*_My Bestie's husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Free book_*
*_7-8_*
_Masu Bina suna cewa na turo musu daga farko kuyi hqr bazan iya bane duk groups din da kukaganshi to ku tambaya zaku samu abun zaimin yawa nayi typing nayi Post sannan nazo na rinqa binku one by one Ina tura muku please kada wata tace banida da mutunci wlh ko kin bini bazan turaba Amma fah kuyimin uzuri nima inada uzurirrika na na qashin kaina sannan wannan book din kyautane sadaukawa ga duk wani masoyina dake fadin duniya nasan addu'ar ku ke samamin kariya gurin Ubangiji Kuma Allah ya kareku daga bakin duniya😘_
____________________________
____________________________Batare da yayi aune ba ko ya zata yaji saukar yatsun hannunta akan kyakkyawar fuskarsa me cike da saje abinda ya haddasa masa cin wani uban birki ji kaki qiiiiiiy! Abinda yasasu wata girgiza hakan baisa Rafi'ah ta daina tsumar da takeyi ba idanunta har yanzu na kansa ya saki baki yana kallonta rabon da asa hannu a mareshi har ya manta.
Bude qofar takai hannu zatayi yayi saurin danna pin din ta juyo cikin bala'i tace "zanci kutumar ubanka Ja'afar zan yaga alfarmarka da mutuncinka matuqar baka budemin motarnan ba...." hannu ya sa ya toshe kunnensa ta sake daga murya cikin qaraji tace "ka budemin mota nace stupid man kawa...." Bata rufe bakinta ba ya cafki bakinta da nasa ai baigama Kama harshenta ba ta gasa masa cizo a harshe dake cikkaken dan air ne ido kawai ya rintse ya sake tura harshen nasa cikin bakinta yana qoqarin sanya qarfi ya janyota jikinsa ta cure jikinta ta banqara ta kwace ta zame daga kujerar ta rushe da kuka tace "nashiga uku ni Rafi'ah wannan wacce irin baqar ranace Jama'a meye yake faruwa danine...." Bude motar yayi ya dube fiddausi yace "jeki little jirani...." Kafin ya ankara Rafi'ah ta bude qofar ta dire waje kamar wata mahaukaciya ta kwasa da gudun bala'i ta runtuma cikin daji.Cikin tashin hankali ya fito yabi bayanta a guje dake dogone ita Kuma tsayin ba sosai ba sai gashi yacin Mata da taimakon bishiyar da tayi karo da ita ta caki goshinta tayi baya taga taga zata fadi ya tareta ta fada hannunsa ga matsanancin mamakinsa sai yaga ta fado hannunsa sumammiya abinda ya qara fitar dashi a hayyacinsa ya dagakai ya kalli Fiddausi data dafe qirji tanason mgn Amma tsoron jizginsa ya hanata yace "meye hakan Fiddausi saboda nace inasonta shine harta suma"
Cije lebe tayi tace "yaya abinda girma ka taimaketa ka kaiyi Mata urgent treatment" sabarta yayi a kafadarsa ya sata a mota ya shiga cikin garin Kai tsaye wani asibintinsa ya nufa sabone bai dade da budeshi ba ya dauketa kamar beby ya shiga da ita har dakin da zai dubata ya cire babbar rigarsa duk likitocin dake asibitin ya hanasu tabata dakansa yayi treet nata ya cire Mata iccen daya shiga goshinta ya wanke gurin da magani, yana tsaka da dressing din gurin wayarsa ta fara ring ya daga ganin number Ni'imah ya danna ok Bai bata damar mgn ba yace "naje cikin Bauchi ne inada wani petiant bama lallai tafiyar nan yau ba saboda yanada muhimmanci a gurina" yana Shirin kashe wayar yaji tace "sweet kaje gurin Bestie kace nace tabani abin dadi" duk da damuwar dake cinsa Saida yayi murmushi yace "insha Allah zanyi qoqari" yana fadin haka ya kashe wayarsa yaci gaba da abinda yakeyi.Yana gama dressing din ta farka ganinta daure da drip yasata miqewa ta fincike allurar ta watsar juyowar da zaiyi yaganta tana daye dressing din da yayi mata ya nufota a guje yana cewa "kewai meye hakanne baki da hankali ne jibi yanda kika jiwa kanki ciwo kina tunanin hakanne zaisa na janye qudurina" wani matsiyacin kallo tayi masa ta nufi qofa ya nufota da niyyar hanata fita ta juyo tace "wlh tallahi ka qara matsata sai nayimaka ihu na tona maka asiri fajiri maci amanar qauna ka dauka ni yar iskace da zakazomin da wannan games din to kayi gaggawar lashe amanka kafin ka fuskanci qasqanci a gurina Ja'afar bana zama inuwa daya da maci amana maha'inci dan uwan shaidan me burin shiga tsakanin qauna,
Sakin baki yayi tare da rungume hannunsa a qirjinsa shi masifar tata ma burgeshi takeyi baitaba ganin mutumin da yake fada yana kyau ba sai ita yana wannan tunanin ta fice da sauri cikin saa tana fita ta fada napep ta fada masa inda zai kaita Koda ya fito baiga alamarta ba ya tambaya akace tahau napep kafin yaje ya dauko rigarsa ya nemo Fiddausi har takai school tana zuwa ta nufi hostel tanata wucce mutane bata gane su waye har ta Isa dakin ta fada gado ta rushe da kuka tana furta " Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un Allahummah ajirni fih musibati wa'akalifni khairin minha" ta jima tana kuka me dafa zuciya bata taba shiga tashin hankali irin na yauba ji tayi anzauna a gefenta ta tashi firgigit.
Ajiyar zuciya tayi ganin Nina ce tace "meye Kuma pretty?" Kukanta ta qarawa qarfi tanasa tisue tana tsane jinin da Bai daina zuba a ciwon ba Nina ce ta dauko wani dan qaramin akwati ta bude ta dauko auduga da magani tayi Mata dress na gurin tace "yanzu Mutuminnan na jiya yazo yabani magunguna yace na kawo miki garinyaya kikaji ciwo?" Dora Mata magungunan tayi a cinyarta tayi watsi dasu tace "kije kice masa banaso bana buqata ki hada masa da kayansa na jiya duka banaso ya fadi meye yakeso bayan wannan na fadawa abbana ya biyashi nidai roqona ya janye furucinsa, kwanciya tayi tace "Nina meye yasa mutane basusan girman aminta ba meyesa basusan darajar alaqa ba ? Meyesa Ja'afar zaiyimana haka wlh bantaba zatoba Koda wasa nayi tunanin duk abinda yakeyimin saboda Bestie na yakeyi min meyesa zaiyimin haka me yake nufi dani Nina ya cutar dani ko iya haka kalamansa suka tsaya na rantse da Ubangijin da yake rayani bayan ya kasheni a kowanne lkc nayi bacci bantaba jin tsanar wani mutum araina ba sai yau naji tsanar Ja'afar Wakil ta darsu a qoqon zuciyata natsani mutum maci amana"

YOU ARE READING
MY BESTIE'S HUSBAND
RomantikaMIJIN AMIÑIYATA Lbrn wasu aminai da suka kasance basa rabuwa sai kwanciyar bacci, aurene ya zamo silar rabuwarsu wanda daya tayi aure tabar daya inda mijin dayar ya rinqa zagayewa yana bibiyar dayar har yayi nasara tare da cusa Mata matsananciyar qa...