EL-BASHEER 16-20

601 50 0
                                    

EL-BASHEER


Na
Nuceeyluv😘

*srry fans kun jini shiru ko? Wlh wni abu ne ya shamin kai, masu cmmnts inajin dadi kwarai da yanayin cmmnt dinku Allah ya barmu tare😘 masu cewa kwana biyu banyi typing ba to yaudai gashi😁👐🏻 aci gaba da gashi...🤺🏌🏻‍♀🤾🏻‍*


16-20

Kwatsam haj suwaiba na parlo taji dirin mota a harabar gidan, lekawar da zatayi ta hango Alhj Usman ne ya dawo, hankalin ta ya tashi matuka dan batayi tsammanin ganinsa yanzu ba, da sauri ta shige dakinta tana haki kamar wadda tayi gudu, Alhj usman ya iso cikin gidan nasa daya dade be samu zama cikin sa ba har zai gifta dake part din el-bash ne farko saiya hango kofar part din a bude, mmki ya kama shi dan yasan duk lkcin da yake gida yana gaya masa to amma tun yaushe yazo? Har zai je part din ya fasa nan ya wuce bangaren cikin gida, shigar sa parlo yyi daidai da fitowar haj daga daki tana yaken dole dan bataso dawowar sa yanzu ba, "sannu da zuwa Alhajina irin wannan bazata haka?"

Alhj yyi murmushi yana zama kan kujera yace,

"kai haj ko bakiyi farinciki bane?"

Haj ta sake fadada murmushin ta tace, "haba ni na isa? Ai yanzu haka da kke gani nafi kowa farincinkin zuwan ka,"  ta karasa mgnr tana me aje masa ruwa da lemo data dakko a fridge, Alhj usman yasha ruwa yyi hamdala yace, "wai yaron nan yana gari ne? Naga kamar part dinsa a bude,"

wani qullutun bakin ciki ne ya tirnike haj suwaiba kamar ta tashi ta shake shi ta huta da takaici haba ace mutum baida aiki sai son yaron sa? Komai zaiyi dansa shine first kome yake el-bash, zance yake el-bash sai kace wani dan gwal.....!

"Kinyi shiru kin zuba min ido hala baki gane me nake nufi ba?" Yyi mgnr yana son karantar yanayin ta, cikin sauri haj ta sauya yanayin ta Alamar tausayi hade da kokarin matso kwallar karya tana karya murya tace, "wlh Alhj bazaka gane bane bayan tafiyar ka mun shiga mummunan tashin hankali wlh"

"Subhanallah"

Alhaj ya mike daga kishingiden da yake yace  "fito fili ki fadamin meke faruwa wani abu ya samu dan nawa?" Wani takaici ya sake rike haj Amma ta danne tana share kwalla tace, "wata rana ne el-bash ya dawo yazo nan ransa a matukar bace idonsa yyi ja sbd bacin rai ganinsa a haka hankali na ya tashi nace yarona meya sameka? Sai cewa yyi rikici ne ya hadashi da wani inyamuri yana mgn rai a bace yace wai dan yaga Allah yana bashi ci gaba ashe inyamurin haushin sa yakeji shi el-bash be sani ba, saida dan rikicin ya hadasu mutum budar bakinsa yace wlh sai kasan kayi fada dani zaka gani ka jirayi sakamako, shine fa ran el-bash ya baci yana gayamin yace har akwai wani bil'adam dazai tsoratani? Wlh duk abinda yake ji dashi zan sauke masa ba inyamuri ba ko shine dangin Aljanu be isa yamasa abinda Allah be masa ba."

ta karashe mgnr tana me sake rushewa d  kuka.

A razane Alhj usman yace, "da suka samu sabanin wani abu ya masa?" Haj tana girgiza kai kukan karya yaci karfin ta tace, "kasan inyamurai akwai tsafi toh  bayan kwana biyu sai muka tsinci jin wata kara a bangaren sa muna zuwa muka ga ya hargitsa komai na parlon sa a takaice dai babu alamar hankali a tare dashi."

murya na rawa Alhj usman yace, "kina nufin *HAUKA* Yake?"

Haj tace,

"Eh"

cikin muryar kuka.

Alhj Usman be sake sauraran ta ba ya fito daga dakin cikin sassarfa yyi bangaren dansa el-bash hankali a matukar tashe. Fitarsa keda wuya haj suwaiba ta kwashe da wata iriyar dariya tana tafi tace, "ai wlh haka 'yan film suka ganmu suka bari wajen hada drama idan nice har abada ta bunnu kenan bazaka san gskyr lamari ba" tayi mgnr tana sake sakin dariya ta leka ta windo ta hango yana shiga part din ta tabe baki tace, "kaima a sannu zan maidaka wata halittar matukar naga zaka batamin lamari."

EL-BASHEERWhere stories live. Discover now