25. Final

179 16 4
                                    

بسم الله الرحمن الرحيم 💘
اسلام عليكم ورحمة الله وبركاته 💖

Husna sun fara exams, ta maida hnkali sosai akan jarabawarta, kuma hakan ba qaramin taimakon ta yayi ba sbd dagiya da hazaqa, yadda take yin exams din, ita kanta tana gamsuwa da irin qoqarin da takeyi, tana da hope akan samun nasararta.

💖💖💖💖💖
Ta samu interval din 5days, tana zaune a garden tana karatu, muhammad na gefenta yana bacci. Rigace a jikinta doguwa iyaka gwiwa sai dankali data daura ta dora santala santalan kafafunta akan pillow.

Kamar ance ta daga kai, aiko hussain ta gani ya zuba mata ido,

Kashhh ta fada aranta! Ko miye hakan oho? An kusa aura maka ni doesn't mean ni matarka ce.

Hijab din da taiwa Muhammad pillow dashi ta zare ta zura tare da lakwashe qafafunta, a dan daqile ta gaishe shi,
Murmushi yayi yace amarya to duk wannan stressing kan naki da kike dan ina kallonki ne?

Aike kyakkyawa ce husna, kyanki yakai matakin da babu wanda zai iya dauke ido a kanki ballentani ni da nake sonki kuma nake dab da aurenki.

Bata ta tanka ba,

Sanin bazata tanka mashi ba ne yasa yace Muhammad bacci yake kenan, Allah ya taimaka ma baki tasheshi ba garin daukar hijab.

Hmm ai nasan bazai tashi ba, Muhammad baida matsala.

Naga alama sbd yadda kike samun damar karatunki.

Eh nana ma tana taimakawa dan idan rigiman ya motsa sai ajikina zaiyi bacci.

Tohh lalle ne, ya fada yana yaqe.

Yasan yana son husna kuma yana son Muhammad amma yadda take prioritizing yaron yana dan damunshi, ace ko hira indai bai tsomo danta aciki ba baya samun yadda yake so?

Gacan kuma Asiya ta kunna wutar bore sai rashin mutunci take kala kala, har takai matakin da inya neme ta zata ce yaje husna ta bashi, yakan ce me kike ci na baka na zuba, mu ba mazinata bane, amma idan mukai auren zata bani.

Wannan cika baki da confidence taba dab ta barewa muddin husna bata sauya mindset dinta ba, yana tsoro matuka kar husna ta bashi wahala!!

💕💕💕💕💕
Anyi exams an gama lfy, ana ta shirye shiryen auren hussain da husna, wanda ita husnan ko ajikinta.

Tace ko walima bazatai ba. Da aka matsa mata tasa kuka.
Tace;
Adda we live once, love once nd marry once, u made me into marrying twice pls don't force me to love twice, love occur naturally.

Haka akai bikin nan lami ta bangaren husna ko kwalliya batai ba, tadai sanya sutturu na alfarma wadanda suka sha dinki, bakin kaduna duk an hallara.

Hussain kuwa ya rasa inda zai tsoma ranshi don dadi, Muhammad ma an mishi ado kana gani kaga dan amarya.

Bayan magrib Abban husna yace ango yazo ya tafi da amaryarshi babu me rakasu...

Husna kuwa Muhammad ta saba a kafada ta fito, baki bude adda tace,
Amma husna baki da hankali, sai lallabaki ake tun dazu kin botsewa? Gidan ubanwa zaki da Muhammad din? Ke husna ki shigo hankalin ki aure ba abun wasa bane!!

A wane garin kika taba jin an kai amarya da goyo?

A tunaninki meyasa nai murna da Muhammad ya yaye kanshi sati uku da suka wuce???

Toh bazai yiwu ba, bazai ki maida mu en iska ba...!

Tunda Adda ta fara bambami husna take kuka, they're making the decision more tedious for her, they couldn't understand she's just obeying!

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 14, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HUSNA_HUMAID (completed )Where stories live. Discover now