13, Doctor Knight

145 19 13
                                    

Bismillahirrahmanirrahim❤️

Lemme bribe u with chocolates🙊

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Lemme bribe u with chocolates🙊

It been a while.

Husna_humaid

13. Dr. Knight

Humaid ne ya waiga a nutse yace uncle abdul shall we??

Murmushi uncle abdul yayi yace yeah son!
Kallon abban husna yayi ya kalli baba qarami yace mu shiga daga ciki,
Husna ce cikin hawaye tace humaid meke faruwa? Wai waye zai rabamu? Kume me sa??😭

Auwal ne yace uwarsa ce zata rabaku sbd ke shegiya ce! Ko iyayenki basu fada miki zina sukai suka haifeki ba???

Dimmmmm husna ta daina jin komai, blur ta fara gani sai jiri, luuuu tayi zata fadi humaid ya taro yana kwala mata kira, HUSSSSNAAAA!!! wlh in kika mutu nima mutuwa zanyi!!

Hammad ne ya shaqo auwal yana fadin ka cuceni, in ka kashe min yarinya wlh saina kasheka!!!

Da sauri anty ta fito su yusra suna binta a baya ganin halin da husna ke ciki tace humaid kawota ciki, kai ba likita bane??? Save her!

Da sauri ya shiga parlor din ya kwantar da ita akan carpet, rasa ma me zai fara yayi da sauri ya dau pulse dinta, daya tabbatar tana raye... quick prescriptions yayi yaba yusra yace yi gudu kije chemists ki siyo abun nan, ko takalmi bata saka ba ta fita da gudu.... me gadi ne yace ina zaki haka, tana haki tai briefing dinshi halin da ake ciki, karba yayi yace ta koma gida babur dinshi ya figa da gudu ya tafi siyo iv fluid din da giving set!

A can waje kuwa baba karami da uncle abdul sun raba hammad da auwal...

Auwal sai kunfar baki yake yana cewa uncle abdul wlh sai na fadawa hajja, ashe kai munafiki za'a hada baki dakai a cuci hajja?? Sbd humaid ba danka bane zaka bari ya auri shegiya???

Uncle abdul daya girmi auwal nesa ba kusa ba hatta hajjan ya girmeta kawai kau da kai yayi dan bazai tsaya kula auwal ba!

Kallon baba karami yayi yace Allah bai haramta auren nan ba sbd haka ni inayiwa humaid waliy tare da izininsa, wa zaiyiwa husna???

Baba karami yace zan zama waliy a gareta...

Makwabta abban husna ya gayyata suka shaida, aka bi siga irinta addinin musulunci, waliyyai suka amice da bayar da aure tare da karbar aure, a bisa dokoki da sharuda na musulunci, aka biya sadaka dubu dari lakadan ba ajalan ba!!!

Allah is great aure ya dauru tsakanin humaid da husna!!

🎶🎵Mekesa darajar da namiji ta dada hauhawa?  Aure
Me raba ya da umma idan ka cire mana mutuwa? Aure
Ta rayu gidan mijinta su zam abokan shawara... aure
Rayuwar aure da dadi nima rana na zuwa.. aure
Yadda duk na dafe haka innai aure sai kunga nai haske!!🎶🎵

HUSNA_HUMAID (completed )Where stories live. Discover now