2. how it all started

293 22 0
                                    


The spicy one, trust me u will like it💕💕💕

Sunana  Aysha ta nabiyyu, kamar yadda kika ganni kaf gidan mu haka muke kyawawa na nunawa a gari, babanmu sananne ne a garin gombe ya riqe muqamai da yawa kafin mutuwar shi, umman mu ita kadai ce mata a gareshi, gaba dayan mu mata ne. Saboda baiwa ta kyau da gata da kudi da muka samu ya sanya rayuwar mu ta ginu akan buri da son auren mai kudi, dukkan yayuna masu kudi suka aura, daga matar minister sai matar governor sai matar controller da manya manyan attajirai na garin gombe da kewaye.
Lokacin da aurena yazo naga gata domin uwata tamin, ubana yamin yayuna sumin sannan mazajensu ma sumin, sbd duk na saba da mazajen nasu domin duk hutun makaranta na a gidajensu nake qareshi.
Kar in jaki da nisa, nima auren kudin nayi sai dai kash... Shigo shigo ba zurfi ne domin shima mijin hangen kudinmu yake, aiko ko wata biyu ba'ai ba zaman aure yaqi dadi... Ban bata lokaci ba kuwa na lalato auren na dawo gd dan bazan iya zama a wannan gidan ba!

Saidai me? Ina dawowa gidan mu zawarci sai ga ciki boom ya bayyana, babu yadda banyi ba na zubar amma babana yace muddin na zubar saiya kasheni haka na hakura na soma rainon cikin ibrahim ( ex-husband) dina.

Cikin nada wata 8 ummanmu ta kwanta jinya ai kuwa rai yai halinshi, shima abban mu ba'a jima ba ya bita... A sannan ne duniya tamin zafi nafara jin dama na zauna gidan ibrahim ko kuwa zai dinga yankar naman jikina ne yana soyawa...

HUSNA_HUMAID (completed )Where stories live. Discover now