10. eclipse

167 18 7
                                    


بسم الله الرحمن الرحيم

Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa bara ka tuhu..

Husna_humaid

10.eclipse😑



Asma'u tana kuka tace hammad what have we done? Innalillahi wa inna ilaihi rajiuna! Na mutu na lalace... Zinah.. Na shiga uku na tsani kaina ban taba zaton bazan kai mutuncina gidan miji ba, meya shiga kaina ne? Meya faru? Na rusa alkwarin addana, na rusa farin cikina... Hammad tell me mafarki ne, just tell me I'm a virgin... Ta qarasa da matsanancin kuka me qona zuciya😭😭😭😭

Hammad shima da nadama ta gama rufeshi ya dago ido yana kallonta tsananin tausayinta ne ya kama shi.... A take haushinta ya darsu a zuciyarshi dan gani yake meyasa ma ta amince masa suka aikata haka? Wace irin karamar brain gareta da zata yadda suyi lalata bayan ya tuba ta maidoshi ruwa!

(Niko nace kadan daga aikin namijin daya samu galaba akan mace)

Tashi yayi tare da gajeran tsaki yace ma'u wannan kukan babu abunda zai chanza yanxu dai ki tashi ki gyara jikinki yadda adda bazata gane komai ba.. Anjima zanzo gidan sai muyi magana at any moment su auwal zasu iya zuwa bana son su zargi wani abu.

Toh tace ta mike da kyar, zai taimaka mata tace kada ka qara tabani ka barni zan iya.

Baki ya tabe aranshi yace daga baya kenan.

Haka ta gyara jikinta ta tsarkake kanta sannan ta fito ya nemi ya rakata tace bata so, yace toh sai nazo, bata kulashi ba tayi ficewarta.

Ajiyar zuciya ya sauke ya kwanta tare da lumshe ido yana tariyo abunda ya faru. Ya sani nan duniya babu macen da yake muradi sama da Asma'u, ya samu nutsuwa kasancewa da ita, amma sam ya rasa peace of mind... Ya rasa  meyake damunshi ya akai ya keta haddin wannan innocent soul din? Meya sa ya ribace ta har aminta dashi? Wata zuciyar tace ai Asma'un ce wawiya akan me zata yadda kenan idan wani ne ma ya rudeta zata iya amince masa? ( tun ba'aje ko ina ba zargi ya shigo, muyi hattara en mata)

Wani sashen kuma yace nooo kawai dai dan tana sonka ne bata son bacin ranka! Haka yaita tunani amma har ya qare tunaninshi bai ynke hukuncin zai aureta ko kuma bazai aureta ba!

😑😑😑😑😑😑😑😑😑😑😑

Shigar Asma'u gida a tsorace gani take suna hada ido da adda zata san meya faru... Tana shiga adda tace yauwa ma'u ke nake jira dama zani gidan suna diyar maryama ta haihu.. Ki kula da gidan ki ci abinci in kin gama ki dora tuwon dare...

A sanyaye tace to adda... Har adda ta sa kai zata fita sai ta dawo gaban Asma'u ya fadi.. Adda tace lafiya kike kuwa? Naga kinyi laushi ko baki da lfy ne?

A'a lfy lau nake zane mu akai duka aji wai ana surutu...

Shine kuma dan sakarci kikai ta kuka?

Shiru ma'u tayi..

Adda tace toh Allah ya kyauta kiyi wanka da ruwan dumi kidanji dadin jikinki.

Toh tace.. Adda ta fita tana mamakin wai yau Asma'u tazo da complain din duka... Abin ma dariya ya bata.

Bayan fitar adda... Ruwa ta dafa ta sake gasa jikinta, ta tsarkake kanta sosai. Tanayi tana hawayen bakin ciki... Bayan ta fito tayi sallah kuka take iya qarfinta tana neman gafarar ubangiji...

Bayan ta gama ta dau abincinta taba almajiri dan bazata iya ci ba kuma bata shirya amsa tmbayoyin adda ba.

Batai qasa a gwiwa ba ta dora tuwo... Duk abunda takeyi tana istighfari tanaji kamr a mafarki ne wai yau ta rasa budurcinta.

HUSNA_HUMAID (completed )Where stories live. Discover now