toilet hakan yasa ya fahimci inda yake, zama yyi yana jiran fitowar sa, ba'a jima ba kuwa ya fito, El-bash yana ganin suraj ya saki murmushi wow ashe haka murmushi ke masa kyau? Har wasu dimples gareshi suna lotsawa ya salam!  Abin dai so Masha Allah, fararen hakoran sa kuwa har wani sheki suke sai kace ba mahaukaci ba, suraj ya mike yana masa alama da hannu yace,

"ka sameni a kasa."

girgiza kai kawai el-bash yyi batare da yace komai ba.

Kayan bccinsa yasa bayan ya mulke jikinsa da cream hade da turare me dadin kamshi, kai lamarin el-bash akwai abin mmki idan yyi wani abun kamar me lpy wani lkcin kuwa idan ya birkice sai a hankali. Sakkowa yyi kasa nan ya tarar da suraj na jiransa, Suraj ya jawo plate daya dakko a kitchen yana bude ledar dayazo da ita yace,

"Srry na barka da yunwa ba lefi na bane kaji"

yyi mgnr yana kallon sa da murmushi, el-bash dai sai murmushin yake shima duk lkcin daya kasance da suraj baida aiki sai murmushi kamar wanda akayi masa bushara da gidan Aljanna, Suraj kuma tausayin frnd din nasa yake sosai dukda baya amsa masa hakan bazai hana yyi hira dashi ba shima yanajin dadin kasancewa dashi aminai ne na amana matuka, suraj ya tura masa plate din yace,

"bismillah muci,"

nan el-bash ya sake yin murmushi shima yasa hannunsa, nan suka fara cin abincin tare batare da sunce komai ba, can suraj ya sake kallon el-bash yace,

"frnd gsky muna mssn dinka a wajen aiki munyi rashin babban gwarzon jami'i,"

el-bash da ba ganewa yake ba ya sake yin murmushi, suraj duk jikinsa yyi sanyi sam bayason ganin frnd dinsa cikin wannan halin, to amma ya zasuyi? Haka Allah ya tsara, shima suraj din murmushin yake yyi sbd gaba1 tausayi ya lullube masa zuciya ya nisa kadan yace,

"Allah dai ya kawo mana karshen wannan abin Insha Allahu kaine bisa kansu frnd muna tayaka Addu'ah sosai"

yyi mgnr yana kama hannun el-bash ya hada da nasa ya dunkule yana girgiza kansa hade da murmushi, el-bash shima yyi kamar yadda yaga yyi wato ya girgiza kai yana murmushi. Kwashe komi suraj yyi ya mayar kitchen dake plate 1 ne nan ya wanke ya maida inda ya dakko dama ya saba yin hakan, dawowa parlo yyi nan ya samu el-bash ya koma kan kujera ya zauna, suraj ya zauna shima hade da kunna kayan kallo ya kamo tashar kwallo kusan 30mins lkcin 10pm yyi suraj ya kashe komi ya dafa el-bash yace,

"frnd am going,"

el-bash ya danyin murmushi kawai, suraj shima murmushin yyi yace,

"ok gudnyt, take care ok?"

El-bash ya sake sakin murmushi, Suraj ya juya kansa gefe yana kokarin maida kwallar da take shirin zubo masa ace mutum har mutum baida damar walwala? Kai duniya ana abubuwa a cikin ta, kallonsa ya dawo kan el-bash ya danyi masa murmushi yana me daga masa hannu, binsa da kallo el-bash yyi harya bacewa ganin sa.

Lumshe ido yyi yana me sake gyara kwanciyar sa. Suraj yana fitowa yaga alamar an wulga da sauri kamar inuwar wani abu, kunna wayarsa yyi ya haska wajen yaga bega komi ba, dan girgiza kai yyi yana cije lips yace,
_yeah i know, but it's just the matter of time._  Nan yyi wucewar sa gun motar sa yabar gidan.

EL-BASHEERWhere stories live. Discover now