22. Solace

107 18 9
                                    

بسم الله الرحمن الرحيم
اسلام عليكم و رحمة الله و بركته

The previous chapter is boring nd painful! I cried also, it's fiction nd can be very real! Allah yasa mu dace, ameen❤️🙏🏽


Mutane suna zaune a harabar gidan hajja duk su mummy ma suna can, ansa carpet ana ta amsar gaisuwa.

Hajja, adda, mummy da husna da sauran matan suna cikin daki.

Carbi ne hannun husna tana ja amma bata san me take cewa ba! Gani take kamar mafarki ne ko wasa wannan masoyin da babu kamarshi yazo mata kamar walqiya kuma bat ya bace ba tare da kwakkwarar sallama ba.

Kallon dressing mirror din dake gefenta tayi taga turaruka reras!

Tuno kalmar humaid tayi!

"𝑘𝑖𝑛𝑠𝑎𝑛 𝑚𝑒 𝑦𝑎𝑓𝑖 𝑡𝑢𝑟𝑎𝑟𝑒 𝑑𝑎𝑐𝑖?
𝑟𝑎𝑠ℎ𝑖𝑛 𝑚𝑎𝑠𝑜𝑦𝑖!"

Wani zazzafan hawaye ne ya sauko daga idanunta!

Mummy ce ta kalleta ta girgiza kai, tun shekaran jiya sun saba har sun gaji, ita kadai zata tuna wani abu taita hawaye! Ko baka tmby ba kasan wasu memories ne masu nauyi take tunawa.

Hussain ne ya shigo har cikin dakin, kasancewar dan uncle abdul ne kuma abokin humaid to ya zama kaman dan gidan.

Wasu takalma ya mikowa husna.

Pink flat shoe!

Kallonta yayi yace cikin motar Humaid aka gani, ina kyauta zaton naki ne.

Kallon mummy tayi tace mummy,

Wlh Humaid bai taba daukan alkwari bai cika ba, kin gani gawarshi ma cika alkawari takeyi!

Kin gani ko, ya mutu amma bai manta da alkwarinshi ba.

Karba tayi ta rungume takalman aranta cewa take da kana raye da kanka zaka saka minsu, ka sani nayi tafiya ka gani.
Nasan ma sai kace ke tafiyar ma baki iya ba baby? To tsaya kiga yadda zaki taka sai ki fito matar humaid sak.

Wasu hawayen ta goge.

Hajja kanta saida taji kwalla tazo mata.

Haka akai taron sadakar uku, a hnkl mutane suka yoye.

Mummy tace wa hajja ya kamata Husna ta koma wajenta.

Hajja ta roki alfarma abar mata ita zuwa 7 sai ta dawo.

Ba musu suka amince.

Husna bata da aiki sai tunani, tunowa tayi duk sanda humaid yake gida tofa yini zasuyi cikin nishadi, he's so lively!

Ta tuno farkon samun cikinta, ya hanat girki kwata kwata, sai dai ya dafa da kanshi ko yayi musu order.

Ta tuna sanda ya musu order din pizza, sunaci suna dariya akan gado.

Ta tuna sanda ya musu order din pizza, sunaci suna dariya akan gado

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
HUSNA_HUMAID (completed )Where stories live. Discover now