23. Amelioration.

108 20 14
                                    

بسم الله الرحمن الرحيم ❤️🌹
اسلام عليكم و رحمة الله وبركاته 💕🌸

Husna ce zaune tana cin tuwon semo miyan kalkashi yaji man shanu, ta miqe kafafunta dan sun dan tasa sun fara mata kumburi.

Adda ce ta kalle ta tace ohh er nema wlh kika zo haihuwa kikai mana raki sai na koraki dangin ubanki.

Ohh ni husna gorin da ake min ya isa, waya fada miki nima anan zan zauna bayan na haihu?

Ai sai gidan nan ya miki zafi dan mummy zanbi mu koma kaduna.

Kin hakura da bokon kenan?

Ban hakura ba amma sai yarona ko yarinyata yai wayo.

Jifanta adda tai da pillow tace kedai wlh baki da kunya.

Ynxu kuma da ban tanka miki ba sai kice na raina ki.

Shiru adda tayi tana tunanin rabuwa da Asmau dan an yanke shawarar auren ta da hammad idan Allah ya sauki husna lfy.

Sallamar hussain ce ta katse musu hirar tasu da rabinta fada ne.

Da sauri husna ta janyo hijabin dake gefenta dan tunda humaid ya rasu yau kusan wata 8 bata taba zama gaban bare babu hijabi ba duk kusancinsu kuwa, bata taba fita ko ina ba in ba asibiti ba, haka zalika bata taba yin ado ko sanya turare ba.

Iyakarya wanka sai vaseline da roll on. Haka take zamanta, kullum kuwa sai tayi humaid addua saidai in bata kai goshinta qasa ba.

Lokaci zuwa lokaci takan ware taita harkokinta kamar ba abunda ya faru. Wani sa'in kuma taita kuka inta tuno masoyinta yana kwance a inda ba'a dawowa.

Hussain ne ya kalli Husna ta gefen ido yai saurin kauda kai.

Kallo daya ya gane ta yi fari sosai ta dan kumbura, a ranshi yace da Humaid yana raye da sun gaji da labarin baby, da sun gaji babyna tana can tana fama Allah sauketa lfy. Da ynxu ya damesu da cewa ya kusa zama uba.

Shi kanshi yana matuqar kewar Humaid.

Humaid issa very lively human indai zai rabeka to zaka soshi, indai kuka saba u will always miss him wen he isn't there!

Tausayin Husna ne ya shige shi yace Allah ne kadai yasan yadda Husna ke kewar Humaid.

Gaisawa sukai da adda sannan husna, ya dan taba hira da adda ba tare da ya sako Husna ciki ba itama bata saka musu baki ba, tazo tuwon ta rufe dan ta koshi.

Adda tace ko a zubo maka tuwo?

Toh yace.

Husna ce ta miqe ta koma daki ta sanar da mummy zuwan hussain itama ta fito dan su gaisa.

Mummy na fita ta fada kan gadon tana tunanin Humaid!

"𝑏𝑎𝑏𝑦 𝑎𝑚 𝑔𝑜𝑖𝑛𝑔 𝑡𝑟𝑢 𝑡ℎ𝑖𝑠 𝑎𝑙𝑜𝑛𝑒, 𝑖 𝑤𝑖𝑠ℎ 𝑢 𝑟 𝑎𝑙𝑖𝑣𝑒 𝑠𝑜 𝑖 𝑐𝑎𝑛 𝑠𝑒𝑒 𝑡ℎ𝑎𝑡 𝑠𝑚𝑖𝑙𝑒 𝑜𝑓 𝑦𝑜𝑢𝑟𝑠, 𝑠𝑜 𝑖 𝑐𝑎𝑛 𝑠𝑒𝑒 𝑡ℎ𝑎𝑡 𝑖𝑛𝑒𝑣𝑖𝑡𝑎𝑏𝑙𝑒 ℎ𝑎𝑝𝑝𝑖𝑛𝑒𝑠𝑠 𝑜𝑓 𝑢𝑟𝑠 𝑤𝑒𝑛 𝑤𝑒 𝑐𝑢𝑑𝑑𝑙𝑒 𝑖𝑛 𝑏𝑒𝑑🥺, 𝐻𝑢𝑚𝑎𝑖𝑑 𝑢 𝑚𝑎𝑑𝑒 𝑚𝑒 𝑡ℎ𝑒 𝑤𝑜𝑚𝑎𝑛 𝑖 𝑎𝑚 𝑡𝑜𝑑𝑎𝑦, 𝑢 𝑟 𝑚𝑦 ℎ𝑎𝑝𝑝𝑖𝑛𝑒𝑠𝑠 𝑛𝑑 𝑢 𝑚𝑒𝑘 𝑚𝑒 𝑟𝑒𝑎𝑙𝑖𝑠𝑒 𝑤ℎ𝑎𝑡 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑚𝑒𝑎𝑛𝑠, 𝑡ℎ𝑒 𝑣𝑒𝑟𝑦 𝑓𝑖𝑟𝑠𝑡 𝑑𝑎𝑦 𝑖 𝑚𝑒𝑡 𝑢 𝑡𝑖𝑙𝑙 𝑑 𝑑𝑎𝑦 𝑢 𝑙𝑒𝑓𝑡 𝑤𝑖𝑡ℎ𝑜𝑢𝑡 𝑎 𝑔𝑜𝑜𝑑𝑏𝑦𝑒 𝑤𝑎𝑠 𝑚𝑒𝑚𝑜𝑟𝑎𝑏𝑙𝑒 𝑓𝑜𝑟𝑒𝑣𝑒𝑟! 𝑤𝑒𝑛 𝑖 𝑝𝑢𝑡 𝑡𝑜 𝑏𝑒𝑑 𝑖 𝑎𝑚 𝑔𝑜𝑖𝑛𝑔 𝑡𝑜 𝑡𝑒𝑙𝑙 𝑢𝑟 𝑘𝑖𝑑 𝑎𝑏𝑜𝑢𝑡 𝑢, 𝑖 𝑤𝑖𝑙𝑙 𝑡𝑒𝑙𝑙 ℎ𝑖𝑚/ℎ𝑒𝑟 𝑢 𝑟 𝑡ℎ𝑒 𝑏𝑒𝑠𝑡 𝑓𝑎𝑡ℎ𝑒𝑟"

HUSNA_HUMAID (completed )Where stories live. Discover now